Nuwamba
Talata, 1 ga Nuwamba
Wanda ya amsa magana tun bai ji ba, wawanci ne da abin kunyarsa.—K. Mag. 18:13.
Da yake ba mu fahimci yanayin Yunana sosai ba, muna iya ɗauka cewa ba shi da aminci. Jehobah ya umurce shi ya sanar da hukuncinsa a kan mutanen Nineba. Maimakon Yunana ya bi umurnin da aka ba shi, sai ya shiga jirgin ruwa da ke zuwa wani wuri dabam kuma “ya gudu daga gaban Yahweh.” (Yona 1:1-3) Da a ce kai ne, za ka ba Yunana wata damar yin biyayya ga Jehobah? Wataƙila ba za ka yi hakan ba. Amma Jehobah ya ga ya dace ya sake ba Yunana wani zarafi. (Yona 3:1, 2) Addu’ar da Yunana ya yi ta nuna abin da ke cikin zuciyarsa. (Yona 2:1, 2, 9) Babu shakka, Yunana ya yi addu’a ga Jehobah sau da yawa. Amma addu’ar da ya yi sa’ad da yake cikin kifi ta taimaka mana mu san halayensa masu kyau. Furucinsa ya nuna cewa shi mai sauƙin kai ne, mai nuna godiya kuma yana shirye ya yi biyayya ga Jehobah. Shi ya sa Jehobah bai mai da hankali ga kuskuren Yunana ba. Maimakon haka, ya amsa addu’arsa kuma ya ci gaba da zama annabi! Yana da muhimmanci cewa kowane dattijo ya “ji” ainihin abin da ya faru kafin ya ba da shawara! w20.04 15 sakin layi na 4-6
Laraba, 2 ga Nuwamba
[Bulus ya yi] muhawara da su daga cikin Rubutacciyar Maganar Allah. Yana yi musu bayani, yana kuma tabbatar musu.—A. M. 17:2, 3.
Kiristoci a ƙarni na farko sun amince da wannan koyarwar kuma sun dogara ga ruhu mai tsarki ya taimaka musu su fahimci Kalmar Allah. Sun yi bincike don su tabbatar wa kansu cewa koyarwar daga Littafi Mai Tsarki ne. (A. M. 17:11, 12; Ibran. 5:14) Bangaskiyarsu ba ta dangana ga yadda suke ji ba kawai ko kuma don suna farin ciki sa’ad da suka yi cuɗanya da ’yan’uwansu. Maimakon haka, sun kasance da bangaskiya don sun ‘san Allah’ sosai. (Kol. 1:9, 10) Gaskiyar da ke cikin Kalmar Allah ba ta canjawa. (Zab. 119:160) Alal misali, ba ta canjawa idan wani ɗan’uwa ya ɓata mana rai ko kuma ya yi zunubi mai tsanani. Kuma ba ta canjawa sa’ad da muke fuskantar matsaloli. Saboda haka, ya kamata mu san koyarwar Littafi Mai Tsarki sosai, kuma mu tabbatar wa kanmu cewa koyarwar gaskiya ce. Idan muna da bangaskiya sosai, za mu kasance da aminci ga Jehobah sa’ad da muke fuskantar matsaloli. w20.07 9 sakin layi na 6-7
Alhamis, 3 ga Nuwamba
Ya . . . umarce mu mu yi wa mutane wa’azi, mu kuma yi shaida.—A. M. 10:42.
Idan mun goyi bayan shafaffu, Yesu yana ɗaukan hakan a matsayin alherin da muka yi masa. (Mat. 25:34-40) Hanya mafi muhimmanci da za mu iya goyon bayan shafaffu ita ce ta almajirtarwa kamar yadda Yesu ya umurci mabiyansa su yi. (Mat. 28:19, 20) Sai da taimakon “waɗansu tumaki” ne shafaffu za su iya cim ma wa’azin da aka ce su yi. (Yoh. 10:16) Idan kana sa ran yin rayuwa a duniya, za ka nuna cewa kana ƙaunar shafaffu da kuma Yesu a duk lokacin da ka fita wa’azi. Ƙari ga haka, muna iya zama abokan Jehobah da kuma Yesu ta wajen yin amfani da dukiyarmu don mu tallafa wa hidimarsu. (Luk. 16:9) Alal misali, za mu iya tallafa wa aikin da ake yi a faɗin duniya da gudummawar kuɗi. Ana yin amfani da kuɗaɗen nan don tanadar da kayan agaji ga waɗanda bala’i ya shafa. Ƙari ga haka, za mu iya ba da gudummawar kuɗi don mu tallafa wa ikilisiyarmu da kuma ikilisiyoyin da muka san cewa suna da bukata.—K. Mag. 19:17. w20.04 24 sakin layi na 12-13
Jumma’a, 4 ga Nuwamba
Ba zai kula da gumakan kakanninsa ba. . . . A maimakon haka zai girmama allahn wurare masu katanga.—Dan. 11:37, 38.
