Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
Ya Kāre Bauta ta Gaskiya
ILIYA ya kalli jama’a da suke hawan Dutsen Karmel. Har ma da sassafe za a ga talauci da rashin abinci da waɗannan mutane suke fuskanta. Fari na shekara uku da rabi ya ci jikinsu sosai.
A cikin jama’ar akwai annabawan Ba’al su 450 cike da fahariya da kuma baƙar ƙiyayya ga Iliya, annabin Jehobah. Sarauniya Jezebel ta kashe bayin Jehobah da yawa, amma wannan mutumin ya yi tsayin daka wajen gaba da bautar Ba’al. Amma har yaushe? Wataƙila waɗannan firistoci suna ganin shi kaɗai ba zai iya cin nasara a kan dukansu ba. (1 Sarakuna 18:3, 19, 20) Sarki Ahab shi ma ya zo a kan karusarsa ta sarauta. Shi ma ba ya ƙaunar Iliya.
Wannan annabi da ke shi kaɗai zai fuskanci aukuwa na musamman a rayuwarsa. A gaban Iliya yanayin ya kasance na arangama tsakanin nagarta da mugunta da bai taɓa faruwa ba a duniya. Yaya ya ji sa’ad da ranar ta kusa? Ba mutum ba ne marar tsoro, tun da yana “da tabi’a kamar tamu.” (Yaƙub 5:17) Muna da tabbaci game da abu guda: Da yake mutane marasa bangaskiya, da sarkinsu da ya yi ridda, da kuma firistocinsu masu kisa sun kewaye shi, Iliya ya ji shi kaɗai ne ba wanda yake tare da shi.—1 Sarakuna 18:22.
Me kuma ya jefa Isra’ila cikin wannan matsalar? Kuma me za ka iya koya daga wannan labarin a yau? Littafi Mai Tsarki ya aririce mu mu lura da rayuwar bayin Allah masu ibada kuma mu yi “koyi da bangaskiyarsu.” (Ibraniyawa 13:7) Ka yi la’akari yanzu da misalin Iliya?
Gwagwarmaya ta Dogon Lokaci ta Zo Ƙarshenta
A yawancin rayuwarsa Iliya yana kallo sa’ad da aka yi watsi da bautar Jehobah wadda ita ce aba mafi muhimmanci a gare su. Ka gani, Isra’ila ta daɗe tana ƙoƙari ta yi zaɓi tsakanin bauta ta gaskiya da ta ƙarya, tsakanin bautar Jehobah Allah da bautar gumaka na al’umman da suka kewaye su. A zamanin Iliya wannan gwagwarmaya ta ƙara muni.
Sarki Ahab ya auri Jezebel ’yar sarkin Sidon. Jezebel ta kuɗiri aniyar yaɗa bautar Ba’al a ƙasar Isra’ila kuma ta kawar da bautar Jehobah. Ba tare da wani ɓata lokaci ba ta rinjayi Ahab. Ya gina haikali da kuma bagadi ga Ba’al kuma ya yi ja-gora wajen bauta wa wannan allahn arna. Ya ɓata wa Jehobah rai sosai.—1 Sarakuna 16:30-33.a
Menene ya sa bauta Ba’al abin ƙyama ce haka? Ta rinjayi Isra’ila, ta juyar da mutane da yawa daga Allah na gaskiya. Addini ne na lalata da mugunta. Ta ƙunshi yin karuwanci a haikali na maza da mata, sha’awa, da kuma hadayar yara. Jehobah ya mai da martani ta wajen aika Iliya wurin Ahab ya sanar da shi game da fari da zai ci gaba har sai annabin Allah ya sanar da ƙarshensa. (1 Sarakuna 17:1) Shekaru da yawa suka wuce kafin Iliya ya je wurin Ahab ya gaya masa ya tara mutane da kuma annabawan Ba’al a kan dutsen Karmel.
