Ka Kusaci Allah
Ya Tuna Cewa “Mu Turɓaya Ne”
“BAN taɓa tunanin cewa Jehobah zai iya gafarta mini dukan zunubai na ba, na ɗauka cewa zan ci gaba da ɗaukan wannan nauyin a dukan rayuwata.” Abin da wata Kirista ta rubuta ke nan game da kurakurenta na dā. Hakika, lamirin da ke damun mutum kaya ne mai nauyi. Amma Littafi Mai Tsarki ya ba da ƙarfafawar da za ta iya sauƙaƙa baƙin cikin masu zunubi da suka tuba. Ka yi la’akari da waɗannan kalmomi na mai zabura Dauda da ke Zabura 103:8-14.
Dauda ya san cewa “Ubangiji cike da tausayi ya ke” kuma ba ya ‘tsauta mana kullum.’ (Ayoyi 8-10) Idan Allah ga dalilin nuna jin ƙai, yana gafartawa gabaki ɗaya kuma a yalwace. Dauda, wanda ƙwararren mawaƙi ne ya yi amfani da kwatance guda uku domin ya kwatanta yawan jin ƙai da Allah yake nuna mana.
“Kamar yadda sama ta yi nisa birbishin duniya, haka nan kuma jinƙansa yana da girma zuwa ga masu-tsoronsa.” (Aya ta 11) Idan muka kalli sama da dare, ba za mu iya fahimtar nisan da ke tsakanin taurari da duniya ba. Ta hakan ne Dauda ya koya mana yawan jin ƙan Jehobah, wanda fanni ne na ƙaunarsa ta aminci. “Masu-tsoron” Allah ne kaɗai za su iya samun wannan jin ƙan, wato, waɗanda suke “matuƙar girmama ikonsa,” in ji wani masani.
“Kamar nisan gabas da yamma, hakanan ya kawar da saɓe saɓenmu, ya nisantadda su.” (Aya ta 12) Yaya nisan yake? Iyakar tunaninmu. Wani littafin bincike na Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka yi tunanin cewa kana tafiya cikin sarari daga gabas zuwa yamma, yayin da kake ƙara tafiya, haka rata za ta ci gaba da ƙaruwa tsakanin ka da gabas.” A nan, Dauda yana gaya mana ne cewa idan Allah ya gafarta mana zunubanmu, yana jefar da su nesa da mu fiye da yadda muke zato.
“Kamar yadda uba ya kan yi juyayin ’ya’yansa, hakanan Ubangiji yana juyayin masu-tsoronsa.” (Aya ta 13) Dauda, wanda mahaifi ne ya san yadda mahaifi mai ƙauna yake ji a zuciyarsa. Irin wannan mahaifin yana nuna tausayi ga ’ya’yansa, musamman sa’ad da ba sa jin daɗi. Dauda ya tabbatar da mu cewa Babanmu mai ƙauna da ke sama yana nuna jin ƙai ga yaransa na duniya, musamman sa’ad da suka tuba kuma suka kasance da ‘karyayyun’ zukata saboda zunubansu.—Zabura 51:17.
Bayan waɗannan kwatance guda uku, Dauda ya bayyana abin da yake motsa Jehobah ya nuna jin ƙai ga ’yan Adam ajizai: “Gama ya san tabi’ammu; Ya kan tuna mu turɓaya ne.” (Aya ta 14) Jehobah ya san cewa ya halicce mu ne da turɓaya, kuma muna da kumamanci da kasawa. Domin ya san cewa mu ajizai ne, Jehobah yana “hanzarin gafartawa,” idan muka tuba da gaske.—Zabura 86:5.
Kalmomin da Dauda ya faɗa game da jin ƙan Jehobah sun ratsa zuciyarka kuwa? Matar da aka yi ƙaulinta a farkon wannan talifin ta yi nazarin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da gafartawar da Allah yake nunawa, hakan ya sa ta ce: “Na fara jin cewa zan iya ƙara kusantar Jehobah, kuma na ji kamar an sauke mini wani nauyi daga kaina.”a Me zai hana ka koya game da jin ƙan Allah da kuma yadda za ka same shi? Wataƙila kai ma za ka ji kamar an sauke maka nauyi.
[Hasiya]
a Ka duba babi na 26, “Allah Wanda Yake da ‘Hanzarin Gafartawa,’” a littafin nan Ka Kusaci Jehovah, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
[Bayanin da ke shafi na 23]
“Na fara jin cewa zan iya ƙara kusantar Jehobah, kuma na ji kamar an sauke mini wani nauyi daga kaina”