Don a cika wannan annabcin, sarkin arewa ya nuna bai damu da “gumakan kakanninsa ba.” Ta yaya? Tarayyar Soviet tana so ta kawar da addinai, saboda haka, ta yi ƙoƙarin ƙwace ikonsu. Don ta cim ma hakan, tun daga shekara ta 1918, gwamnatin Tarayyar Soviet ta ba da umurni da ya sa aka soma koyarwa a makarantu cewa Allah ba ya wanzuwa. Ta yaya wannan sarkin arewa ya “girmama allahn wurare masu katanga”? Tarayyar Soviet ta kashe kuɗaɗe sosai don ta horar da sojojinta da kuma gina dubban makaman nukiliya domin ta sami iko sosai. A ƙarshe, sarakunan nan biyu suna da makamai masu ɗimbin yawa da za su iya amfani da su wajen kashe biliyoyin mutane! Sarkin arewa da sarkin kudu sun yi aiki tare don “su kafa abin ƙazanta mai kawo halakarwa,” wato, Majalisar Ɗinkin Duniya.—Dan. 11:31. w20.05 6-7 sakin layi na 16-17
Asabar, 5 ga Nuwamba
Ɗan’uwanka nan . . . dā ya ɓace, amma yanzu an same shi.—Luk. 15:32.
Wane ne zai iya taimaka wa waɗanda suka daina fita wa’azi da halartan taro? Duk masu shela a ikilisiya za su iya taimakawa don a nemi waɗanda suka bijire, har da dattawa da majagaba da kuma dangin ’yan’uwan da suka bijire. Shin akwai wani abokinka ko danginka da ya bijire? Ka taɓa haɗuwa da wani da ya bijire a lokacin da kake wa’azi gida-gida ko kuma a wurin da jama’a suke? Ka bayyana wa mutumin cewa idan zai so wani ya ziyarce shi, za ka ba dattawan ikilisiyarku adireshinsa ko kuma lambar wayarsa. Wani dattijo mai suna Thomas ya ce: “Da farko, ina tambayar ’yan’uwa cewa ko sun san wuraren da waɗanda suka bijire suke da zama. Ko kuma in tambaye su ko sun san wasu da suka daina halartan taro. Daga baya, idan na ziyarci waɗanda suka bijire, ina tambayar su yadda yaransu da kuma iyalinsu suke. Wasu da suka bijire suna kawo yaransu taro a dā kuma wataƙila yaran masu shela ne a lokacin. Su ma suna bukatar taimako.” w20.06 24 sakin layi na 1; 25 sakin layi na 6-7
Lahadi, 6 ga Nuwamba
Ya Yahweh, zan tuna da manyan ayyukanka. I, na tuna da ayyukan ban mamaki abubuwan da ka aikata a dā.—Zab. 77:11.
A cikin dukan halittun da ke duniya, ʼyan Adam ne kaɗai suke iya koyan darussa ta wajen tunawa da abubuwa da suka taɓa faruwa da kuma yin la’akari da su. A sakamakon haka, muna iya koyan ƙa’idodi masu kyau, mu canja tunaninmu da salon rayuwarmu. (1 Kor. 6:9-11; Kol. 3:9, 10) Muna iya horar da zuciyarmu don ta san abu mai kyau da marar kyau. (Ibran. 5:14) Za mu iya koyan nuna ƙauna da tausayi da kuma jin ƙai. Kuma za mu iya koyan nuna adalci. Hanya ɗaya da za mu nuna godiya don wannan baiwar tunawa da abu ita ce ta wajen tuna cewa Jehobah ya taimaka da kuma ƙarfafa mu a dā. Hakan zai tabbatar mana da cewa zai taimaka mana a nan gaba. (Zab. 77:12; 78:4, 7) Wata hanya kuma ita ce ta wajen tunawa da alherin da mutane suka yi mana da kuma nuna godiya. Binciken da aka yi ya nuna cewa mutanen da ke nuna godiya sun fi farin ciki. w20.05 23 sakin layi na 12-13
Litinin, 7 ga Nuwamba
Ku ji tsoron sunan nan mai ɗaukaka mai ban tsoro, wato sunan Yahweh Allahnku.—M. Sha. 28:58.
Ka yi tunanin yadda Musa ya ji a lokacin da yake kan dutse kuma ya ga ɗaukakar Jehobah. Littafin nan Insight on the Scriptures ya ce: “Babu shakka wannan ne abu mafi ban-mamaki da ɗan Adam ya taɓa gani kafin Yesu ya zo duniya.” Musa ya ji furucin nan: “Ni ne Ubangiji, Ubangiji Allah mai jinƙai, mai alheri, mai jinkirin fushi, mai yawan ƙauna, mai gaskiya. Ni ne mai nuna ƙauna ga dubbai, mai gafarta mugunta, da laifi, da zunubi.” (Fit. 33:17-23; 34:5-7, Littafi Mai Tsarki) Yayin da Musa yake kiran sunan Jehobah kamar yadda aka nuna a nassin yini na yau, wataƙila ya tuna abin da ya faru ne a lokacin can. A duk lokacin da muka yi tunani game da sunan nan Jehobah, ya kamata mu yi tunani a kan mai sunan. Muna bukatar mu yi tunani a kan ikonsa da hikimarsa da adalcinsa da kuma ƙaunarsa. Idan muka yi tunani a kan waɗannan halaye da kuma wasu, hakan zai taimaka mana mu riƙa daraja Jehobah sosai.—Zab. 77:11-15. w20.06 8-9 sakin layi na 3-4
Talata, 8 ga Nuwamba
Ka ci gaba da abin da ka koya, ka kuma tabbatar da gaskiyar koyarwar.—2 Tim. 3:14.