Menene ma’anar wannan gwagwarmaya a gare mu yau? Wasu za su ga cewa wannan labari game da bautar Ba’al ba shi da amfani, tun da ba ma ganin haikali da bagadi na Ba’al a yanzu. Amma wannan ba labari ba ne kawai na zamanin dā. (Romawa 15:4) Kalmar nan “Ba’al” tana nufin “mai shi” ko “mai gida.” Jehobah ya gaya wa mutanensa cewa su zaɓe shi a matsayin “ba’al” ɗin su, ko kuma maigidansu. (Ishaya 54:5) Ka yarda cewa mutane har yanzu suna da masu gidansu waɗanda ba Allah Makaɗaici ba ne? Hakika, ko mutane suna yin amfani da rayuwarsu wajen bautar kuɗi, aiki, nishaɗi, jima’i, ko kuma wasu alloli masu yawa da ake bauta musu mai makon Jehobah, suna zaɓan maigida. (Matta 6:24; Romawa 6:16) Wato, abubuwa da bautar Ba’al ta ƙunsa suna nan a yau. Wannan gwagwarmaya ta dā tsakanin Jehboah da Ba’al za ta iya taimakonmu mu yi zaɓi da hikima wanda za mu bautawa.
Ta Yaya Ake “Ɗingishi?”
Daga tsololonsa, ana iya ganin dukan ƙasar Isra’ila, daga tafkin Kishon da ke ƙasa har zuwa Bahar Rum da ke kusa har zuwa duwatsun Lebanon da suke can arewaci.b Da rana ta fito a wannan ranar ƙarshe, ko ina ya kasance a bushe. Ƙasar da take ba da amfani da Jehobah ya bai wa ’ya’yan Ibrahim, yanzu ta zama matacciya. Yanzu ƙasa ce kawai da rana take ƙonawa, kuma mutanen Allah ne suka halaka ta saboda wautarsu! Sa’ad da mutanen suka taru, Iliya ya tunƙare su ya yi musu magana ya ce: “Har yaushe za ku yi ɗingishi a kan wannan imani da wancan? idan Ubangiji shi ne Allah, ku bi shi; amma idan Baal ne, sai ku bi shi.”—1 Sarakuna 18:21.
Menene Iliya yake nufi da wannan furcin “ɗingishi a kan wannan imani da wancan?” Waɗannan mutane ba su fahimci cewa dole ne su zaɓa tsakanin bautar Jehobah da ta Ba’al ba. Suna tsammanin za su iya haɗa bautan biyu, su faranta wa Ba’al rai da ayyukansu na tawaye kuma har ila su nemi tagomashin Jehobah Allah. Wataƙila sun yi tunanin cewa Ba’al zai albarkaci gonakinsu da tumakinsu, “Allah mai runduna” kuma zai kāre su a baƙin yaƙi. (1 Samaila 17:45) Sun mance da wata gaskiya, wadda mutane da yawa a yau ba su fahimta ba, cewa Jehobah baya raba bautarsa da kowa. Yana bukatar cikakkiyar bauta kuma ya cancanci haka. Ba ya karɓan dukan bauta da aka haɗa ta da wasu irin bauta, tana ma ɓata masa rai!—Fitowa 20:5.
Saboda da haka waɗannan Isra’ilawa suna “ɗingishi” ko kuma yawo da hankali kamar mutumin da yake ƙoƙari ya bi hanya biyu a lokaci guda. Mutane da yawa suna irin wannan kuskure a yau, suna ƙyale “ba’al” ɗinsu su shigo cikin rayuwarsu, su mamaye wurin bautar Allah! Kira da Iliya ya yi su daina yawo da hankalinsu zai iya taimakonmu mu sake bincika abubuwa masu muhimmanci a rayuwarmu da kuma bautarmu.
Gwaji na Ƙarshe
Sai Iliya ya ba da shawara a yi gwaji. Ba mai wuya ba ne. Firistocin Ba’al za su kafa bagadi su miƙa hadaya a kai; sai kuma su yi wa allahnsu addu’a ya ƙona hadayar. Iliya ma zai yi haka. Ya ce: “Allahn da ya amsa da wuta, shi za shi zama Allah.” Iliya ya san Allah na gaskiya. Bangaskiyarsa tana da ƙarfi ƙwarai ta sa bai yi jinkiri ba wajen ƙyale annabawan Ba’al su fara. Ya ƙyale magabatansa su zaɓi bijiminsu domin hadaya kuma su je ga Ba’al da farko.c—1 Sarakuna 18:24, 25.
