BABI NA GOMA SHA BIYU
Allahnsa Ya Ƙarfafa Shi
1, 2. Mene ne ya faru a ranar da Iliya ya fi yin hidima a rayuwarsa?
ILIYA yana gudu a cikin ruwan sama yayin da gari yake daɗa yin duhu. Yana da sauran tafiya sosai kafin ya isa birnin Jezreel, kuma shi ba matashi ba ne. Duk da haka, ya ci gaba da yin gudu kuma bai gaji ba. Me ya sa? Domin “hannun Ubangiji” yana tare da shi. Jehobah ya sa ya yi ƙarfi sosai a wannan ranar. Shi ya sa ya tsere wa karusan da Sarki Ahab ke ciki!—Karanta 1 Sarakuna 18:46.
2 Yanzu dai, ya riga ya tsere wa Sarki Ahab amma har ila yana da sauran tafiya. Ka yi tunanin yadda ruwan da ake sheƙawa yake dūkan fuskar Iliya yayin da yake tunani a kan ranar da ya fi yin hidima a rayuwarsa. Babu shakka, wannan nasara ce mai girma ga Jehobah, Allahn Iliya, da kuma bauta ta gaskiya. Iliya ya riga ya bar Dutsen Karmel wanda hadari ya rufe a can baya, inda Jehobah ya yi amfani da shi wajen fallasa bautar Baal a hanya mai girma da kuma ban al’ajabi. An fallasa ɗarurruwan annabawan Baal waɗanda miyagun ’yan zamba ne, kuma an yi musu kisan da ya dace. Bayan haka, Iliya ya roƙi Jehobah ya kawo ƙarshen fari da ya addabi ƙasar har shekara uku da rabi. Sai aka yi ruwa kamar da bakin ƙwarya!—1 Sar. 18:18-45.
3, 4. (a) Me Iliya yake ɗokin gani ya faru yayin da yake gudu zuwa Jezreel? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?
3 Yayin da Iliya yake gudu a cikin ruwan sama zuwa Jezreel da ke da nisan mil 19, wataƙila yana tunanin cewa tun da yake an halaka annabawan Baal, abubuwa za su canja. Ahab zai tuba! Bayan abubuwan da ya shaida da idanunsa, ya kamata ya daina bauta wa Baal, ya kwaɓi sarauniyarsa Jezebel kuma ya sa a daina tsananta wa bayin Jehobah.
4 Babu shakka, idan abubuwa suna tafiya yadda muke so, za mu so hakan ya ci gaba. Wataƙila ma muna iya tunanin cewa mun rabu da matsalolinmu ke nan. Ba zai kasance abin mamaki ba idan Iliya ya yi irin wannan tunanin, domin shi “ɗan Adam ne kamarmu.” (Yaƙ. 5:17, Littafi Mai Tsarki) Gaskiyar ita ce, tsugunne bai ƙare ba. Hakika, nan da ’yan sa’o’i kaɗan, Iliya zai tsorata sosai, zai yi matuƙar baƙin ciki har ya gwammace ya mutu. Me zai sa ya yi hakan, kuma ta yaya Jehobah ya taimaka wa annabin ya inganta bangaskiyarsa da kuma gaba gaɗinsa? Bari mu gani.
Canjin Yanayi Ba Zato Ba Tsammani
5. Shin Ahab ya daraja Jehobah bayan abin da ya faru a Dutsen Karmel, kuma ta yaya muka sani?
5 Sa’ad da Ahab ya isa fadarsa a Jezreel, shin ya nuna cewa ya riga ya tuba ne? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ahab ya faɗa wa Jezebel dukan abin da Iliya ya aika, da yadda ya kashe dukan annabawa da takobi.” (1 Sar. 19:1) Ahab bai ambata Jehobah, Allahn Iliya ba a labarin da ya ba da. Me ya sa? Domin Ahab bai da dangantaka da Allah, shi ya sa ya ɗauka cewa al’ajaban da suka faru ayyukan ɗan Adam ne, wato “abin da Iliya ya aika.” A bayyane yake cewa bai daraja Jehobah ba. Kuma mene ne wannan mata mai son ɗaukan fansa ta yi?
