DARASI NA 7
Ka Taɓa Jin Kaɗaici da Tsoro?
Ka kalli ƙaramin yaron da ke hoton nan. Kamar yana jin tsoro don yana ganin shi kaɗai ne, ko ba haka ba? Hakan ya taɓa faruwa da kai?— Hakan yana iya faruwa da kowannenmu a wani lokaci. Akwai labarin wasu abokan Allah a cikin Littafi Mai Tsarki da suka ji kaɗaici da tsoro. Ɗaya daga cikinsu shi ne Iliya. Bari mu koya game da shi.
Iliya ɗan Isra’ila ne kuma ya yi rayuwa shekaru da yawa kafin a haifi Yesu. Ahab sarkin Isra’ila ba ya bauta wa Jehobah, Allah na gaskiya. Ahab da matarsa Jezebel suna bauta wa wani alla na ƙarya da ake kira Baal. Hakan ya sa mutane da yawa a Isra’ila suka soma bauta wa Baal. Jezebel matar sarkin muguwa ce. Tana so ta kashe Iliya da kuma dukan mutanen da suke bauta wa Jehobah! Ka san abin da Iliya ya yi?—
Iliya ya gudu! Ya tafi can cikin jeji kuma ya ɓoye a cikin wani ƙogo. A ganinka me ya sa ya yi hakan?— Domin ya ji tsoro. Amma bai kamata Iliya ya ji tsoro ba. Me ya sa? Domin ya san cewa Jehobah zai iya taimakonsa. Jehobah ya taɓa nuna wa Iliya cewa yana da iko. Akwai lokacin da Iliya ya yi addu’a, sai Jehobah ya sa wuta ta sauko daga sama. Saboda haka, Jehobah zai iya taimaka wa Iliya a wannan lokacin ma!
A lokacin da Iliya yake cikin wannan ƙogon, Jehobah ya tambaye shi: ‘Me kake yi a nan?’ Iliya ya ce: ‘Ni kaɗai na rage da ke bauta maka, kuma ina jin tsoro don mutane suna so su kashe ni.’ Iliya yana ganin kamar an kashe duk sauran mutanen da ke bauta wa Jehobah. Amma Jehobah ya ce masa: ‘A’a, hakan ba gaskiya ba ne. Akwai mutane har 7,000 da suke bauta mini. Kada ka ji tsoro. Ina da aiki da yawa da za ka yi mini!’ Kana ganin Iliya ya yi farin cikin jin hakan kuwa?—
Mene ne ka koya daga abin da ya faru da Iliya?— Bai kamata ka ji tsoro kamar kai kaɗai ne ka rage ba. Kana da abokai da suke ƙaunarka kuma suke ƙaunar Jehobah. Ƙari ga haka, Jehobah yana da ƙarfi sosai kuma zai taimake ka a kowane lokaci! Kana murnar sanin cewa Jehobah yana tare da kai a koyaushe?—
KARANTA NASSOSIN NAN
1 Sarakuna 19:3-18
Zabura 145:18
1 Bitrus 5:9