Yesu ya ce za a san almajiransa ta ƙauna da suke nuna wa juna. (Yoh. 13:34, 35) Amma akwai ƙarin abubuwa da muke bukatar mu yi don mu ƙarfafa bangaskiyarmu. Bai kamata mu kasance da bangaskiya don ƙaunar da mutanen Allah suke nuna wa juna kawai ba. Me ya sa? Don muna iya daina bauta wa Jehobah idan wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa, wataƙila dattijo ko majagaba ya yi zunubi mai tsanani. Muna kuma iya yin hakan idan wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ta ɓata mana rai, ko wani ya yi ridda, kuma ya ce muna koyar da ƙarya. Saboda haka, idan kana so ka kasance da bangaskiya sosai, wajibi ne ka ƙulla abota na kud da kud da Jehobah. Idan bangaskiyarka ta dangana ga abin da wasu suke yi ba don kana da dangantaka da Jehobah ba, bangaskiyarka ba za ta yi ƙarfi ba. Ra’ayinka game da Jehobah da mutanensa zai taimaka maka ka kasance da bangaskiya. Amma yana da muhimmanci ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki sosai, ka fahimci abin da kake koya kuma ka yi bincike. Yin hakan zai sa ka tabbatar wa kanka cewa abin da kake koya game da Jehobah gaskiya ne.—Rom. 12:2. w20.07 8 sakin layi na 2-3
Laraba, 9 ga Nuwamba
Mu taimaka wa marasa ƙarfi.—A. M. 20:35.
Da akwai misalai da yawa da suka nuna cewa mala’iku suna taimaka mana mu nemi mutanen da suka daina fita wa’azi da halartan taro da suke so su komo ga Jehobah. (R. Yar. 14:6) Alal misali, wani ɗan’uwa mai suna Silvio daga ƙasar Ecuador da ya daina fita wa’azi da halartan taro ya roƙi Jehobah ya taimaka masa ya dawo ƙungiyarsa. A lokacin da yake addu’ar, dattawa biyu sun ƙwanƙwasa ƙofarsa. Sa’ad da suka ziyarce shi sun yi farin cikin soma taimaka masa ya komo ga Jehobah. Za mu yi farin ciki sosai idan muka taimaka wa mutanen da suka bijire su komo ga Jehobah. Wani majagaba mai suna Salvador da yake taimaka wa mutanen da suka bijire ya ce: “A wasu lokuta, ina zub da hawaye don farin ciki. Ina farin ciki cewa na yi aiki tare da Jehobah wajen taimaka wa ɗaya cikin tumakinsa ya komo gare shi.” Idan ka daina cuɗanya da bayin Jehobah, ka kasance da tabbaci cewa har yanzu, Jehobah yana jira ka komo gare shi kuma zai marabce ka sosai. w20.06 29 sakin layi na 16-18
Alhamis, 10 ga Nuwamba
Za ku ga Malaminku.—Isha. 30:20.
Da yake Jehobah ‘Malaminmu’ ne Mafi Girma, ya tanadar mana misalai a Kalmarsa don ya koyar da mu. (Isha. 30:21) Muna koyon darussa yayin da muke yin bimbini a kan labaran Littafi Mai Tsarki game da waɗanda suke da halayen da ke faranta ran Allah. Ban da haka, muna koyan darasi yayin da muka bincika abin da ya faru da waɗanda suka ƙi kasancewa da halayen nan masu kyau. (Zab. 37:37; 1 Kor. 10:11) Ka yi tunani a kan abin da ya faru da Sarki Saul. Shi matashi ne mai tawali’u. Ya san kasawarsa kuma ya yi jinkirin karɓan ƙarin matsayi. (1 Sam. 9:21; 10:20-22) Amma, da shigewar lokaci Saul ya zama mai girman kai. Ya nuna wannan mugun halin ba da daɗewa ba bayan ya zama sarki. Akwai lokacin da ya ƙi yin haƙuri sa’ad da yake jiran annabi Sama’ila kuma ya miƙa hadayar ƙonawa duk da cewa ba shi da izinin yin hakan. Saboda haka, Saul ya ɓata ran Jehobah kuma ya ƙi shi a matsayin sarki. (1 Sam. 13:8-14) Zai dace mu koyi darasi daga wannan misalin kuma mu guji yin abubuwan da ba mu da ikon yi. w20.08 10 sakin layi na 10-11
Jumma’a, 11 ga Nuwamba
Ku ba masu fama da aiki a cikinku girma, wato, shugabanninku cikin Ubangiji.—1 Tas. 5:12.
Gaskiya ne cewa Jehobah ya yi amfani da Yesu don ya ba da “baiwa” ga ikilisiya. (Afis. 4:8) Wannan “baiwa” ta haɗa da Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu da masu taimaka musu da Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu da masu kula da da’ira da masu koyarwa a makarantun ƙungiyar Jehobah da dattawa da kuma bayi masu hidima. An naɗa duka ’yan’uwan nan da ruhu mai tsarki don su kula da tumakin Jehobah kuma su ƙarfafa su. (1 Bit. 5:2, 3) Ana naɗa ’yan’uwa da ruhu mai tsarki don su yi ayyuka dabam-dabam a ikilisiya. Kamar yadda gaɓoɓin jiki, wato hannaye da ƙafafu suke aiki tare don jikin mutum gabaki ɗaya ya amfana, haka ma ’yan’uwan da aka naɗa su da ruhu mai tsarki suke aiki tuƙuru don ’yan’uwa a ikilisiya su amfana. Ba sa yin hakan don a riƙa ɗaukaka su. A maimakon haka, suna iya ƙoƙarinsu don su ƙarfafa ’yan’uwa. (1 Tas. 2:6-8) Muna yi wa Jehobah godiya don waɗannan ’yan’uwa da suka fi mai da hankali ga bukatun wasu fiye da nasu! w20.08 21 sakin layi na 5-6
Asabar, 12 ga Nuwamba
Ku je . . . ku sa su zama almajiraina.—Mat. 28:19.
