Kana Bukatar Ka Ƙara Ƙwazo a Ƙungiyar Jehobah?
“Ka mai da hankali ga karatu, da gargaɗi, da koyarwa.”—1 TIM. 4:13.
WAƘOƘI: 45, 70
1, 2. (a) Ta yaya Ishaya 60:22 take cika a wannan kwanaki na ƙarshe? (b) Mene ne ake bukata a ƙungiyar Jehobah a yau?
“ƘARAMIN za ya zama dubu, ƙanƙanin kuma za ya zama al’umma mai-ƙarfi.” (Isha. 60:22) Waɗannan kalmomin suna cika a waɗannan kwanaki na ƙarshe. Domin a shekarar hidima ta 2015, adadin masu shelar Mulki guda 8,220,105 ne suka yi wa’azi a faɗin duniya! Ya kamata dukan Kiristoci su yi tunani sosai a kan sashe na ƙarshe na wannan annabcin, don Ubanmu da ke sama ya ce: “Ni, Ubangiji, zan hanzarta wannan a lotonsa.” Kamar yadda fasinjoji da ke cikin mota sun san lokacin da direban ya ƙara wuta, mu ma mun san cewa muna bukatar mu ƙara ƙwazo a hidimarmu. Ta yaya muke ɗaukan batun ƙara ƙwazo a hidimarmu? Shin muna yin iya ƙoƙarinmu don mu yishelar Mulki da ƙwazo? ’Yan’uwa da yawa suna yin hidimar majagaba na kullum ko na ɗan lokaci. Ƙari ga haka, muna farin ciki sosai da yadda ’yan’uwa da yawa suke zuwa hidima a inda ake bukatar masu shela ko kuma yin wasu hidimomi a ƙungiyar Jehobah.
2 Ban da haka, mun ga cewa ana bukatar ’yan’uwa sosai da za su taimaka a ikilisiyoyi da dama, don a kowace shekara ana ƙafa ikilisiyoyi guda 2,000. Idan ana bukatar dattawa 5 a cikin kowacce sabuwar ikilisiya, hakan yana nufin cewa a kowace shekara, ana bukatar bayi masu hidima guda 10,000 da za su zama dattawa. Hakan ya nuna cewa ana bukatar ’yan’uwa maza dubbai su cancanci zama bayi masu hidima. Ƙari ga haka, dukanmu muna bukatar mu “yawaita cikin aikin Ubangiji.”—1 Kor. 15:58.
ABIN DA ZA KA YI DON KA SAMU CI GABA
3, 4. Mene ne samun ci gaba a hidimarka ga Jehobah yake nufi a gare ka?
3 Karanta 1 Timotawus 3:1. Aikatau na Helenanci da aka fassara “biɗan aiki” yana nufin mutum ya miƙa hannunsa don ya ɗauki wani abin da hannunsa bai kai ba. Bulus ya yi amfani da wannan Kalmar don ya nuna cewa mutum yana bukatar ya ƙoƙarta sosai don ya samu ci gaba a hidimarsa ga Jehobah. A ce wani ɗan’uwa yana so ya zama bawa mai hidima. Amma ya san cewa yana bukatar ya ƙoƙarta sosai don ya kyautata halayensa. Ƙari ga haka, idan ya zama bawa mai hidima, zai ci gaba da yin aiki tuƙuru don ya zama dattijo.
4 Hakazalika, ’yan’uwa maza da mata da suke so su soma hidimar majagaba ko hidima a Bethel ko kuma gina Majami’ar Mulki suna bukatar su ƙoƙarta sosai don su cim ma burinsu. Bari mu tattauna yadda Kalmar Allah take ƙarfafa dukanmu mu samu ci gaba a bautarmu ga Jehobah.
KA CI GABA DA ƘOƘARTAWA DON KA SAMU CI GABA
5. Ta yaya matasa za su iya yin amfani da ƙarfinsu a hidimarsu ga Jehobah?
5 Matasa suna aiki tuƙuru a hidimarsu ga Jehobah don suna da ƙarfi da kuma koshin lafiya. (Karanta Misalai 20:29.) Wasu matasa da suke hidima a Bethel suna aiki a inda ake buga littattafanmu da kuma Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, matasa maza da mata da yawa suna aikin gina da kuma adana Majami’un Mulki. Sa’ad da bala’o’i suka faru, matasa suna aiki tare da ’yan’uwan da suka manyanta don ba da kayan agaji. Kuma matasa da yawa da suke hidimar majagaba suna wa’azi a yankuna da ake harsuna dabam-dabam.