6. Wane saƙo ne Jezebel ta aika wa Iliya, kuma mene ne hakan yake nufi?
6 Jezebel ta fusata! Sai ta aika wannan saƙon ga Iliya: “Bari alloli su yi haka nan da ni, har su yi da ni fiye da haka ma, idan ban maida ranka kamar ran ɗaya daga cikinsu ba kafin gobe warhaka.” (1 Sar. 19:2) Wannan muguwar barazana ce ga ransa. Jezebel ta rantse cewa ko ta mutu ko ta kashe Iliya a wannan ranar, domin ta rama abin da ya yi wa annabawanta na Baal. Ka yi tunanin yadda aka ta da Iliya daga barci a wani madaidaicin masauki a Jezreel a wannan daren da ake ruwa da iska mai ƙarfi, kuma ɗan aikan sarauniyar ya gaya masa wannan saƙo mai ban tsoro. Ta yaya hakan ya shafe shi?
Ya Yi Sanyin Gwiwa Kuma Ya Ji Tsoro
7. Yaya barazanar da Jezebel ta yi ta shafi Iliya, kuma mene ne ya yi?
7 Idan a dā Iliya yana tunanin cewa yaƙi da bautar Baal ya riga ya ƙare, a yanzu ya ga cewa hakan ba gaskiya ba ne. Jezebel ba ta ja da baya ba. Ta riga ta sa an kashe abokan aikin Iliya masu aminci da yawa, kuma yanzu, shi take so a kashe. Yaya barazanar da Jezebel ta yi ya shafi Iliya? Wata fassarar Littafi Mai Tsarki ta ce: “[Iliya] ya ji tsoro.” Wataƙila Iliya ya yi tunanin irin mugun kisan da Jezebel take shirin a yi masa. Amma idan ya ci gaba da yin hakan, to ba abin mamaki ba ne cewa ya yi sanyin gwiwa. Ko da mene ne, Iliya ya “gudu domin shi tsira da kansa.”—1 Sar. 18:4; 19:3.
Idan muna so mu ci gaba da kasancewa da bangaskiya bai kamata mu rika yin tunani a kan wasu abubuwan da za su iya sa mu ji tsoro ba
8. (a) Ta yaya matsalar Bitrus ta yi kama da na Iliya? (b) Wane darasi ne muka koya daga Iliya da Bitrus?
8 Ba Iliya kaɗai ba ne mutumi mai bangaskiya da ya taɓa tsorata ba. Shekaru da yawa bayan wannan aukuwar, manzo Bitrus ya fuskanci irin wannan matsalar. Alal misali, sa’ad da Yesu yake tafiya a kan teku, ya gaya wa Bitrus ya zo ya same shi, amma sa’ad da manzon ya soma kallon “iska,” sai ya tsorata kuma ya soma nitsewa. (Karanta Matta 14:30.) Mun koyi darasi sosai daga misalan Bitrus da kuma Iliya. Idan muna son mu kasance da gaba gaɗi, kada mu yi tunanin haɗarurrukan da suke tsoratar da mu. Muna bukatar mu mai da hankalinmu a kan Tushen begenmu da kuma ƙarfinmu, wato Jehobah.
“Ya Isa”
9. Ka kwatanta irin tafiyar da Iliya ya yi da kuma yadda ya ji yayin da yake gudu.
9 Saboda Iliya ya tsorota, sai ya tsere zuwa kudu maso yamma, tafiyar mil 95 zuwa Beer-sheba wani gari da ke kusa da kudancin iyakar Yahuda. A nan ne ya bar mai yi masa hidima kuma ya shiga daji shi kaɗai. Labarin ya ce ya yi “tafiyar yini,” saboda haka, wataƙila ya fara tafiyar tun da asuba, kuma bai ɗauki abinci ko wasu tanadodi ba. Cike da baƙin ciki da tsoro, ya ci gaba da tafiya cikin rana mai ƙuna a jejin da ke cike da haɗari. Iliya ya gaji da tafiyar yayin da rana ta soma faɗuwa kuma dare yana yi. Saboda haka, sai ya zauna a ƙarƙashin wani itace, a wannan hamadar da babu itatuwa da yawa.—1 Sar. 19:4.
