Ka Yi Koyi Da Imaninsu
Ya Sami Ƙarfafawa Daga Wajen Allahnsa
ILIYA yana gudu a cikin ruwan sama yayin da gari yake daɗa yin duhu. Yana da sauran tafiya sosai a gabansa kafin ya isa Jezreel, kuma shi ba matashi ba ne. Duk da haka, ya ci gaba da yin gudu ba tare da ya gaji ba, domin “hannun Ubangiji” yana tare da shi. Hannun Jehobah ya sa ya kasance da irin kuzarin da bai taɓa ji ba. Shi ya sa ya tsere wa karusan da ke ɗauke da Sarki Ahab!—1 Sarakuna 18:46.
Yanzu dai, ya riga ya tsere wa Sarki Ahab, kuma yana da doguwar tafiya a gabansa. Ka yi tunanin yadda ruwan da ake sheƙawa yake dukan fuskar Iliya yayin da yake tunani a kan rana mafi cike da hidima a rayuwarsa. Babu shakka, wannan nasara ce mai girma ga Jehobah, Allahn Iliya, da kuma bauta ta gaskiya. Ya riga ya bar Dutsen Karmel can baya inda Jehobah ya yi amfani da Iliya wajen fallasa bautar Baal a hanya mai girma kuma mai ban al’ajabi, kuma duhun hadari ya riga ya rufe dutsen. An fallasa ɗarurruwan annabawan Baal waɗanda miyagun ’yan zamba ne kuma an yi musu kisan da ya dace. Bayan haka, Iliya ya yi addu’a ga Jehobah don ya kawo ƙarshen fari da ya addabi ƙasar na shekara uku da rabi. Sai aka soma sheƙa ruwa!a—1 Sarakuna 18:18-45.
Yayin da Iliya yake sheƙa gudu a cikin ruwan sama zuwa Jezreel da ke da nisan kilomita 30, wataƙila yana tunanin cewa tun da yake an halaka annabawan Baal, za a sami canji mai kyau. Ahab yana bukatar ya tuba! Bayan abubuwan da ya shaida da idanunsa, dole ya daina bauta wa Baal, ya kwaɓi sarauniyarsa, Jezebel, kuma ya hana tsanantawar da ake yi wa bayin Jehobah.
Idan abubuwa suna tafiya yadda muke so, za mu so a ce abubuwa sun ci gaba hakan. Muna iya soma tunanin cewa yanayinmu a rayuwa zai ci gaba da inganta, kuma wataƙila ma mun kawar da matsalolinmu mafi wuya. Ba zai kasance abin mamaki ba idan Iliya ya yi irin wannan tunanin, domin shi “ɗan adam ne kamarmu.” (Yaƙub 5:17, Littafi Mai Tsarki) Gaskiyar ita ce, da sauran rina a kaba, matsalolin Iliya ba su ƙare ba. Hakika, nan da ’yan sa’o’i kaɗan, Iliya zai tsorata sosai, zai yi matuƙar baƙin ciki har ya gwammace ya mutu. Me ya faru? Kuma ta yaya Jehobah ya taimaka wa annabinsa ya sabonta bangaskiyarsa da kuma gaba gaɗinsa? Bari mu gani.
Canjin Yanayi na Ba Zato
Sa’ad da Ahab ya isa fadarsa a Jezreel, ya nuna cewa ya riga ya tuba ne, kuma ruhaniyarsa ta ƙaru? Mu karanta: “Ahab ya faɗa ma Jezebel dukan abin da Iliya ya aika, da yadda ya kashe dukan annabawa da takobi.” (1 Sarakuna 19:1) Ka ga cewa Ahab bai ambata Jehobah, Allahn Iliya ba, a labarin da ya ba da. Ahab wanda mutumi ne marar ruhaniya, ya ɗauki abubuwan al’ajabi da suka faru a matsayin ayyukan ɗan Adam, wato, “abin da Iliya ya aika.” A bayyane yake cewa ba ya daraja Jehobah Allah. Mene ne Jezebel wadda take son ɗaukar fansa ta yi?
Ta fusata! Cike da fushi, ta aika wannan saƙon ga Iliya: “Bari alloli su yi haka nan da ni, har su yi da ni fiye da hakama, idan ban maida ranka kamar ran ɗaya daga cikinsu ba kamin gobe warhaka.” (1 Sarakuna 19:2) Wannan muguwar barazana ce ga ransa. Wato, Jezebel ta ɗauki alkawari ne cewa ko ta mutu ko ta kashe Iliya a wannan ranar, domin ta rama abin ya yi wa annabawanta na Baal. Ka yi tunanin yadda aka ta da Iliya daga barci a wani madaidaicin masauki a Jezreel a wannan daren da ake ruwa da iska mai ƙarfi, kuma ɗan aiken sarauniyar ya gaya masa wannan saƙo marar daɗi. Ta yaya hakan ya shafe shi?