6-8. (a) Ta yaya wani matashi ya canja ra’ayinsa game da hidimar Allah, kuma mene ne sakamakon yin hakan? (b) Ta yaya za mu ɗanɗana kuma mu ga cewa “Ubangiji nagari ne”?
6 Hakika, mun san muhimmancin bauta wa Allah da dukan zuciyarmu. Amma, idan kana jin yadda wani ɗan’uwa mai suna Aaron ya ji a dā kuma fa? Duk da cewa ya girma a iyalin da suke bauta wa Jehobah, ya ce: “Ba na jin daɗin taro da kuma zuwa wa’azi.” Yana so ya yi farin ciki yayin da yake bauta wa Allah amma bai san abin da ya sa ba ya yin hakan ba. Wane mataki ne ya ɗauka?
7 Aaron ya yi ƙoƙari ya riƙa karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai, da shirya taro da kuma yin kalami. Kuma ya soma yin addu’a a kai a kai. Ya samu ci gaba sosai yayin da ya soma ƙaunar Jehobah da dukan zuciyarsa. Tun daga lokacin, Aaron ya yi hidimar majagaba kuma ya yi aiki da wasu ’yan’uwa a wurin ba da kayan agaji kuma ya yi wa’azi a wata ƙasa. Yanzu, Aaron yana hidima a Bethel kuma shi dattijo ne. Yaya yake ji game da tafarkin da ya zaɓa? “Na ‘ɗanɗana na ga cewa Ubangiji nagari ne.’ Domin yadda Jehobah ya albarkace ni, ya kamata in nuna masa godiyata. Shi ya sa na ƙara ƙwazo a hidimata kuma hakan ya sa na sami albarka sosai.”
8 Marubucin wannan zaburar ya ce: “Waɗanda suke biɗan Ubangiji ba za su rasa kowane abu mai-kyau ba.” (Karanta Zabura 34:8-10.) Hakika, Jehobah ba zai taɓa barin waɗanda suke bauta masa da dukan zuciyarsu su rasa abin da suke bukata ba. Idan muna iya ƙoƙarinmu a hidimar Allah, muna ɗanɗana kuma muna ganin cewa “Ubangiji nagari ne.” Ƙari ga haka, idan muka bauta wa Allah da dukan zuciyarmu, za mu yi farin ciki sosai.
KADA KA YI SANYIN GWIWA
9, 10. Me ya sa yake da muhimmanci mu “jira” lokacin Allah?
9 Wataƙila muna so mu ƙara ƙwazo a bautarmu ga Jehobah, amma idan ba a ba mu wani gata a cikin ikilisiya kuma ba fa? Muna bukatar mu yi haƙuri kuma mu “jira” lokacin Jehobah. (Mi. 7:7) Ko da yake Jehobah yana iya ƙyale mu mu kasance a cikin wani yanayi, muna da tabbaci cewa zai riƙa tallafa mana a kowane lokaci. Alal misali, Jehobah ya yi wa Ibrahim alkawari cewa zai haifi ɗa, amma Ibrahim yana bukatar ya kasance da bangaskiya kuma ya jira lokacin da Jehobah zai cika wannan alkawarin. (Ibran. 6:12-15) Duk da cewa ya jira shekaru da yawa kafin a haifi Ishaku, Ibrahim bai karaya ba, kuma daga baya Jehobah ya cika alkawarinsa.—Far. 15:3, 4; 21:5.
10 Ba shi da sauƙi mutum ya ci gaba da jiran wani abu. (Mis. 13:12) Amma za mu iya yin sanyin gwiwa idan muka ci gaba da tunani game da yanayinmu. Ya kamata mu yi amfani da lokacinmu don mu kyautata halayen da muke bukata mu kasance da shi don kula da wasu ayyuka a cikin ikilisiya. Bari mu tattauna hanyoyi uku da za mu yi hakan.
11. Waɗanne halaye ne ya kamata mu yi ƙoƙari mu kasance da su, kuma me ya sa suke da muhimmanci?
11 Ka kasance da halaye masu kyau. Za mu iya zama masu hikima da basira da sanin yakamata da ilimi da hankali da kuma fahimi idan muna karanta Kalmar Allah kuma muna yin bimbini a kanta. Masu ja-gora a cikin ikilisiya suna bukatar su kasance da irin waɗannan halayen. (Mis. 1:1-4; Tit. 1:7-9) Ƙari ga haka, za mu san ra’ayin Allah a kan batutuwa da yawa yayin da muke karanta littattafanmu da ke bayyana Littafi Mai Tsarki. Kullum muna fuskantar batutuwa da suka shafi nishaɗi da saka tufafi da yin ado da yadda za mu riƙa kashe kuɗi da kuma sha’ani da mutane. Za mu iya yin abin da zai faranta wa Jehobah rai idan muka bi shawarar da ke cikin Littafi Mai Tsarki.