Ɗaya daga cikin dalilai da suka sa muke wa’azi shi ne, domin mutane “suna shan wahala kuma ba mai taimako.” Don haka, suna bukatar su koyi gaskiya game da Mulkin Allah. (Mat. 9:36) Jehobah yana so dukan mutane su san gaskiya domin su sami ceto. (1 Tim. 2:4) Za mu so yin wa’azi idan muka yi tunanin yadda yin hakan zai ceci mutane. (Rom. 10:13-15; 1 Tim. 4:16) Muna bukatar kayan aikin da suka dace don yin wa’azi. Kuma muna bukatar mu san yadda za mu yi amfani da su. Yesu ya koya wa almajiransa yadda za su yi wa’azi. Ya gaya musu abin da bai kamata su ɗauka ba da inda za su yi wa’azi da kuma abin da za su faɗa. (Mat. 10:5-7; Luk. 10:1-11) A yau, ƙungiyar Jehobah ta yi mana tanadin abubuwan da za su taimaka mana mu yi koyarwa da kyau. Kuma ana koya mana yadda za mu yi amfani da su. Wannan koyarwar tana taimaka mana mu kasance da ƙarfin zuciya kuma mu ƙware a yin wa’azi.—2 Tim. 2:15. w20.09 4 sakin layi na 6-7, 10
Lahadi, 13 ga Nuwamba
Ba abin da ya fi sa ni farin ciki fiye da in ji cewa ’ya’yana suna bin gaskiya.—3 Yoh. 4.
Babu shakka, manzo Yohanna ya yi farin ciki sosai sa’ad da ya ji cewa mutanen da ya taimaka musu su koyi gaskiya sun ci gaba da bauta wa Jehobah. Kiristocin nan masu aminci da Yohanna ya ɗauka kamar ʼya’yansa sun fuskanci ƙalubale da yawa, kuma Yohanna ya ƙoƙarta sosai don ya ƙarfafa su. Hakazalika, muna matuƙar farin ciki sa’ad da yaranmu ko kuma mutanen da muka koya wa gaskiya suka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma suka ci gaba da bauta masa. (3 Yoh. 3) A wajen shekara ta 98 kafin haihuwar Yesu, ruhu mai tsarki ya sa Yohanna ya rubuta wasiƙu uku. Ya rubuta wasiƙun ne don ya taimaka wa Kiristoci su riƙe amincinsu kuma su ci gaba da bin gaskiya. Yohanna ne ya fi tsawon rayuwa a cikin manzannin Yesu kuma ya damu sosai don yadda malaman ƙarya suke gurɓata ikilisiyoyi. (1 Yoh. 2:18, 19, 26) ʼYan ridda sun yi da’awar sanin Allah, amma ba sa bin dokokinsa. w20.07 20 sakin layi na 1-3
Litinin, 14 ga Nuwamba
Ku ba da gaskiya ga Allah, ku kuma ba da gaskiya gare ni.—Yoh. 14:1.
Mun gaskata da saƙon da muke wa’azin sa. Saboda haka, muna ɗokin gaya wa mutane da yawa saƙon. Mun gaskata da alkawuran da ke cikin Kalmar Allah. (Zab. 119:42; Isha. 40:8) Ban da haka, muna ganin cikar annabcin Littafi Mai Tsarki a zamaninmu. Mun ga yadda mutane suka kyautata rayuwarsu sa’ad da suka soma bin shawarar Littafi Mai Tsarki. Hakan ya taimaka mana mu gaskata cewa ya kamata kowa ya ji wa’azi game da Mulkin Allah. Mun kuma yi imani da Allahn da ke da saƙon da muke wa’azi a kai, da kuma Ɗansa Yesu da ya naɗa a matsayin Sarkin Mulkinsa. Jehobah zai ci gaba da zama mafakarmu ko da wane yanayi ne muke ciki. (Zab. 46:1-3) Ƙari ga haka, muna da tabbaci cewa Yesu yana mana ja-goranci a wa’azin da muke yi kuma yana amfani da ikon da Jehobah ya ba shi. (Mat. 28:18-20) Kasancewa da bangaskiya zai sa mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai albarkace mu. w20.09 12 sakin layi na 15-17
Talata, 15 ga Nuwamba
Ai, abu mai kyau ne ta yi mini. . . . Ta yi iyakacin ƙoƙarinta.—Mar. 14:6, 8.
A wasu lokuta, ’yan’uwa mata za su bukaci wanda zai kāre su sa’ad da suke cikin wata matsala. (Isha. 1:17) Alal misali, wata gwauruwa ko wadda aurenta ya mutu tana iya bukatar wani da zai taimaka mata ta yi wasu abubuwa da mijinta yake yi a dā. ’Yar’uwa da ta tsufa tana iya bukatar taimako don tattaunawa da likita. Ko kuma ’yar’uwa majagaba za ta bukaci wani ya kāre ta idan aka ce ba ta fita wa’azi kamar yadda sauran majagaba suke yi. A wace hanya ce kuma za mu iya taimaka wa ’yan’uwa mata? Bari mu tattauna misalin Yesu. Yesu ya yi saurin kāre mata a lokacin da mutane ba su fahimce su ba. Alal misali, ya kāre Maryamu sa’ad da Marta ta yi gunaguni game da ita. (Luk. 10:38-42) Yesu ya sake kāre ta sa’ad da wasu suka ce ta yi abin da bai dace ba. (Mar. 14:3-9) Yesu ya fahimci abin da ke zuciyar Maryamu kuma ya yaba mata. Ya ma annabta cewa za a riƙa faɗin abin da ta yi a “duk inda za a yi shelar labarin nan mai daɗi a duniya duka.” w20.09 24 sakin layi na 15-16
Laraba, 16 ga Nuwamba
Ina roƙonku, ku yi kiwon garken Allah da aka danƙa muku amanarsa, kuna kuma yi musu shugabanci. Kada ku ga kamar ana sa ku tilas ne, amma ku yi shi da yardar ranku yadda Allah yake so.—1 Bit. 5:2.