Yanzu ba zamanin mu’ujiza ba ne. Duk da haka, Jehobah bai sake ba. Muna iya kasancewa da tabbaci a gare shi kamar yadda Iliya ya kasance. Alal misali, sa’ad da wasu suka ƙi yarda da abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa, kada mu ji tsoran ƙyale su su faɗi abin da suke so. Kamar Iliya, mu dogara ga Allah ya magance al’amura. Za mu yi haka ne ba ta wajen dogara ga kanmu ba, amma ta wajen dogara a kan Kalmarsa da ya hure, wanda aka tsara domin “kwaɓewa.”—2 Timothawus 3:16.
Sai annabawan Ba’al suka shirya hadayarsu suka kira allahnsu. “Ya Baal, ka ji mu,” suka yi ta roƙo. Suna ta kira lokaci kuma yana shigewa. “Amma babu murya, ba kuwa wanda ya amsa,” in ji Littafi Mai Tsarki. Da rana ta yi tsaka sai Iliya ya fara yi musu ba’a, yana cewa wataƙila Ba’al ya duƙufa ne cikin wani aiki shi ya sa bai amsa ba, wai wataƙila ya ratse ne, ko kuma yana barci ana bukatar wani ya tashe shi. “Ku yi ihu” Iliya ya gaya wa waɗannan annabawan ƙarya. A bayyane yake cewa ya fahimci bautar Ba’al rashin hankali ne, kuma yana son mutanen Allah su fahimci haka.—1 Sarakuna 18:26, 27.
Sai firistocin Ba’al suka amsa da hauka na ɗan lokaci, “Suka yi ihu, suka tsatsage jikinsu da wuƙaƙe da māsu, bisa ga adassu, har jini ya ɓulɓulo masu.” Amma duka a banza! “babu murya, ba kuwa wanda ya amsa, ko wanda ya kula.” (1 Sarakuna 18:28, 29) Hakika, babu Ba’al. Ƙage ne kawai na Shaiɗan domin ya rinjayi mutanen Allah daga Jehobah. Kamar yadda ya kasance a dā haka yake a yanzu, zaɓan wani ubangaji im ba Jehobah ba, zai kai ga baƙin ciki da kunya.—Zabura 25:3; 115:4-8.
An Amsa
Da yamma ta yi kusa, lokacin Iliya ya yi. Ya gyara bagadin Jehobah da abokan gaban bauta ta gaskiya suka rusa. Ya yi amfani da duwatsu 12, wataƙila ya tunasar da ƙabilu 10 na Isra’ila cewa Doka da aka bai wa ƙabilu 12 dole ne su bi ta. Sai ya ajiye hadayarsa ya sa aka jika wurin da ruwa, wataƙila wanda aka ɗiba daga Bahar Rum da ke kusa. Ya sa aka tona rami aka kewaye bagadin aka cika shi da ruwa. Kamar yadda ya sa abubuwa suka kasance da sauƙi ga annabawan Ba’al, ya sa abubuwa suka kasance da wuya ga Jehobah, domin tabbacinsa ga Allahnsa.—1 Sarakuna 18:30-35.
Sa’ad da aka gama shirya kome, Iliya ya yi addu’a. Mai sauƙi mai motsawa, addu’ar ta nuna abin da ya fi muhimmanci a rayuwar Iliya. Da farko, yana so a sani cewa Jehobah ne “Allah cikin Isra’ila,” ba Ba’al ba. Na biyu, yana so kowa ya sani cewa shi bawan Jehobah ne, saboda haka, dukan wani yabo da ɗaukaka ga Allah ne. A ƙarshe, ya nuna cewa har yanzu yana ƙaunar mutanensa, domin yana ɗokin ganin Jehobah ya “juyadda zukatansu.” (1 Sarakuna 18:36, 37) Duk da wahala da suka jawo wa kansu domin rashin amincinsu, har ila Iliya yana ƙaunarsu. Sa’ad da muke addu’a ga Allah, za mu iya nuna irin wannan damuwa domin sunan Allah, da kuma tawali’u da juyayin waɗanda suke bukatar taimako?
Kafin addu’ar Iliya, wataƙila wannan taron jama’a tana mamaki ko Jehobah zai kasance ƙarya ne kamar Ba’al. Amma bayan addu’ar, babu lokacin kakabi. Aka ce a labarin: “Da wannan, sai wutar Ubangiji ta fāɗo, ta cinye hadaya ta ƙonawa, da itacen, da duwatsu, da ƙura, ta shanye ruwan wuriya.” (1 Sarakuna 18:38) Wannan amsa ce ta musamman! Me mutanen suka yi?