10, 11. (a) Mece ce ma’anar addu’ar da Iliya ya yi? (b) Ta wajen yin amfani da nassosi da ke sakin layin, ka faɗa yadda wasu bayin Allah suka ji sa’ad da suka yi sanyin gwiwa.
10 Da yake Iliya yana matuƙar baƙin ciki, sai ya roƙa ya mutu. Ya ce: “Ban fi ubannina kyau ba.” Ya san cewa kakanninsa sun riga sun zama turɓaya da ƙasusuwa a cikin kabari, ba za su iya yi wa kowa kome ba. (M. Wa. 9:10) Sai ya yi tunani cewa shi ma ba zai iya yin kome ba. Shi ya sa ya ce da babbar murya: “Ya isa!” Bai ga amfanin rayuwa ba.
11 Shin abin mamaki ne cewa bawan Allah ya yi baƙin ciki? A’a. Akwai maza da mata masu aminci da dama a cikin Littafi Mai Tsarki da aka nuna cewa sun yi baƙin ciki sosai har suka gwammace su mutu. Wasu cikinsu su ne Rifkatu da Yakubu da Musa da kuma Ayuba.—Far. 25:22; 37:35; Lit. Lis. 11:13-15; Ayu. 14:13.
12. Ta yaya za ka bi misalin Iliya idan kana sanyin gwiwa?
12 Muna rayuwa a cikin “miyagun zamanu,” saboda haka, ba abin mamaki ba ne cewa mutane da yawa, har da bayin Allah masu aminci sukan yi baƙin ciki a wasu lokatai. (2 Tim. 3:1) Idan kana cikin irin wannan yanayi mai wuya, ka bi misalin Iliya ta wajen gaya wa Allah yadda kake ji. Domin Jehobah ne “Allah na dukan ta’aziyya.” (Karanta 2 Korintiyawa 1:3, 4.) Ya ƙarfafa Iliya kuwa?
Jehobah Ya Tallafa wa Annabinsa
13, 14. (a) Ta yaya Jehobah ya yi amfani da mala’ikansa don ya nuna cewa ya damu da annabinsa da ya faɗa cikin matsala? (b) Ta yaya sanin cewa Jehobah ya san da kowannenmu har da kasawarmu yake ƙarfafa mu?
13 Yaya kake ganin Jehobah ya ji sa’ad da ya kalli ƙasa kuma ya ga ƙaunataccen annabinsa yana kwance a ƙarƙashin itacen nan cikin jeji yana roƙo ya mutu? Ba sai mun yi dogon tunani ba. Bayan barci ya kwashi Iliya, Jehobah ya aiki mala’ika zuwa wurinsa. Mala’ikan ya ɗan taɓa Iliya, ya ta da shi daga barci kuma ya ce: “Tashi, ka ci [abinci].” Iliya ya yi hakan, domin mala’ikan ya riga ya shirya masa burodi mai ɗumi da kuma ruwa. Shin ya ma yi wa mala’ikan godiya kuwa? Ba mu sani ba. Amma, an faɗi a labarin cewa annabin ya koma barci bayan ya ci kuma ya sha. Shin baƙin ciki ne da karaya suka hana shi yin magana? Ko ma mene ne, mala’ikan ya sake ta da shi, wataƙila da wayewar gari. Ya sake gaya wa Iliya, “Tashi, ka ci [abinci],” kuma ya daɗa waɗannan muhimman kalmomi, “gama tafiya ta fi ƙarfinka.”—1 Sar. 19:5-7.