Ya Yi Baƙin Ciki da Sanyin Gwiwa
Idan a dā Iliya yana tunanin cewa yaƙi da bautar Baal ya riga ya ƙare, a yanzu ya ga cewa hakan ba gaskiya ba ne. Jezebel ba ta yi ƙasa a gwiwa ba. Ta riga ta sa an kashe da yawa daga cikin abokan aikin Iliya masu aminci, kuma a yanzu, shi take so a kashe. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Ya gani.” New World Translation ya fassara wannan ayar kamar haka: “Ya tsorata.” Iliya ya gani, ko kuma ya yi tunanin irin mugun kisan da Jezebel take shirin yi masa. Idan ya yi ta tunani a kan hakan, to ba abin mamaki ba ne cewa ya yi ƙasa a gwiwa. Ko da mene ne, Iliya ya “gudu domin shi tsira da kansa.”—1 Sarakuna 18:4; 19:3.
Ba Iliya kawai ba ne mutumi mai bangaskiya da ya taɓa tsorata ba. Shekaru da yawa bayan wannan aukuwar, manzo Bitrus ya fuskanci irin wannan matsalar. Alal misali, sa’ad da Yesu ya gaya wa Bitrus ya yi tafiya tare da Shi a kan ruwa, manzon ya soma kallon “iska.” Ya ji tsoro kuma ya soma nitsewa. (Matta 14:30) Misalan Bitrus da Iliya sun koya mana darassi mai amfani sosai. Idan muna son mu riƙe gaba gaɗinmu, kada mu yi tunanin haɗarurrukan da suke tsoratar da mu. Muna bukatar mu mai da hankalinmu a kan Tushen begenmu da ƙarfinmu.
“Ya Isa”
Saboda ya tsorota, Iliya ya tsere zuwa kudu maso yamma, tafiyar kilomita 150 zuwa Beer-sheba wani gari da ke kusa da kudancin iyakar Yahuda. A nan ne ya bar mai yi masa hidima kuma shiga daji shi kaɗai. Labarin ya ce ya yi “tafiyar yini,” saboda haka, za mu iya yin tunanin cewa ya fara tafiyar ce tun daga fitowar rana, ba tare da abinci ko wasu tanadodi masu muhimmanci ba. Cike da baƙin ciki da tsoro, ya ci gaba da tafiya cikin rana mai zafi a kan wannan hanyar da ke cike da haɗari a cikin daji. Iliya ya gaji da tafiyar yayin da rana ta soma faɗuwa kuma dare yana yi. Saboda ya gaji matuƙa, ya zauna a ƙarƙashin wani itace, inda kawai zai iya hutawa a wannan hamadar marar itatuwa.—1 Sarakuna 19:4.
Cikin matuƙar karaya, Iliya ya yi addu’a. Ya nemi ya mutu. Ya ce: “Ban fi ubannina kyau ba.” Ya san cewa kakanninsa sun riga sun zama turɓaya da ƙasusuwa a cikin kabari, ba za su iya yi wa kowa kome ba. (Mai-Wa’azi 9:10) Shi ma Iliya ya yi tunanin cewa ba zai iya yin kome ba. Shi ya sa ya ce da babbar murya: “Ya isa!” Mene ne amfanin ci gaba da rayuwa?
Abin mamaki ne cewa mutumin Allah zai iya yin baƙin ciki kamar haka? Ba lallai ba ne. Akwai maza da mata masu aminci da dama a cikin Littafi Mai Tsarki da aka nuna cewa sun yi baƙin ciki sosai har suka gwammace su mutu, wasu daga cikinsu su ne Rifkatu da Yakubu da Musa da kuma Ayuba.—Farawa 25:22; 37:35; Littafin Lissafi 11:13-15; Ayuba 14:13.
A yau, muna zama ne cikin “miyagun zamanu,” saboda haka ba abin mamaki ba ne cewa mutane da yawa, har da bayin Allah masu aminci, sukan yi baƙin ciki a wasu lokatai. (2 Timotawus 3:1) Idan ka samu kanka cikin irin wannan yanayi mai wuya, ka bi misalin Iliya a wannan fanni: Ka gaya wa Allah gabaƙi ɗaya yadda kake ji. Domin Jehobah ne “Allah na dukan ta’aziyya.” (2 Korintiyawa 1:3) Ya ƙarfafa Iliya kuwa?
