TALIFIN NAZARI NA 2
Wane Darasi Ne Za Mu Iya Koya Daga Ƙanen Yesu?
“Yakub bawan Allah da kuma na Ubangiji Yesu Almasihu.”—YAK. 1:1.
WAƘA TA 88 Ka Koya Mini Hanyoyinka
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1. Ka bayyana yadda iyalin Yakub take.
YAKUB ya fito daga iyalin da suke ƙaunar Jehobah sosai. Iyayensa, wato Yusufu da Maryamu masu ƙaunar Jehobah ne sosai kuma sun yi iya ƙoƙarinsu su bauta masa. Ban da wannan, yayansa ya zama Almasihu daga baya. Hakika ba ƙaramin gata ba ne Yakub ya samu na kasancewa a cikin irin wannan iyalin.
2. Waɗanne dalilai ne Yakub yake da su na bin misalin yayansa?
2 Akwai dalilai da yawa da suka sa ya kamata Yakub ya bi misalin yayansa. (Mat. 13:55) Alal misali, sa’ad da Yesu yake shekara 12, ya san Nassosi sosai har hakan ya burge malaman da suke Urushalima. (Luk. 2:46, 47) Wataƙila Yakub ya yi aikin kafinta tare da Yesu. Idan haka ne, mai yiwuwa yin aiki tare da Yesu ya sa ya daɗa sanin halayen ɗan’uwansa. A yawancin lokuta, Nathan H. Knorr yakan ce, “Idan kana aiki tare da mutum ne za ka iya sanin halinsa sosai.”b Babu shakka, Yakub ya lura da yadda “Yesu ya yi ta ƙaruwa da hikima da tsayi, ya kuma sami farin jini a gaban Allah da kuma a gaban mutane.” (Luk. 2:52) Don haka, za mu iya ɗauka cewa Yakub ne zai fara zama almajirin Yesu. Amma ba abin da ya faru ba ke nan.
3. Mene ne Yakub ya yi a lokacin da Yesu ya soma hidimarsa?
3 A lokacin da Yesu yake hidima a duniya, Yakub bai zama almajirinsa ba. (Yoh. 7:3-5) Mai yiwuwa Yakub yana ɗaya daga cikin dangin Yesu da suka ce Yesu “ya haukace!” (Mar. 3:21) Kuma babu abin da ya nuna cewa Yakub yana nan tare da mamarsa Maryamu a lokacin da aka kashe Yesu a kan gungumen azaba.—Yoh. 19:25-27.
4. Waɗanne darussa ne za mu tattauna?
4 Daga baya, Yakub ya ba da gaskiya ga Yesu kuma ya zama dattijo da ake daraja shi sosai a cikin ikilisiya. A wannan talifin, za mu tattauna darussa biyu da za mu iya koya daga Yakub: (1) dalilin da ya sa ya zama dole mu zama masu sauƙin kai, da kuma (2) yadda za mu iya zama masu koyarwa da kyau.
KU ZAMA MASU SAUƘIN KAI KAMAR YAKUB
5. Mene ne Yakub ya yi sa’ad da Yesu ya bayyana a gare shi bayan tashinsa daga mutuwa?
5 A wane lokaci ne Yakub ya soma bin Yesu? Bayan da aka tā da Yesu daga mutuwa, “ya bayyana ga Yakub, sa’an nan kuma ga dukan manzanni.” (1 Kor. 15:7) Bayan wannan haɗuwar ce Yakub ya zama mabiyin Yesu. Yana tare da manzannin Yesu a lokacin da suke jira su sami ruhu mai tsarki a cikin wani gidan sama a Urushalima. (A. M. 1:13, 14) Daga baya ya zama memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Kiristoci a ƙarni na farko. (A. M. 15:6, 13-22; Gal. 2:9) Kuma kafin shekara ta 62 bayan haihuwar Yesu, an hure shi ya rubuta wasiƙa ga Kiristoci shafaffu. Wannan wasiƙar za ta taimaka mana a yau sosai ko da muna da begen yin rayuwa a duniya ko a sama. (Yak. 1:1) Bisa ga abin da wani masanin tarihi a ƙarni na farko ya faɗa, babban firist na Yahudawa mai suna Hananiya ne ya sa aka kashe Yakub. Yakub ya riƙe amincinsa ga Jehobah har ƙarshen hidimarsa a duniya.