14 Mala’ikan ya san inda Iliya ya dosa domin Allah ya ba shi basira. Ya kuma san cewa tafiyar mai nisa ce, kuma Iliya ba zai iya yin ta da ƙarfinsa kaɗai ba. Abin ban ƙarfafa ne mu bauta wa Allahn da ya fi mu sanin muradinmu da kuma kasawarmu! (Karanta Zabura 103:13, 14.) Ta yaya Iliya ya amfana daga wannan abincin?
15, 16. (a) Ta yaya abincin da Jehobah ya ba Iliya ya taimaka masa? (b) Me ya sa za mu nuna godiya don tanadin da Jehobah yake yi wa bayinsa a yau?
15 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya tashi, ya ci, ya sha; a cikin ƙarfin wannan abinci fa ya kama tafiya yini arba’in da dare arba’in har ya zo Horeb dutsen Allah.” (1 Sar. 19:8) Iliya ya yi azumi dare da rana har kwanaki 40, kamar yadda Musa da ya rayu ƙarnuka shida kafin shi da kuma Yesu da ya rayu ƙarnuka kusan goma bayan shi suka yi. (Fit. 34:28; Luk 4:1, 2) Wannan abinci guda bai warware dukan matsalolinsa ba, amma ya taimaka masa ta hanyar mu’ujiza. Ka yi tunanin yadda wannan dattijon yake takawa cikin ƙungurmin daji dare da rana har tsawon kwanaki 40!
16 Hakazalika, Jehobah yana kula da bayinsa a yau, ba ta abincin da aka tanadar ta mu’ujiza ba, amma a wata hanya mafi muhimmanci. Yana yi wa bayinsa tanadin abubuwan da za su taimaka musu su ƙarfafa dangantakarsu da shi. (Mat. 4:4) Idan muka ci gaba da koya game da Allah ta wajen karanta Kalmarsa da kuma littattafan da suke bayyana Littafi Mai Tsarki, za mu ƙarfafa dangantakarmu da shi. Mai yiwuwa, karanta waɗannan littattafan ba zai warware dukan matsalolinmu ba, amma zai iya taimaka mana mu jimre da su. Zai kuma sa mu samu “rai na har abada.”—Yoh. 17:3.
17. Wane wuri ne Iliya ya je, kuma me ya sa wurin yake da muhimmanci?
17 Iliya ya yi tafiyar kusan mil 200 kafin ya isa Dutsen Horeb. A wurin nan ne Jehobah ya taɓa bayyana ga Musa a cikin kurmi da ke cin wuta, kuma daga baya ya ba Isra’ila Dokar alkawari. Iliya ya samu mafaka a cikin kogon dutsen nan.
Yadda Jehobah Ya Ƙarfafa Annabinsa
18, 19. (a) Mene ne mala’ikan Jehobah ya tambayi Iliya, kuma wace amsa ce ya ba da? (b) Waɗanne dalilai uku na yin sanyin gwiwa ne Iliya ya ba da?
18 Jehobah ya aiki mala’ika ya tambayi Iliya a Dutsen Horeb cewa: “Me ka ke yi a nan, ya Iliya?” Mai yiwuwa, ya yi wa Iliya wannan tambayar da murya marar ƙarfi, shi ya sa ya samu damar furta yadda yake ji. Hakika, abin da ya yi ke nan! Ya ce: “Na yi kishi ƙwarai domin Ubangiji, Allah mai-runduna; gama ’ya’yan Isra’ila sun ƙi alkawarinka, sun kaɓantar da bagadanka, sun kashe annabawanka da takobi: ni ma, ga ni kaɗai na rage; suna kuwa neman raina su ɗauka.” (1 Sar. 19:9, 10) Kalmomin Iliya sun bayyana aƙalla dalilai uku da suka sa shi baƙin ciki.