Jehobah Ya Tallafa wa Annabinsa
Yaya kake ganin Jehobah ya ji sa’ad da ya kalli ƙasa daga sama kuma ya gan ƙaunataccen annabinsa yana kwance a ƙarƙashin itacen nan cikin jeji yana roƙon ya mutu? Ba sai mun yi dogon tunani ba. Bayan barci ya ɗauke Iliya, Jehobah ya aika mala’ika zuwa wurinsa. Mala’ikan ya ɗan taɓa Iliya, ya ta da shi daga barci kuma ya ce: “Tashi, ka ci” abinci. Iliya ya yi hakan, domin mala’ikan ya riga ya shirya masa kalacin burodi mai ɗumi da kuma ruwa. Ya ma gode wa mala’ikan kuwa? Labarin dai ya ce annabin ya ci kuma ya sha bayan haka ya koma barci. Baƙin ciki ne da karaya suka hana shi yin magana? Ko ma mene ne, mala’ika ya sake ta da shi, wataƙila da wayewar gari. Ya sake gaya wa Iliya, “Tashi, ka ci” abinci, kuma ya daɗa waɗannan muhimman kalmomi, “gama tafiya ta fi ƙarfinka.”—1 Sarakuna 19:5-7.
Domin basirar da Allah ya ba mala’ikan, ya san inda Iliya ya dosa. Ya kuma san cewa tafiyar mai nisa ce, kuma Iliya ba zai iya yin ta da ƙarfinsa kaɗai ba. Abin ban ƙarfafa ne mu bauta wa Allahn da ya san muradinmu da kuma kasawarmu fiye da mu! (Zabura 103:13, 14) Ta yaya Iliya ya amfana daga wannan kalacin?
Mu karanta: “Ya tashi, ya ci, ya sha; a cikin ƙarfin wannan abinci fa ya kama tafiya yini arba’in da dare arba’in har ya zo Horeb dutsen Allah.” (1 Sarakuna 19:8) Kamar Musa da ya yi rayuwa ƙarnuka shida kafin Iliya, da kuma Yesu da ya rayu ƙarnuka kusan goma a bayan Iliya, Iliya ya yi azumi na kwanaki 40 dare da rana. (Fitowa 34:28; Luka 4:1, 2) Wannan kalacin guda bai warware dukan matsalolinsa ba, amma ya taimaka masa ta hanyar mu’ujiza. Ka yi tunanin wannan dattijon yana takawa cikin ƙungurmin daji marar turba dare da rana har tsawon kwanaki 40!
Hakazalika, Jehobah yana kula da bayinsa a yau, ba ta abincin da aka tanadar ta hanyar mu’ujiza ba, amma a wata hanya mafi muhimmanci sosai. Yana yi wa bayinsa tanadi na ruhaniya. (Matta 4:4) Koyo game da Allah daga Kalmarsa da littattafan da suke bayyana Littafi Mai Tsarki yana ƙarfafa ruhaniyarmu. Mai yiwuwa, cin abinci na ruhaniya ba zai warware dukan matsalolinmu ba, amma zai iya taimaka mana mu jimre abubuwan da ba za mu iya jimrewa da ƙarfinmu ba. Yana kuma kai ga samun “rai na har abada.”—Yohanna 17:3.
Iliya ya yi tafiyar kusan kilomita 320 kafin ya isa Dutsen Horeb, inda Jehobah Allah ta hanyar mala’ikansa ya taɓa bayyana ga Musa a cikin kurmi da ke cin wuta kuma daga baya Jehobah ya ba Isra’ila Dokar alkawari. Iliya ya samu mafaka a cikin wani kogo.
Yadda Jehobah Ya Ƙarfafa Annabinsa
A Horeb, ta bakin mala’ika, Jehobah ya tambayi Iliya: “Me ka ke yi a nan, ya Iliya?” Mai yiwuwa, an yi wannan tambayar ce da murya mai daɗi, domin Iliya ya ɗauki hakan ne a matsayin zarafin bayyana yadda yake ji. Hakika, abin da ya yi ke nan! Ya ce: “Na yi kishi ƙwarai domin Ubangiji, Allah mai-runduna; gama ’ya’yan Isra’ila sun ƙi alkawarinka, sun kaɓantar da bagadanka, sun kashe annabawanka da takobi: ni ma, ga ni kaɗai na rage; suna kuwa neman raina su ɗauka.” (1 Sarakuna 19:9, 10) Kalmomin Iliya sun bayyana aƙalla dalilai guda uku da suka sa shi baƙin ciki.