Makiyayi nagari ya san cewa tunkiya za ta iya ɓacewa. Idan tunkiya ta ɓata, makiyayin ba zai wulaƙanta ta ba. Ka yi la’akari da misalin da Allah ya kafa sa’ad da yake taimaka wa wasu cikin bayinsa da suka ɗan bijire. Annabi Yunana ba ya so ya yi aikin da Jehobah ya ba shi. Amma, Jehobah bai ƙi Yunana ba. Kamar makiyayi nagari, Jehobah ya cece shi kuma ya taimaka masa ya samu ƙarfin da yake bukata don ya yi aikin da aka ba shi. (Yona 2:7; 3:1, 2) Daga baya, Allah ya yi amfani da wani ɗan tsiro don ya taimaka wa Yunana ya fahimci cewa ran ’yan Adam yana da daraja. (Yona 4:10, 11) Wane darasi ne muka koya? Bai kamata dattawa su yi saurin yasar da waɗanda suka bijire ba. A maimakon haka, suna ƙoƙari su fahimci dalilin da ya sa ’yan’uwan suka bijire daga garken. Kuma sa’ad da suka komo ga Jehobah, dattawa za su ci gaba da nuna musu ƙauna. w20.06 20-21 sakin layi na 10-12
Alhamis, 17 ga Nuwamba
Za su ɗan sami ƙarfafawa.—Dan. 11:34.
Bayan da Tarayyar Soviet ta rugurguje a shekara ta 1991, bayin Allah da ke zama a waɗannan yankunan sun “ɗan sami ƙarfafawa,” wato sun ɗan sami ’yanci. A sakamakon haka, sun sami zarafin yin wa’azi a sake, kuma ba da daɗewa ba, adadin masu shela ya ƙaru sosai a yankunan. Amma bayan ʼyan shekaru, Rasha da magoya bayanta sun zama sarkin arewa. Kafin wata gwamnati ta zama sarkin arewa ko sarkin kudu, dole ta yi abubuwan nan uku: (1) sarakunan za su sarauci ƙasashen da mutanen Allah suke zama ko kuma su tsananta musu, (2) yadda za su bi da mutanen zai nuna cewa sun tsani Allah, kuma (3) za su riƙa yin jayayya da juna. Rasha da magoya bayanta sun kai wa bayin Allah hari ta wajen saka wa aikinsu takunkumi da kuma tsananta wa dubban ʼyan’uwa. Waɗannan abubuwa sun nuna cewa sun tsani Jehobah da mutanensa. Ƙari ga haka, suna yin jayayya da sarkin kudu, wato Amirka da Birtaniya. w20.05 12-13 sakin layi na 3-4
Jumma’a, 18 ga Nuwamba
Ka lura sosai da . . . koyarwarka.—1 Tim. 4:16.
Muna bukatar mu ƙware a koyarwa kafin mu iya almajirtar da mutane. Muna nazari da miliyoyin mutane a faɗin duniya. Muna daraja abin da muke koya wa mutane daga Kalmar Allah. Saboda haka, za mu iya so mu yi dogon jawabi sa’ad a muke koyar da mutane. Amma bai kamata mu riƙa hakan ba sa’ad da muke gudanar da nazarin Hasumiyar Tsaro ko Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya ko kuma nazari da ɗalibinmu. Idan malami yana so ya yi amfani da Littafi Mai Tsarki a koyarwarsa, ya kamata ya mai da hankali don kada ya bayyana kome-da-kome da ya sani a kan wata aya ko kuma wani batu. (Yoh. 16:12) Ka yi tunani a kan yawan ilimin da kake da shi sa’ad da ka yi baftisma da kuma wanda kake da shi yanzu. Babu shakka, ka koyi abubuwa masu sauƙi a lokacin. (Ibran. 6:1) Ka yi shekaru da yawa kafin ka koyi abubuwan da ka sani a yau. Saboda haka, kada ka yi ƙoƙarin koya wa ɗalibinka kome a lokaci ɗaya. w20.10 14-15 sakin layi na 2-4
Asabar, 19 ga Nuwamba
Wannan . . . shi ne kafintan nan . . . ɗan Maryamu.—Mar. 6:3.
Jehobah ya zaɓi iyaye mafi dacewa da za su haifi Yesu. (Mat. 1:18-23; Luk. 1:26-38) Furucin Maryamu a Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa tana ƙaunar Jehobah da kuma Kalmarsa. (Luk. 1:46-55) Kuma yadda Yusufu ya bi ja-gorancin Jehobah ya nuna cewa yana tsoron Allah kuma yana so ya faranta masa rai. (Mat. 1:24) Ka lura cewa Jehobah bai zaɓi iyaye masu arziki don su haifi Yesu ba. Hadayar da Yusufu da Maryamu suka miƙa bayan an haifi Yesu ya nuna cewa su talakawa ne. (Luk. 2:24) Da alama cewa ba su da kuɗi da kuma kayayyaki sosai, musamman da yake suna da aƙalla yara bakwai. (Mat. 13:55, 56) Jehobah ya kāre Yesu daga wasu haɗarurruka, amma bai kāre shi daga dukan ƙalubale ba. (Mat. 2:13-15) Alal misali, wasu cikin dangin Yesu ba su yarda da koyarwarsa ba, kuma ba su yarda cewa shi ne Almasihu ba. (Mar. 3:21; Yoh. 7:5) Kuma wataƙila Yusufu ya rasu sa’ad da Yesu yake matashi, kuma hakan ya sa shi baƙin ciki sosai. w20.10 26-27 sakin layi na 4-6
Lahadi, 20 ga Nuwamba
Har abada ba zan bar ka ba, sam sam ba zan yar da kai ba.—Ibran. 13:5.