19 Na farko, Iliya yana ganin cewa ya yi aikin banza. Duk da shekarun da ya yi yana “kishi ƙwarai” a bautar Jehobah da kuma ɗaukaka sunan Allah da bautarsa fiye da kome, Iliya ya ga kamar yanayin sai daɗa muni yake yi. Har ila, mutanen suna rashin bangaskiya da tawaye, yayin da bautar ƙarya take haɓaka. Na biyu, Iliya yana ganin cewa shi kaɗai ne ya rage cikin waɗanda ke bauta wa Jehobah a al’ummar. Shi ya sa ya ce: “Ni ma, ga ni kaɗai na rage.” Na uku, Iliya ya tsorata. An riga an kashe ’yan’uwansa annabawa da yawa, kuma ya tabbata cewa shi ake neman a kashe. Mai yiwuwa furta yadda yake ji bai zo wa Iliya da sauƙi ba, amma bai ƙyale girman kai ko kunya ta hana shi yin hakan ba. Ta wurin bayyana wa Allahnsa yadda yake ji a cikin addu’a, Iliya ya kafa misali mai kyau ga dukan masu aminci.—Zab. 62:8.
20, 21. (a) Mene ne Iliya ya gani daga bakin kogo da ke Dutsen Horeb? (b) Mene ne Iliya ya koya daga yadda Jehobah ya nuna ikonsa?
20 Ta yaya Jehobah ya magance damuwa da kuma tsoron da Iliya yake ji? Mala’ikan ya gaya wa Iliya ya tsaya a mashigin kogon. Iliya bai san abin da zai faru ba, amma duk da haka ya yi biyayya. Farat ɗaya, sai iska mai ƙarfi ta taso! Babu shakka, iskar ta zo da ruri mai tsanani, domin sai da ƙarfinta ya tsatsage duwatsu. Ka yi tunanin yadda Iliya yake ƙoƙarin kāre idanunsa yayin da yake riƙe gam da tufafinsa na fata da iska take kaɗawa. Bayan hakan, ya soma ƙoƙarin riƙe kansa don kada ya faɗi, domin an soma girgizar ƙasa a yankin! Bai gama farfaɗowa ba sa’ad da wuta ta taso, kuma hakan ya tilasta masa ya koma cikin kogon domin ya kāre kansa daga zafin wutar.—1 Sar. 19:11, 12.
21 Labarin ya sa mu tuna cewa Jehobah ba ya cikin waɗannan abubuwa masu ban mamaki da yake amfani da su wajen bayyana ikon halitta. Iliya ya san cewa Jehobah ba Allah marar rai ba ne kamar Baal, wanda masu bauta masa da aka ruɗa suke yabonsa a matsayin “Mahayin Gajimare,” ko wanda yake tanadar da ruwan sama. Jehobah ne ainihin Tushen dukan iko mai ban mamaki da ake gani a halitta, kuma ya fi ƙarfin duk wani abin da ya halitta. Ko sammai ba za su iya ɗaukansa ba! (1 Sar. 8:27) Amma, ta yaya ne dukan waɗannan abubuwan suka taimaka wa Iliya? Ka tuna cewa dā ma yana jin tsoro. Amma tun da Jehobah, Allah mai iko duka yana tare da shi, ba ya bukatar ya ji tsoron Ahab da Jezebel!—Karanta Zabura 118:6.
22. (a) Ta yaya “murya marar-ƙarfi” ta sake ƙarfafa Iliya cewa yana da daraja? (b) Wane ne yake da “murya marar-ƙarfi” ɗin? (Duba hasiya.)
22 Bayan wutar ta wuce, sai ko’ina ya yi tsit kuma Iliya ya ji wata “murya marar-ƙarfi.” Muryar ta ba Iliya damar sake bayyana yadda yake ji da kuma dukan abubuwan da ke damunsa.a Wataƙila, hakan ya ƙara kwantar masa da hankali. Babu shakka, Iliya ya samu ƙarin ƙarfafa daga abin da wannan “murya marar-ƙarfi” ta gaya masa. Jehobah ya tabbatar wa Iliya cewa shi bawansa ne mai daraja sosai. Ta yaya? Allah ya bayyana nufinsa na nan gaba game da yaƙin da zai yi da bautar Baal a Isra’ila. Hakika, Iliya bai yi aikin banza ba, domin nufin Allah ya ci gaba babu tangarɗa. Bugu da ƙari, Iliya yana da matsayin da zai ɗauka don wannan nufin ya cika, domin Jehobah ya sake tura shi zuwa bakin aiki kuma ya ba shi takamaiman umurni.—1 Sar. 19:12-17.