Na farko, Iliya yana ganin cewa ya yi aikin banza. Duk da shekarun da ya yi yana “kishi ƙwarai” a bautar Jehobah da kuma ɗaukaka sunan Allah da bautarsa fiye da kome, Iliya ya ga kamar yanayin ya daɗa muni. Har ila, mutanen suna nuna rashin bangaskiya da tawaye, yayin da bautar ƙarya take haɓaka. Na biyu, Iliya yana ganin cewa shi kaɗai ne ya rage. “Ni ma, ga ni kaɗai na rage,” in ji shi, kamar shi kaɗai ne ya rage cikin waɗanda ke bauta wa Jehobah a cikin al’ummar. Na uku, Iliya ya tsorata. An riga an kashe ’yan’uwansa annabawa da yawa, kuma ya tabbata cewa shi ake neman a kashe. Mai yiwuwa, furta yadda yake ji bai zo wa Iliya da sauƙi ba, amma bai ƙyale girman kai ko kunya ta hana shi yin hakan ba. Ta wurin bayyana wa Allahnsa yadda yake ji a cikin addu’a, Iliya ya kafa misali mai kyau ga dukan mutane masu aminci.—Zabura 62:8.
Ta yaya Jehobah ya warware damuwa da kuma tsoron da Iliya yake da shi? Mala’ikan ya gaya wa Iliya ya tsaya a mashigin kogon. Ya yi biyayya, ba tare da sanin ko mene ne zai faru ba. Farat ɗaya, sai iska mai ƙarfi ta taso! Babu shakka, iskar ta zo da ruri mai tsanani, domin sai da ƙarfinta ya tsatsage duwatsu. Ka yi tunanin yadda Iliya yake ƙoƙarin kāre idanunsa yayin da yake riƙe gam da tufafinsa madaidaici na gashi da iskar take kaɗawa. Bayan hakan, ya soma ƙoƙarin riƙe kansa don kada ya faɗi, domin ƙasa ta soma motsi, wato, an yi girgizar ƙasa da ta jijjiga wannan yankin! Farfaɗowarsa ke da wuya sai ga wuta ta taso, hakan ya tilasta masa ya koma cikin kogon domin ya kāre kansa daga zafin wutar.—1 Sarakuna 19:11, 12.
A kowace aukuwa, labarin ya tuna mana cewa Jehobah ba ya cikin waɗannan hanyoyi masu ban mamaki na bayyana ikon halitta. Iliya ya san cewa Jehobah ba wani allan halitta marar wanzuwa ba ne kamar Baal, wanda masu bauta masa da aka ruɗa suke yabonsa a matsayin “Mahayin Gajimare,” ko wanda yake tanadar da ruwan sama. Jehobah ne ainihin Tushen dukan iko mai ban mamaki da ake gani a halitta, kuma ya fi ƙarfin duk wani abin da ya halitta. Ko sammai na zahiri ba za su iya ɗaukansa ba! (1 Sarakuna 8:27) Amma, ta yaya ne dukan waɗannan abubuwan suka taimaka wa Iliya? Ka tuna da tsoron da yake ji. Tun da Allah mai iko marar iyaka kamar Jehobah yana tare da shi, Iliya ba ya bukatar jin tsoron Ahab da Jezebel!—Zabura 118:6.
Bayan wutar ta wuce, sai ko’ina ya yi tsit kuma Iliya ya ji “ƙaramar murya mara-ƙarfi.” Muryar ta ba Iliya damar sake bayyana yadda yake ji, kuma ya yi hakan, ya sake bayyana dukan abubuwan da ke damunsa.b Wataƙila, hakan ya ƙara kwantar masa da hankali. Babu shakka, Iliya ya samu ƙarin ƙarfafa daga abin da wannan “ƙaramar murya mara-ƙarfi” ta gaya masa. Jehobah ya tabbatar da Iliya cewa yana da daraja sosai. Ta yaya? Allah ya bayyana nufinsa na nan gaba game da yaƙin da zai yi da bautar Baal a Isra’ila. Hakika, Iliya bai yi aikin banza ba, domin nufin Allah yana ci gaba babu tangarɗa. Bugu da ƙari, Iliya yana da matsayin da zai ɗauka a cikar wannan nufin, domin Jehobah ya sake tura shi zuwa bakin aiki kuma ya ba shi takamaiman umurni.—1 Sarakuna 19:12-17.