Ka taɓa ji kamar babu wanda zai taimaka maka ka jimre matsalolin da kake fuskanta? Mutane da yawa sun taɓa jin hakan, har da bayin Jehobah masu aminci. (1 Sar. 19:14) Idan hakan ya faru da kai, ka tuna alkawarin da Jehobah ya yi. Ya ce: “Har abada ba zan bar ka ba, sam sam ba zan yar da kai ba.” Shi ya sa, ba tare da shakka ba, muna iya cewa: “Ubangiji mai taimakona ne, ba zan ji tsoro ba.” (Ibran. 13:5, 6) Manzo Bulus ya rubuta waɗannan kalmomi ga Kiristocin da ke Yahudiya a wajen shekara ta 61 bayan haihuwar Yesu. Kalmominsa sun tuna mana da abin da wani marubucin zabura ya ce a Zabura 118:5-7. Kamar wannan marubucin zabura, Bulus ya san cewa Jehobah zai taimaka masa domin ya yi hakan a dā. Alal misali, shekaru biyu kafin ya rubuta wasiƙa ga Ibraniyawa, Bulus ya tsira daga muguwar guguwa sa’ad da yake tafiya a jirgin ruwa. (A. M. 27:4, 15, 20) Shekaru da yawa kafin wannan tafiyar, Jehobah ya taimaka masa a hanyoyi da yawa. w20.11 12 sakin layi na 1-2
Litinin, 21 ga Nuwamba
Kada ka ce, “Me ya sa kwanakin dā sun fi na yanzu?”—M. Wa. 7:10.
Me ya sa ba zai dace mu riƙa tunanin cewa rayuwarmu a dā ta fi na yanzu ba? Irin wannan tunanin zai sa mu fi mai da hankali ga abubuwa masu kyau da suka faru da mu a dā. Ka yi la’akari da abin da ya faru da Isra’ilawa a zamanin dā. Bayan sun bar ƙasar Masar, sun yi saurin mance irin wahalar da suka sha a ƙasar. Amma suka mai da hankali ga abinci masu kyau da suke ci a ƙasar. Suka ce: “Mun tuna yadda a ƙasar Masar muka ci kifi kyauta. Mun kuma tuna da su kakamba, da kabewa, da albasa mai ganye da mai ƙwaya, da tafarnuwa.” (L. Ƙid. 11:5) Amma gaskiya ne cewa “kyauta” ce suke ci waɗannan abubuwan? A’a. Isra’ilawan sun sha wahala sosai domin a lokacin su bayi ne a ƙasar Masar. (Fit. 1:13, 14; 3:6-9) Daga baya, sun mance da wahalolin da suka sha kuma suka so rayuwarsu ta kasance yadda take a dā. Sun mai da hankali ga abubuwan da suka ji daɗinsa a dā maimakon abin da Jehobah ya yi musu. Hakan ya ɓata wa Jehobah rai.—L. Ƙid. 11:10. w20.11 25 sakin layi na 5-6
Talata, 22 ga Nuwamba
Ga waɗanda an karya musu ƙarfin gwiwa, Yahweh yana kusa da su, yakan kuɓutar da masu fid da zuciya.—Zab. 34:18.
A wasu lokuta, muna tunani a kan yadda kwanakin rayuwarmu ba su da yawa. Da kuma yadda rayuwarmu ke cike da “wahala.” (Ayu. 14:1) Babu shakka, hakan na sa mu sanyin gwiwa. Bayin Jehobah da yawa ma a dā sun yi sanyin gwiwa. Wasu ma sun gwammace su mutu. (1 Sar. 19:2-4; Ayu. 3:1-3, 11; 7:15, 16) Amma Jehobah, Allahn da muke dogara gare shi yana ƙarfafa mu a kowane lokaci. Jehobah ya sa a rubuta labaransu domin idan mun karanta su, za mu sami ƙarfafa. (Rom. 15:4) Ka tuna da Yusufu ɗan Yakubu. A cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, rayuwar Yusufu ta canja gabaki ɗaya. Ba ya tare da babansa da ke ƙaunar sa, kuma ya zama bawan wani mutum a ƙasar Masar da ba ya bauta wa Jehobah, kuma ana wulaƙanta shi sosai. (Far. 37:3, 4, 21-28; 39:1) Sai matar Fotifar ta ɗora masa sharri cewa yana so ya yi mata fyaɗe. A lokacin da Fotifar ya ji labarin, bai yi bincike don ya san gaskiyar lamarin ba. Ya yanke hukunci a kan Yusufu kuma ya jefa shi cikin kurkuku. (Far. 39:14-20; Zab. 105:17, 18) Babu shakka, abubuwan nan sun sa Yusufu sanyin gwiwa sosai. w20.12 16-17 sakin layi na 1-4
Laraba, 23 ga Nuwamba
A kiyaye sunanka da tsarki.—Mat. 6:9.