23. A waɗanne hanyoyi biyu ne Jehobah ya magance kaɗaicin da Iliya yake yi?
23 Kaɗaicin da Iliya yake ji kuma fa? Jehobah ya yi abubuwa guda biyu game da hakan. Na farko, ya gaya wa Iliya ya naɗa Elisha a matsayin annabin da zai gaje shi da shigewar lokaci. Wannan matashin zai yi shekaru da dama a matsayin abokin tafiyar Iliya da kuma mataimakinsa. Hakika, hakan ya ƙarfafa shi sosai! Na biyu, Jehobah ya bayyana wannan saƙo mai daɗin ji: ‘Na rage mutum [dubu bakwai] a cikin Isra’ila, dukan guwawun da ba su durƙusa ga Baal ba, kowane baki wanda ba ya yi masa sumba ba.’ (1 Sar. 19:18) Ba Iliya ne kaɗai ya rage ba. Babu shakka, zai yi murnar jin cewa akwai mutane dubbai masu aminci da suka ƙi bauta wa Baal. Suna bukatar Iliya ya ci gaba da hidimarsa da aminci, don ya kafa musu misali mai kyau na aminci a wannan lokacin da kusan kowa ya juya bayansa ga Jehobah. Kalmomin “murya marar-ƙarfi” da Iliya ya ji ta bakin wanda Jehobah ya aika sun ratsa zuciyarsa sosai.
Littafi Mai Tsarki yana kama ne da wannan “murya marar-ƙarfi,” idan muka ƙyale ya yi mana ja-gora a yau
24, 25. (a) A wace hanya ce za mu iya jin “murya marar-ƙarfi” na Jehobah a yau? (b) Me ya sa muka ce Iliya ya amfana daga yadda Jehobah ya ƙarfafa shi?
24 Kamar Iliya, abubuwa masu ban al’ajabi da muke gani a halitta za su iya sa mu mamaki, kuma hakan ya dace. Halitta tana bayyana ikon Mahalicci. (Rom. 1:20) Har yanzu, Jehobah yana yin amfani da ikonsa marar iyaka don taimaka wa bayinsa. (2 Laba. 16:9) Amma, Allah ya fi yin mana magana ne ta Kalmarsa, wato Littafi Mai Tsarki. (Karanta Ishaya 30:21.) A wani ɓangare, Littafi Mai Tsarki yana kama ne da wannan “murya marar-ƙarfi,” idan muka ƙyale ya yi mana ja-gora a yau. Jehobah yana yin amfani da shi don ya yi mana gyara da ƙarfafa mu da kuma nuna cewa yana ƙaunarmu.
25 Iliya ya amfana daga ƙarfafar da Jehobah ya ba shi a Dutsen Horeb kuwa? Babu shakka! Ba da daɗewa ba, wannan amintaccen annabi mai gaba gaɗi ya tasar wa bauta ta ƙarya. Idan muka saka hurarrun kalmomin Allah a zuciya, wato “ta’aziyyar da Littattafai ke yi mana,” za mu iya yin koyi da bangaskiyarsa.—Rom. 15:4, LMT.
a Mai yiwuwa wannan “murya marar-ƙarfi” na ruhun da aka yi amfani da shi wajen idar da “maganar Ubangiji” ne a 1 Sarakuna 19:9. A aya ta 15, an kira shi ruhun “Ubangiji.” Hakan zai iya tuna mana da mala’ikan da Jehobah ya yi amfani da shi wajen yi wa Isra’ilawa ja-gora a cikin jeji kuma wanda Allah ya ce game da shi: “Sunana yana cikinsa.” (Fit. 23:21) Hakika, ba za mu iya nacewa a wannan batun ba, amma yana da kyau mu lura cewa kafin Yesu ya zo duniya, ya yi hidima a matsayin “Kalma,” wato Kakaki na musamman ga bayin Jehobah.—Yoh. 1:1.