6. A wace hanya ce Yakub ya bambanta da shugabannin addinai na zamaninsa?
6 Yakub mai sauƙin kai ne. Me ya sa muka faɗi hakan? Ka yi tunanin abin da Yakub ya yi bayan da Yesu ya bayyana a gare shi da kuma abin da shugabannin addinai suka yi. Bayan da Yakub ya ga tabbaci cewa Yesu Ɗan Allah ne, Yakub ya amince da hakan. Amma ba abin da manyan firistoci a Urushalima suka yi ba ke nan. Sun san cewa Yesu ya tā da Li’azaru daga mutuwa da gaske, amma maimakon su yarda cewa Jehobah ne ya aiko Yesu duniya, sai suka yi ƙoƙari su kashe Yesu da Li’azaru. (Yoh. 11:53; 12:9-11) Daga baya da aka tā da Yesu daga mutuwa, sun yi ƙoƙarin hana mutane sanin hakan. (Mat. 28:11-15) Girman kai ya sa waɗannan shugabannin addinai sun ƙi Almasihu.
7. Me ya sa ya kamata mu guji girman kai?
7 Darasi: Ka guji girman kai kuma ka bar Jehobah ya koyar da kai. Kamar yadda cuta za ta iya sa zuciyar mutum ya kasa yin aiki yadda ya kamata, haka ma girman kai za ta iya sa ya yi mana wuya mu bi ja-gorancin Jehobah. Duk da hujjojin da Farisawa suka gani cewa Yesu shi ne Ɗan Allah kuma yana da ruhun Allah, girman kai ta hana su yarda da hakan. (Yoh. 12:37-40) Girman kansu ta cutar da su domin ta hana su samun rai na har abada. (Mat. 23:13, 33) Shi ya sa yake da muhimmanci sosai mu ci gaba da barin ruhun Allah da Kalmarsa su yi tasiri a kan halinmu da shawarwarinmu da kuma tunaninmu. (Yak. 3:17) Da yake Yakub mai sauƙin kai ne, ya yarda Jehobah ya koyar da shi. Kuma kamar yadda za mu gani a gaba, sauƙin kansa ne ya taimaka masa ya zama ƙwararren malami.
KA ƘWARE A YADDA KAKE KOYARWA KAMAR YAKUB
8. Me zai taimaka mana mu ƙware a matsayin malamai?
8 Yakub bai yi makaranta sosai ba. Babu shakka shugabannin addinai na zamaninsa sun ɗauke shi yadda suka ɗauki manzo Bitrus da manzo Yohanna, wato “marasa ilimi, … talakawa kuma.” (A. M. 4:13) Amma Yakub ya koyi yadda zai zama ƙwararren malami. Mun ga tabbacin hakan a littafin da ya rubuta da ke ɗauke da sunansa. Kamar Yakub, mai yiwuwa mu ma ba mu yi makaranta sosai ba. Duk da haka, da taimakon ruhun Jehobah da kuma koyarwa da muke samu daga ƙungiyarsa, mu ma za mu iya zama malamai da suka ƙware. Bari mu tattauna misalin Yakub a matsayin malami da kuma darussa da za mu iya koya daga wurinsa.
9. Yaya za ka bayyana yadda Yakub yake koyarwa?
9 Yakub bai yi amfani da manyan-manyan kalmomi ko ya bayyana abubuwa a hanya mai wuyar fahimta ba. Hakan ya sa masu sauraronsa sun san abin da ya kamata su yi da kuma yadda za su yi hakan. Alal misali, ka yi tunanin yadda Yakub ya koya wa Kiristoci ta hanya mai sauƙi cewa ya kamata su jimre rashin adalci da za a yi musu ba tare da riƙe mutane a zuciya ba. Ya ce: “Waɗanda suka jimre mukan ce da su masu albarka ne. Kun dai ji irin jimrewar da Ayuba ya yi, kun kuma san yadda Ubangiji ya albarkace shi a ƙarshe. Gama Ubangiji mai jinƙai ne, mai yawan tausayi kuma.” (Yak. 5:11) Ka lura cewa Yakub ya yi amfani da abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki ne sa’ad da yake magana. Ya yi amfani da Kalmar Allah don ya taimaka wa masu sauraronsa su san cewa Jehobah ba ya fasa yi wa masu aminci kamar Ayuba albarka. Yakub ya yi amfani da kalmomi da bayanai masu sauƙin fahimta don masu sauraronsa su fahimci abin da yake faɗa. Ta hakan ya jawo hankalin masu sauraronsa ga Jehobah maimakon kansa.
10. A wace hanya ce za mu iya bin misalin Yakub sa’ad da muke koyarwa?
10 Darasi: Ku koyar da mutane bisa ga abin da ke Kalmar Allah a hanya mai sauƙin fahimta. Idan muna koyar da mutane, kada mu yi ƙoƙarin burge su da iliminmu, amma mu nuna musu cewa Jehobah ne ya fi kowa ilimi kuma ya damu da su. (Rom. 11:33) Za mu iya yin hakan ta wajen tabbata cewa koyarwarmu ta jitu da Littafi Mai Tsarki. Alal misali, idan ɗalibanmu sun nemi shawara daga wurinmu, maimakon mu gaya musu abin da za mu yi da a ce mu ne muke yanayinsu, ya kamata mu taimaka musu su yi tunanin misalan da ke Littafi Mai Tsarki kuma su fahimci ra’ayin Jehobah da tunaninsa. Hakan zai sa su bi abin da muke koya musu domin suna so su faranta wa Jehobah rai, ba mu ba.