Dukansu suka ce: ‘Jehobah, shi ne Allah; Jehobah shi ne Allah.” (1 Sarakuna 18:39) A ƙarshe sun fahimci gaskiya. Duk da haka, ba su nuna bangaskiya ba tukuna. A gaskiya, yarda cewa Jehobah shi ne Allah na gaskiya bayan an ga wuta ta faɗo daga sama domin amsa addu’a ba nuna bangaskiya ba ne mai burgewa. Saboda haka Iliya ya bukaci wani abu daga mutanen. Ya ce su yi wani abin da ya kamata da sun yi shekaru masu yawa da suka shige, su bi Dokar Jehobah. Dokar ta ce a kashe annabawan ƙarya da kuma masu bautar gumaka. (Kubawar Shari’a 13:5-9) Waɗannan firistocin Ba’al abokan gaban Jehobah Allah ne waɗanda da gangan suka yi hamayya da nufinsa. Sun cancani a ji ƙansu ne? To, an nuna jin ƙai ne ga yara marasa laifi da aka ƙona su da ransu domin hadaya ga Ba’al? (Misalai 21:13; Irmiya 19:5) Waɗannan mutane ba su cancanci a yi musu jin ƙai ba ko kaɗan. Saboda haka Iliya ya ba da umurni a kashe su, kuma aka kashe su.—1 Sarakuna 18:40.
Wasu masu sūka na zamani ba su yarda da ƙarshen wannan gwaji ba a Dutsen Karmel. Wasu sun damu cewa masu zafin ra’ayi na addini za su yi amfani da wannan su halalta ayyukan mugunta na addini. Kuma abin baƙin ciki, a yau da ayyukan mugunta masu yawa na addini. Duk da haka Iliya ba ruɗaɗɗe ba ne. Yana aiki ne a madadin Jehobah wajen kisa na halal. Bugu da ƙari, Kiristoci na gaskiya sun sani cewa ba za su iya bin tafarkin Iliya ba ta wajen ɗaukan takobi su yaƙi miyagu ba. Bayan da Almasihu ya zo, an sami mizani ga dukan almajiran Yesu cikin kalmomin Yesu ga Bitrus: “Mayar da takobinka gidansa: gama dukan waɗanda suka ɗauki takobi, da takobi za su lalace.” (Matta 26:52) Jehobah zai yi amfani da Ɗansa wajen zartar da hukuncin Allah a nan gaba.
Wajibin Kiristoci na gaskiya shi ne su yi rayuwa ta bangaskiya. (Yohanna 3:16) Hanya ɗaya da za su yi haka shi ne su yi koyi da mutane masu bangaskiya kamar su Iliya. Ya bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya kuma ya aririci mutane su yi haka. Ya fallasa aikin da Shaiɗan yake amfani da shi ya rinjayi mutane daga Jehobah. Kuma ya dogara ga Jehobah ya magance al’amura maimakon ya dogara ga kansa da kuma iyawansa. Hakika, Iliya ya kāre bauta ta gaskiya. Bari kowannen mu ya yi koyi da bangaskiyarsa!
[Hasiya]
a Don ƙarin bayani game da dagantakar Iliya da Ahab, ka dubi wannan talifi “Do You Have Faith Like Elijah’s?” a Hasumiya Tsaro ta 1 ga Afrilu, 1992 na Turanci.
b A koyaushe Karmel tana da dausayi, iska mai lema daga teku tana tasowa daga tundanta, tana zubo da ruwan sama da kuma raɓa. Domin an ce Ba’al ne yake kawo ruwan sama, wannan dutse babu shakka yana da muhimmanci wajen bautar Ba’al. Saboda haka, Karmel da ta bushe ta kasance wuri da ta dace domin fallasa yaudarar bautar Ba’al.
c Iliya ya gaya musu: “Kada ku sa wuta a ƙalƙashin” hadayar. Wasu masana sun ce irin waɗannan masu bautar gumaka suna amfani da bagadi da ke da rami a ƙarƙashi saboda da wuta ta fito ta bayyana kamar daga Allah ce.
[Bayanin da ke shafi na 20]
Zaɓan wani ubangaji ban da Jehobah zai kai ga ɓacin rai
[Hoto a shafi na 21]
‘Jehobah ne Allah na gaskiya!’