Yesu ya ce ya kamata tsarkake sunan Allah ya zama abu mafi muhimmanci da za mu yi addu’a a kai. Me Yesu yake nufi? A tsarkake wani abu yana nufi a sa ya kasance da tsarki ko kuma tsabta. Amma, wasu suna iya cewa, ‘Ai sunan Allah yana da tsarki da kuma tsabta!’ Muna bukatar mu yi tunani a kan abin da suna ya ƙunsa. Suna ba kalma ba ce da ake rubutawa ko furtawa kawai ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gwamma suna mai kyau da samun dukiya.” (K. Mag. 22:1; M. Wa. 7:1) Me ya sa suna yake da muhimmanci sosai? Domin ya ƙunshi ayyuka da halaye da kuma yadda mutane suke ganin mai sunan. Don haka, yadda ake rubuta suna ko furta shi ba shi ne yake da muhimmanci ba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne abin da mutane suke tunaninsa sa’ad da suka ga an rubuta wani suna ko suka ji an furta sunan. Sa’ad da mutane suka ga munanan abubuwa suna faruwa, suna ɗora wa Jehobah laifi kuma ta hakan suna ɓata sunansa. w20.06 3 sakin layi na 5-7
Alhamis, 24 ga Nuwamba
Ya Yahweh, zuciyata ta damu ƙwarai, har yaushe zan yi ta jira?—Zab. 6:3.
Matsaloli za su iya shawo kanmu kuma su sa mu damuwa sosai. Alal misali, muna iya damuwa cewa ba mu da isashen kuɗin biyan bukatunmu ko za mu yi rashin lafiya ko kuma mu rasa aikinmu. Muna iya damuwa cewa idan an jarraba mu, ba za mu kasance da aminci ga Jehobah ba. Kuma nan ba da daɗewa ba, Shaiɗan da magoya bayansa za su kai wa mutanen Allah hari. Saboda haka, muna iya damuwa game da abin da za mu yi a lokacin. Muna iya tunanin cewa, ‘Laifi ne in riƙa damuwa game da abubuwan nan?’ Yesu ya gaya wa mabiyansa cewa: “Kada ku damu.” (Mat. 6:25) Hakan yana nufin cewa Yesu ba ya so mu damu game da kome ne? A’a! Ka tuna cewa a zamanin dā, wasu bayin Jehobah sun damu, amma Jehobah bai yi fushi da su ba. (1 Sar. 19:4) Yesu yana ƙarfafa mu ne. Ba ya so mu riƙa damuwa ainun game da biyan bukatunmu har hakan ya shafi ibadarmu ga Jehobah. w21.01 3 sakin layi na 4-5
Jumma’a, 25 ga Nuwamba
Miji shi ne shugaban matarsa.—1 Kor. 11:3.
Miji ne zai ba da lissafi ga Jehobah da Yesu a kan yadda ya yi sha’ani da iyalinsa. (1 Bit. 3:7) Da yake Jehobah ne Maɗaukaki, yana da ikon kafa wa ’ya’yansa dokoki, kuma ya tabbata cewa sun bi dokokin. (Isha. 33:22) Yesu wanda shi ne shugaban ikilisiyar Kirista yana da ikon kafa dokoki. (Gal. 6:2; Kol. 1:18-20) Kamar Jehobah da Yesu, maigida Kirista yana da ikon tsai da shawarwari don iyalinsa. (Rom. 7:2; Afis. 6:4) Amma ikonsa yana da iyaka. Alal misali, ya kamata ya kafa dokoki da suka jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. (K. Mag. 3:5, 6) Kuma maigida bai da ikon kafa wa mutanen da ba ’yan iyalinsa ba dokoki. (Rom. 14:4) Ƙari ga haka, sa’ad da yaransa suka girma kuma suka bar gida, za su riƙa daraja shi amma ba shi da iko a kansu.—Mat. 19:5. w21.02 2-3 sakin layi na 3-5
Asabar, 26 ga Nuwamba
Ka kula da danginka.—1 Tim. 5:8.
Hanya ɗaya da magidanci zai nuna cewa yana ƙaunar iyalinsa ita ce ta wajen biyan bukatunsu. Amma yana bukatar ya tuna cewa taimaka wa iyalinsa ta kasance da dangantaka mai kyau da Allah shi ne ya fi muhimmanci. (Mat. 5:3) A lokacin da Yesu yake kan gungumen azaba, ya tabbatar cewa an kula da Maryamu. Duk da cewa Yesu yana cikin azaba sosai, ya yi shiri don manzo Yohanna ya riƙa kula da Maryamu. (Yoh. 19:26, 27) Ɗan’uwa wanda shi magidanci ne yana da ayyuka da yawa masu muhimmanci. Yana bukatar ya riƙa aiki tuƙuru a wurin aikinsa don a yabi Jehobah. (Afis. 6:5, 6; Tit. 2:9, 10) Kuma wataƙila yana da ayyuka a ikilisiya, kamar su zuwa ziyarar ƙarfafa da kuma yin ja-goranci a wa’azi. Ƙari ga haka, yana da muhimmanci ya riƙa yin nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai da matarsa da kuma yaransa. Za su nuna godiya domin dukan abubuwan da yake yi don su kasance da ƙoshin lafiya, su riƙa farin ciki kuma su ci gaba da bauta wa Jehobah.—Afis. 5:28, 29; 6:4. w21.01 12 sakin layi na 15, 17
Lahadi, 27 ga Nuwamba
[Macen kirki] tana lura da rayuwar gidanta sosai.—K. Mag. 31:27.
