WAƘA TA 30
Jehobah Ubana, Allahna da Abokina
Hoto
(Ibraniyawa 6:10)
1. Muna wahala sosai.
Muna kuka domin ɓacin rai,
Ni ina da tabbaci
“Cewa akwai bege.”
(AMSHI)
Allah mai adalci ne,
Yana tunawa da ƙaunata.
Allah na tare da ni,
Ba zan ji tsoron kome ba.
Shi ne ke kula da ni,
yana kāre ni a koyaushe.
Ai, Jehobah ne Ubana,
Abokina.
2. A dā ni matashi ne,
Yanzu kuma na tsufa sosai.
Amma ina da bege
Na rai har abada.
(AMSHI)
Allah mai adalci ne,
Yana tunawa da ƙaunata.
Allah na tare da ni,
Ba zan ji tsoron kome ba.
Shi ne ke kula da ni,
yana kāre ni a koyaushe.
Ai, Jehobah ne Ubana,
Abokina.
(Ka kuma duba Zab. 71:17, 18.)