12. Ta yaya waɗanda suke cikin ikilisiya za su nuna cewa su tabbatattu ne?
12 Ka zama wanda za a riƙa tabbatawa da shi. Muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu don mu kula da ayyukan da aka ce mu yi a ƙungiyar Jehobah ko da mu maza ne ko mata. A matsayinsa na gwamna, Nehemiya yana bukatar maza da za su kula da ayyuka dabam-dabam. Waɗanne irin mutane ne ya naɗa? Ya naɗa masu tsoron Allah da waɗanda za su yi duk wani aikin da aka ba su. (Neh. 7:2; 13:12, 13) Hakazalika, a yau ‘abin da ake nema ga wakilai, shi ne a iske mutum da aminci.’ (1 Kor. 4:2) Mutane sukan lura da ayyuka masu kyau da muke yi.—Karanta 1 Timotawus 5:25.
13. Ta yaya za ka bi misalin Yusufu sa’ad da mutane suka yi maka rashin adalci?
13 Ka dogara ga Jehobah. Mene ne za ka iya yi idan wasu suka yi maka rashin adalci? Kana iya bayyana musu yadda kake ji. Amma, a wasu lokatai kāre kanka yana iya sa yanayin ya daɗa muni. Alal misali, ’yan’uwan Yusufu sun wulakanta shi, amma hakan bai sa ya riƙe su a zuciya ba. Bayan haka, an yi masa zargin ƙarya kuma aka saka shi a kurkuku ba tare da yin laifi ba. Duk da haka, ya bar Jehobah ya yi masa ja-gora a mawuyacin lokaci. Mene ne sakamakon haka? “Maganar Ubangiji ta [“horar da shi,” NW].” (Zab. 105:19) Abin da Yusufu ya fuskanta ya taimaka masa ya cancanci yin wani aiki na musamman. (Far. 41:37-44; 45:4-8) Idan mutane suka yi maka rashin adalci, ka yi addu’a ga Jehobah ya sa ka kasance da hikima. Zai taimaka maka ka natsu kuma ka bi da su a hankali sa’ad da kake magana da su.—Karanta 1 Bitrus 5:10.
KA CI GABA DA ƘWAZO A YIN WA’AZI
14, 15. (a) Me ya sa muke bukatar mu “mai da hankali” ga yadda muke wa’azi? (b) Ta yaya za ka iya bi da canjin yanayi? (Ka duba hoton da ke shafi na 20 da kuma akwatin nan “Kana Shirye Ka Gwada Wata Hanyar Yin Wa’azi?”)
14 Bulus ya gaya wa Timotawus: “Ka mai da hankali ga karatu, da gargaɗi, da koyarwa, . . . ka mai da hankali da kanka, da kuma koyarwarka.” (1 Tim. 4:13, 16) Timotawus ya ƙware sosai a yin shelar Mulkin Allah. Duk da haka, zai fi taimaka wa mutane a hidimarsa idan ya “mai da hankali” ga koyarwarsa. Ya san cewa mutane za su saurare shi, amma yana bukatar ya ci gaba da kyautata hidimarsa da kuma inganta koyarwarsa don ya iya motsa zuciyarsu. Ya kamata mu bi misalinsa a matsayinmu na masu shelar Mulkin Allah.
15 A yawancin lokaci, ba ma samun mutane a gida sa’ad da muke wa’azi gida-gida. A wasu wurare kuma, ba za mu iya shiga wasu gidajen bene ko kuma gidajen da aka saka musu ƙofa ba. Idan haka yankinku yake, za ka iya neman wata hanya dabam da za ka yi wa mutane wa’azi.
16. Ta yaya yin wa’azi a inda jama’a suke yake kawo sakamako mai kyau?
16 Wata hanya mai kyau sosai ta yaɗa bishara ita ce yin wa’azi a inda jama’a suke. ’Yan’uwanmu da yawa suna jin daɗin yin irin wannan wa’azin. Sukan je su yi wa mutane wa’azi a tashar jirgin ƙasa ko kasuwa da tashoshin motoci da kuma wasu wuraren da za a samu jama’a. Alal misali, wani Mashaidi yana iya amfani da abin da aka faɗa a labarai don ya soma tattaunawa da wani ko ya yaba wa yaran mutumin ko kuma ya yi masa tambaya game da aikinsa. Yayin da suke tattaunawa, sai mai shelar ya kawo wani batu da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma ya tambaye shi mene ne ra’ayinsa game da batun. Sau da yawa, amsar da mutumin ya ba da yakan sa a ci gaba da tattaunawa da shi.