Kalmar Allah ta ce mace mai kirki za ta iya kula da gida, ta sayi gona ta yi shuki kuma ta riƙa kasuwanci. (K. Mag. 31:15, 16, 18) Ita ba baiwa ba ce da ba za ta iya faɗin ra’ayinta ba. Maimakon haka, mijinta yana amincewa da ita kuma ya saurare ta. (K. Mag. 31:11, 26) Idan miji yana daraja matarsa, za ta yi farin cikin yi masa biyayya. Duk da abubuwan da Yesu ya cim ma, bai yi tunanin ya fi ƙarfin yin biyayya ga Jehobah ba. (1 Kor. 15:28; Yoh. 14:28) Hakazalika, mace mai kirki da take yin koyi da Yesu ba za ta ɗauka cewa mijinta zai rena ta idan tana yi masa biyayya ba. Za ta tallafa wa mijinta ba domin tana ƙaunar shi kaɗai ba amma don tana ƙaunar Jehobah da kuma daraja shi. Mace mai yi wa mijinta biyayya ba za ta goyi bayan mijinta idan ya ce ta yi abin da bai jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba. w21.02 11 sakin layi na 14-15; 12 sakin layi na 19
Litinin, 28 ga Nuwamba
Wahala takan jawo jimrewa.—Rom. 5:3.
Bayin Jehobah sun jimre tsanantawa da yawa domin suna ƙaunar sa. Alal misali, a lokacin da majalisar Yahudawa suka ce wa manzannin su daina wa’azi, ƙaunar su ga Allah ta motsa su su “yi wa Allah biyayya fiye da” mutane. (A. M. 5:29; 1 Yoh. 5:3) Irin wannan ƙaunar ta taimaka wa ’yan’uwanmu da hukuma take tsananta musu su kasance da aminci. Maimakon mu yi sanyin gwiwa, muna ganin gata ce a gare mu mu jimre da yadda mutanen duniya suka tsane mu. (A. M. 5:41; Rom. 5:4, 5) Idan danginmu suka tsananta mana, hakan zai kasance da wuya sosai mu jimre. Sa’ad da muka soma nazari, wasu cikinsu suna iya ganin cewa an yaudare mu. Wasu suna iya ganin cewa ba mu san abin da muke yi ba. (Gwada Markus 3:21.) Suna iya soma wulaƙanta mu. Bai kamata hakan ya sa mu mamaki ba. Yesu ya ce: “Mutanen gidan mutum ne kuma za su zama abokan gābansa.”—Mat. 10:36. w21.03 21 sakin layi na 6-7
Talata, 29 ga Nuwamba
Kowa ya kasance mai saurin ji, amma ba mai saurin magana ba —Yak. 1:19.
Idan ka raka wani mai shela yin nazari, ka saurara sosai yayin da malamin da ɗalibin suke tattaunawa. Hakan zai sa ka iya taimaka sa’ad da bukata ta taso. Babu shakka, ya kamata ka yi tunani kafin ka yi magana. Alal misali, ba zai dace ka riƙa dogon jawabi ba ko ka katse wa malamin magana ko kuma ka ta da wani batu dabam ba. Amma za ka iya yin gajeren bayani ko kwatanci ko tambaya da za ta taimaka wa ɗalibin ya fahimci nazarin. A wasu lokuta, za ka iya ganin cewa ba ka da ƙarin bayani. Amma za ka iya yaba wa ɗalibin, ka nuna cewa ka damu da shi, kuma hakan zai taimaka masa ya sami ci gaba. Idan zai dace, ka ɗan gaya wa ɗalibin yadda ka soma bauta wa Jehobah, yadda ka magance wani ƙalubale ko kuma yadda Jehobah ya taimaka maka. (Zab. 78:4, 7) Labarinka zai iya taimaka wa ɗalibin. Zai iya ƙarfafa bangaskiyarsa ko kuma ya sa ya sami ci gaba har ya yi baftisma. w21.03 10 sakin layi na 9-10
Laraba, 30 ga Nuwamba
Ku je ku faɗa wa dukan al’umman duniya su bi ni, ku sa su zama almajiraina.—Mat. 28:19.
Wa ya kamata mu yaba wa idan mun samu sakamako mai kyau a wa’azi? Bulus ya amsa wannan tambayar a lokacin da ya rubuta wa ikilisiyar Korinti cewa: “Ni na shuka, Afollos ya yi ban ruwa, amma Allah ne ya sa shukar ta yi girma. Saboda haka da wanda ya shuka, da wanda ya yi ban ruwan ba a bakin kome suke ba, sai dai Allah kaɗai shi da ya sa shukar ta yi girma.” (1 Kor. 3:6, 7) Kamar Bulus ya kamata mu yaba wa Jehobah don duk wani sakamako mai kyau da muka samu a wa’azi. Ta yaya za mu nuna godiya don gatan ‘yin aiki tare’ da Allah da Kristi da kuma mala’iku? (2 Kor. 6:1) Za mu iya yin hakan ta wajen neman zarafin yi wa mutane wa’azi da ƙwazo. Ba shuka iri na gaskiya kaɗai za mu yi ba, amma za mu yi ban ruwa. Idan akwai wani da yake son saƙon, za mu yi iya ƙoƙarinmu mu ga cewa mun soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Muna murna idan mun ga cewa Jehobah yana taimakon ɗalibin ya canja ra’ayinsa da tunaninsa. w20.05 30 sakin layi na 14, 16-18