WAƘA TA 56
Ka Riƙe Gaskiya
(Misalai 3:1, 2)
1. Bauta wa Allah shi ne abu mafi kyau,
Amma kai ne za ka yi zaɓin.
Don haka ka bi dukan umurnin Allah,
Ka nuna aminci sosai.
(AMSHI)
Ka bauta masa.
Ka yi da duk zuciya.
Jehobah zai yi
Maka albarka
In ka riƙe gaskiya.
2. Duk ƙoƙarinka da ayyukan da ka yi
A bautar Allah da Mulkinsa,
Za su sa Allah ya yi maka albarka,
Ka sami rai har abada.
(AMSHI)
Ka bauta masa.
Ka yi da duk zuciya.
Jehobah zai yi
Maka albarka
In ka riƙe gaskiya.
3. Mu duka muna kamar ’ya’ya gun Allah,
Dole mu bi ja-gorancinsa.
Ka yi tafiya da Ubanmu na sama
Don ka sami albarkarsa.
(AMSHI)
Ka bauta masa.
Ka yi da duk zuciya.
Jehobah zai yi
Maka albarka
In ka riƙe gaskiya.
(Ka kuma duba Zab. 26:3; Mis. 8:35; 15:31; Yoh. 8:31, 32.)