Kaɗaicin da Iliya yake ji fa? Jehobah ya yi abubuwa guda biyu game da hakan. Na farko, ya gaya wa Iliya ya naɗa Elisha a matsayin annabin da zai gaje shi da shigewar lokaci. Wannan matashin zai yi shekaru da dama a matsayin abokin tafiyar Iliya da kuma mataimakinsa. Hakika, wannan ƙarfafawa ce mai amfani! Na biyu, Jehobah ya bayyana wannan saƙo mai daɗin ji: “[Na] rage mutum saba’a a cikin Isra’ila, dukan guwawun da ba su durƙusa ga Baal ba, kowane baki wanda ba ya yi masa sumba ba.” (1 Sarakuna 19:18) Ba Iliya ne kaɗai ya rage ba. Babu shakka, zai yi murnar jin cewa akwai mutane dubbai masu aminci da suka ƙi bauta wa Baal. Suna bukatar Iliya ya ci gaba da hidimarsa na aminci, don ya kafa musu misalin aminci mai ƙarfi da yake da shi ga Jehobah a wannan lokacin da kusan kowa ya juya bayansa ga Jehobah. Kalmomin “ƙaramar murya mara-ƙarfi” da Iliya ya ji ta bakin wanda Jehobah ya aika sun ratsa zuciyarsa sosai. Ga Iliya, kamar Allah ne da kansa ya yi masa magana.
Kamar Iliya, abubuwa masu ban al’ajabi da muke gani a halitta za su iya sa mu cika da mamaki, kuma hakan ya dace. Halitta tana bayyana ikon Mahalicci. (Romawa 1:20) Har yanzu, Jehobah yana yin amfani da ikonsa marar iyaka don ya taimaka wa bayinsa. (2 Labarbaru 16:9) Amma, Allah ya fi yi mana magana ne ta hanyar Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. (Ishaya 30:21) A wani ɓangare, Littafi Mai Tsarki yana kama ne da wannan “ƙaramar murya mara-ƙarfi,” wadda a yau, ta nan ne Jehobah yake yi mana ja-gora, ƙarfafawa, da kuma tabbatar mana da ƙaunarsa.
Iliya ya karɓi ƙarfafawar da Jehobah ya ba shi a Dutsen Horeb kuwa? Babu shakka! Ba da daɗewa ba, wannan amintaccen annabi mai gaba gaɗi ya tasar wa bautar ƙarya da ke cike da mugunta. Idan muka saka hurarrun kalmomin Allah a zuciya, wato, “ta’aziyyar da Littattafai ke yi mana,” za mu iya yin koyi da bangaskiyar Iliya.—Romawa 15:4, LMT.
[Hasiya]
a Ka duba waɗannan talifofi “Ya Kāre Bauta ta Gaskiya” da “Ya Gani, Kuma Ya Jira” da suka fito a ƙarƙashin jigon nan “Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu” a Hasumiyar Tsaro na Janairu-Maris da kuma Afrilu-Yuni 2008.
b Mai yiwuwa tushen wannan “ƙaramar murya mara-ƙarfi” shi ne ruhun da aka yi amfani da shi wajen idar da “maganar Ubangiji” a 1 Sarakuna 19:9. A aya ta 15, an kira wannan ruhun “Ubangiji.” Wannan zai iya tuna mana da mala’ikan da Jehobah ya yi amfani da shi wajen yi wa Isra’ila ja-gora a cikin jeji kuma wanda Allah ya ce game da shi: “Sunana yana cikinsa.” (Fitowa 23:21) Hakika, ba za mu iya nacewa a wannan batun ba, amma yana da kyau mu lura cewa kafin ya zo duniya, Yesu ya yi hidima a matsayin “Kalma,” wato, Kakaki na musamman ga bayin Jehobah.—Yohanna 1:1.
[Hoto a shafi na 19]
Jehobah ya albarkaci Iliya a hanya mai girma, a lokaci mai daɗi da marar daɗi
[Hoto a shafi na 20]
Sa’ad da yake matuƙar baƙin ciki, Iliya ya bayyana yadda yake ji ga Jehobah
[Hoto a shafi na 21]
Jehobah ya yi amfani da ikonsa mai girma don ya ƙarfafa Iliya