11. Waɗanne irin abubuwa ne Kiristoci a zamanin Yakub suka yi fama da su kuma wace irin shawara ce ya ba su? (Yakub 5:13-15)
11 Yakub ya san kasawar ’yan’uwansa kuma ya gaya musu. Daga abin da ya rubuta a wasiƙarsa, mun ga cewa Yakub ya san irin matsalolin da ’yan’uwansa masu bi suke fama da su kuma ya ba su shawara a kan abin da ya kamata su yi. Alal misali, a lokacin, yana yi ma wasu Kiristoci wuya su bi umurni. (Yak. 1:22) Wasu suna nuna son kai ga masu kuɗi. (Yak. 2:1-3) Wasu kuma ba sa iya kame bakinsu. (Yak. 3:8-10) Waɗannan Kiristocin suna da kasawa sosai, amma Yakub ya gaya musu cewa za su iya canjawa. Ya yi musu gargaɗi cikin alheri, amma bai yi kwana-kwana ba. Sa’an nan ya gaya ma waɗanda dangantakarsu da Jehobah ta yi sanyi cewa su nemi taimakon dattawa.—Karanta Yakub 5:13-15.
12. Ta yaya za mu kasance da ra’ayin da ya dace sa’ad da muke taimaka wa ɗalibanmu?
12 Darasi: Ka gaya wa mutane kasawarsu, amma kada ka ɗauka cewa ba za su canja ba. Zai iya yi wa ɗalibanmu wuya su bi abin da ke Littafi Mai Tsarki. (Yak. 4:1-4) Zai iya ɗaukansu lokaci kafin su canja halayensu marasa kyau kuma su soma yin abubuwa kamar Kiristoci na gaskiya. Kamar yadda Yakub ya yi, mu ma ya kamata mu sami ƙarfin zuciyar gaya wa ɗalibanmu inda suke bukatar su yi gyara. Amma ya kamata mu san cewa za su iya canjawa. Ƙari ga haka, ya kamata mu tuna cewa Jehobah ne yake jan mutane masu sauƙin kai zuwa wurinsa kuma zai iya ba su ƙarfin canja halayensu.—Yak. 4:10.
13. Mene ne Yakub ya faɗa a littafin Yakub 3:2?
13 Yakub ba mai ɗagun kai ba ne. Yakub bai ɗauka cewa ya fi wasu Kiristoci muhimmanci don shi ɗan’uwan Yesu ne ko don an ba shi ayyuka na musamman ya yi ba. Ya kira Kiristoci “ ’yan’uwana, waɗanda nake ƙauna.” (Yak. 1:16, 19; 2:5) Bai yi kamar shi ba ya kuskure ba. Amma ya nuna cewa abin da ya faɗa cewa “dukanmu mukan yi kuskure da yawa,” ya shafe shi.—Karanta Yakub 3:2.
14. Me ya sa yake da kyau mu amince cewa mu ma mukan yi kuskure?
14 Darasi: Mu tuna cewa dukanmu ajizai ne. Kada mu ɗauka cewa mun fi ɗalibanmu. Me ya sa? Idan muka sa ɗalibanmu su ɗauka cewa ba ma kuskure, za su iya yin sanyin gwiwa kuma su ɗauka cewa ba za su iya bauta wa Jehobah ba tare da yin kuskure ba. Amma idan mun gaya musu cewa ba kullum ba ne yake yi mana sauƙi mu bi abin da ke Littafi Mai Tsarki, kuma mun bayyana musu yadda Jehobah yake taimaka mana mu bi ƙa’idodinsa, hakan zai iya taimaka musu su ga cewa su ma za su iya bauta wa Jehobah.
15. Yaya za ka kwatanta irin misalan da Yakub ya yi amfani da su? (Yakub 3:2-6, 10-12)
15 Yakub ya yi amfani da misalai masu kyau. Hakika ruhu mai tsarki ne ya taimaka masa ya yi hakan. Amma da alama ya koyi yin amfani da misalai masu kyau daga yayansa wato, Yesu. Misalai da Yakub ya yi amfani da su a cikin wasiƙarsa masu sauƙin fahimta ne, kuma ya yi wa masu sauraronsa sauƙi su ga abin da ya kamata su yi.—Karanta Yakub 3:2-6, 10-12.