17, 18. (a) Ta yaya za ka kasance da gaba gaɗi sa’ad da kake wa’azi a inda jama’a suke? (b) Me ya sa bin misalin Dauda yake da muhimmanci sa’ad da kake wa’azi?
17 Kada ka karaya idan yin wa’azi a inda jama’a suke yana yin maka wuya. Alal misali, wani majagaba mai suna Eddie da yake ƙasar Amirka ba ya iya wa’azi a inda jama’a suke. Amma da shigewar lokaci, ya yi hakan. Mene ne ya taimaka masa? Ya ce: “A lokacin da muke ibada ta iyali, ni da matata mun yin bincike sosai don mu sami amsoshi ga tambayoyi da kuma ra’ayin da mutane suke da shi. Ƙari ga haka, muna neman taimako daga wasu ’yan’uwa.” Yanzu Eddie yana jin daɗin yin wa’azi a inda jama’a suke.
18 Yayin da muke jin daɗin wa’azi da kuma kyautata yadda muke wa’azi, mutane za su ga cewa muna samun ci gaba a ibadarmu ga Jehobah. (Karanta 1 Timotawus 4:15.) Ban da haka, muna ɗaukaka Jehobah kamar yadda Dauda ya yi sa’ad da ya ce: “Zan albarkaci Ubangiji a kowane loto: Yabonsa kuwa za ya zauna a bakina tuttur. Raina za shi yi fahariya a cikin Ubangiji: Mai-tawali’u za ya ji, ya yi murna kuma.” (Zab. 34:1, 2) Wataƙila za mu iya taimaka wa wani ya soma bauta wa Jehobah ta wa’azin da muke yi.
KA ƊAUKAKA ALLAH TA SAMUN CI GABA A HIDIMARSA
19. Me ya sa ya kamata bawan Jehobah ya riƙa farin ciki ko da yana cikin yanayi mai wuya?
19 Dauda ya daɗa cewa: ‘Dukan ayyukanka za su yi godiya gareka, ya Ubangiji; Tsarkakanka kuma za su albarkace ka. Za su yi zancen ɗaukakar mulkinka, su kama maganar ikonka: Domin a sanar wa ’yan Adam ayyukanka masu-iko, da darajar ɗaukaka ta mulkinka.’ (Zab. 145:10-12) Hakika, dukan bayin Jehobah masu aminci suna so su yi hakan. Amma, idan rashin lafiya ko kuma tsufa suka hana ka yin abubuwan da kake so ka yi kuma fa? Ka tuna cewa kana ɗaukaka Allah a duk lokacin da ka yi wa waɗanda suke kula da kai kamar su nas-nas da likitoci da kuma waɗanda suke tare da kai wa’azi. Ƙari ga haka, idan kana kurkuku domin imaninka, za ka iya gaya wa mutane game da Jehobah kuma hakan yana sa shi farin ciki sosai. (Mis. 27:11) Hakazalika, Jehobah yana farin ciki da hidimar da kake masa ko da wasu a iyalinku ba sa bauta masa. (1 Bit. 3:1-4) Za ka iya yaba wa Jehobah, ka ƙarfafa dangantakarka da shi kuma ka samu ci gaba a bautar da kake masa ko da kana cikin yanayi mai wuya.
20, 21. Ta yaya wasu za su amfana idan kana da ƙarin aiki a ƙungiyar Jehobah?
20 Jehobah zai albarkace ka idan kana samun ci gaba a hidimarka. Idan ka yi wasu canje-canje a tsarin ayyukanka ko kuma salon rayuwarka, za ka samu damar taimaka wa mutane su koya game da alkawuran da Allah ya yi. Ƙari ga haka, ’yan’uwa za su amfana sosai daga sadaukarwar da kake yi. Ayyukanka a cikin ikilisiya za su sa ’yan’uwa su ƙaunace ka kuma su tallafa maka.
21 Ko da mun daɗe muna bauta wa Jehobah ko kuma mun soma yin hakan ba da daɗewa ba, dukanmu za mu iya samun ci gaba a bautarmu ga Jehobah. Amma ta yaya Kiristocin da suka manyanta za su taimaka wa sababbi su samu ci gaba a ƙungiyar Jehobah? Za mu tattauna wannan a talifi na gaba.