16. Me ya sa ya dace mu yi amfani da misalai masu kyau?
16 Darasi: Ka yi amfani da misalai masu kyau. Idan kana amfani da misalai yadda ya dace, za ka taimaka wa mutane su yi tunanin abin da ka faɗa kuma su ji kamar suna ganin abin da kake koya musu. Hakan zai taimaka wa masu sauraronka su tuna abubuwa masu muhimmanci da ka koya musu. Yesu ya ƙware sosai a yin amfani da misalai sa’ad da yake koyarwa, kuma ɗan’uwansa Yakub ma ya bi misalinsa. Bari mu tattauna ɗaya daga cikin misalan da Yakub ya yi amfani da su da kuma dalilin da ya sa misalin ya ratsa zuciyar mutane sosai.
17. Me ya sa misalin da ke Yakub 1:22-25 zai taimaka wa mutane sosai?
17 Karanta Yakub 1:22-25. Misalin madubi da Yakub ya bayar ya ratsa zuciyar mutane domin dalilai da yawa. Ya so ya taimaka wa masu sauraronsa su amfana daga Kalmar Allah, wato ta wajen karanta da kuma yin abin da suka koya. Yakub ya yi amfani da misalin da masu sauraronsa za su yi saurin fahimta, wato misalin mutumin da yake kallon madubi. Mene ne yake so ya koyar? Zai zama wauta idan mutum ya kalli madubi, ya ga abin da ya kamata ya gyara a fuskarsa amma bai yi hakan ba. Haka ma, zai zama wauta a gare mu idan muka karanta Kalmar Allah kuma muka ga wani abin da ya kamata mu canja a halinmu amma ba mu yi hakan ba.
18. Waɗanne abubuwa uku ne ya kamata mu yi idan muna so mu ba da misali?
18 Idan kana so ka yi amfani da misali, za ka iya yin koyi da Yakub ta wajen yin abubuwa uku da ke gaba: (1) Ka tabbata cewa misalin ya jitu da abin da kake so ka bayyana. (2) Ka yi amfani da misalin da masu sauraronka za su yi saurin fahimta. (3) Ka bayyana manufar misalin. Idan yana maka wuya ka san irin misalan da za ka iya amfani da su, ka duba Watch Tower Publications Index a Turanci. A ƙarƙashin jigon nan “Illustrations,” za ka iya ganin misalai da yawa da za ka iya amfani da su. Amma ka tuna cewa misalai suna kama da makarufo ne. Kamar yadda makarufo yake sa muryar mai magana ta fito da kyau, haka ma misalai za su iya sa muhimmin batun da ake koyarwa ya fito da kyau. Saboda haka, ka yi amfani da misalai a lokacin da kake so ɗalibinka ya fahimci muhimmin batun da kake koyar da shi ne kawai. Mu tuna cewa dalilin da ya sa ya kamata mu ƙware a koyarwa shi ne don mu taimaka wa mutane da yawa su kasance a cikin iyalin Jehobah mai farin ciki, ba don mu sa mutane su mai da hankali a kanmu ba.
19. Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar ’yan’uwanmu Kiristoci?
19 Yakub ya yi girma da yaya kamiltacce, amma mu ba mu da yayu kamiltattu. Duk da haka, muna da gatan bauta wa Jehobah tare da ’yan’uwa maza da mata masu yawan gaske. Za mu iya nuna musu cewa muna ƙaunarsu ta wajen yin tarayya da su, da koyan abubuwa daga wurinsu, da kuma yin hidima tare da su cikin aminci yayin da muke wa’azi da kuma koyar da mutane. Idan muna yin iya ƙoƙarinmu mu bi misalin Yakub ta halinmu da ayyukanmu da kuma yadda muke koyarwa, za mu ɗaukaka Jehobah kuma za mu taimaka wa mutane masu zuciyar kirki su kusaci Ubanmu na sama mai ƙauna.
WAƘA TA 114 Ku Kasance Masu “Haƙuri”
a Yakub ya fito daga iyali ɗaya da Yesu. Yakub ya san Yesu fiye da yawancin mutane a zamaninsa. A wannan talifin, za mu tattauna abin da za mu koya daga rayuwa da kuma koyarwar ƙanen Yesu, wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda suka ja-goranci ikilisiyar Kirista a ƙarni na farko.
b Ɗan’uwa Nathan H. Knorr memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ne a dā. Ya gama hidimarsa a duniya a 1977.
c BAYANI A KAN HOTO: Yakub ya yi amfani da wuta wajen kwatanta hadarin yin amfani da harshe a hanyar da bai kamata ba. Misalin yana da kyau sosai domin kowa ya san cewa ƙaramar wuta za ta iya jawo gobara.