TALIFIN NAZARI NA 32
Matasa Ku Ci Gaba da Manyanta Bayan Kun Yi Baftisma
“Cikin ƙauna, mu yi girma cikin al’amuranmu duka.”—AFIS. 4:15.
WAƘA TA 56 Ka Riƙe Gaskiya
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1. Waɗanne abubuwa masu kyau ne matasa da yawa suka riga suka yi?
A KOWACE shekara, dubban matasa suna yin baftisma. Kai ma ka yi hakan? Idan haka ne, ʼyan’uwanka maza da mata suna taya ka murna, kuma Jehobah ma yana farin ciki! (K. Mag. 27:11) Ka yi tunanin abubuwan da ka riga ka cim ma. Wataƙila ka yi shekaru da yawa kana nazarin Littafi Mai Tsarki. Nazarin da ka yi ya tabbatar maka cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce. Abu mafi muhimmanci ma, ka san mawallafin wannan littafin kuma ka soma ƙaunar shi. Yadda kake ƙaunar Jehobah ya ƙaru har ya sa ka yi alkawarin bauta masa kuma ka yi baftisma. Hakan zaɓi mai kyau ne!
2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
2 Babu shakka an gwada bangaskiyarka a hanyoyi da yawa yayin da kake ƙoƙarin samun ci gaba don ka yi baftisma. Amma yayin da kake girma, za ka fuskanci sabbin jarrabobi. Shaiɗan zai yi ƙoƙari ya sa ka daina ƙaunar Jehobah da kuma bauta masa. (Afis. 4:14) Kada ka bar hakan ya faru. Mene ne zai taimaka maka ka riƙe amincinka ga Jehobah kuma ka cika alkawarinka? Dole ne ka ci gaba da manyanta. (Ibran. 6:1) Amma ta yaya za ka yi hakan? Za mu tattauna hakan a wannan talifin.
TA YAYA ZA KA MANYANTA A MATSAYIN KIRISTA?
3. Mene ne dukan Kiristoci suke bukatar su yi bayan sun yi baftisma?
3 Bayan mun yi baftisma, dukanmu muna bukatar mu bi shawarar da manzo Bulus ya ba Kiristoci a Afisa. Ya ƙarfafa su cewa su “zama cikakkun” Kiristoci. (Afis. 4:13) Hakan yana nufin cewa ya kamata su ci gaba da manyanta. Bulus ya kwatanta yadda muke manyanta a matsayin Kiristoci da yadda yaro yake girma. Iyaye suna ƙaunar jaririnsu, kuma suna alfahari da shi. Amma dole ne jaririn ya yi girma. Da shigewar lokaci, dole ya bar halin yarintaka. (1 Kor. 13:11) Haka yake da Kiristoci. Bayan baftisma, dole mu ci gaba da manyanta. Bari mu tattauna wasu shawarwari da za su taimaka mana mu yi hakan.
4. Mene ne zai taimaka maka ka sami ci gaba? Ka bayyana. (Filibiyawa 1:9)
4 Ka daɗa ƙaunar Jehobah. Babu shakka kana ƙaunar Jehobah sosai, amma za ka iya daɗa ƙaunar shi. Ta yaya? Manzo Bulus ya ambata hanya ɗaya na yin hakan a Filibiyawa 1:9. (Karanta.) Bulus ya yi addu’a cewa ƙaunar da Filibiyawa suke da ita “ta yi ta yalwata.” Don haka, za mu iya daɗa ƙaunar Jehobah. Za mu iya yin hakan ta wajen samun “sanin Allah da kuma kowace irin ganewa.” Yayin da muke daɗa sanin Jehobah, za mu daɗa ƙaunar shi da halayensa da kuma yadda yake yin abubuwa. Za mu daɗa so mu faranta masa rai a kowane lokaci, kuma mu guji yin abin da zai ɓata masa rai. Za mu yi iya ƙoƙarinmu mu san nufinsa da kuma yadda za mu yi shi.
5-6. Ta yaya za mu daɗa ƙaunar Jehobah? Ka bayyana.
5 Yesu ya bi misalin Jehobah sau da ƙafa, don haka, idan muka san Yesu sosai, za mu daɗa ƙaunar Jehobah. (Ibran. 1:3) Hanya mafi kyau na sanin Yesu ita ce yin nazarin littattafan Linjila. Idan ba ka riga ka soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki a kullum ba, zai dace ka soma yin hakan yanzu. Yayin da kake karanta labarin Yesu, ka mai da hankali ga halayensa. Mutane sun ji daɗin zuwa wurinsa da kuma tattaunawa da shi. Ya kira yara zuwa wurinsa kuma ya ɗauke su a hannunsa. (Mar. 10:13-16) Almajiransa ba su ji tsoron gaya masa abin da ke zuciyarsu ba, domin ya sa sun saki jiki da shi. (Mat. 16:22) Mun san cewa Yesu ya bi misalin Ubansa ne, shi ya sa muka san cewa Jehobah ma haka yake. Za mu iya yin addu’a a gare shi kuma mu gaya masa kome da ke zuciyarmu. Muna da tabbaci cewa ba zai shari’anta mu ba, yana ƙaunar mu kuma ya damu da mu.—1 Bit. 5:7.
6 Yesu ya tausaya wa mutane. Manzo Matiyu ya ce: “Da ya ga jama’a sun taru da yawa, sai ya ji tausayinsu, gama suna shan wahala kuma ba mai taimako, kamar tumakin da ba su da makiyayi.” (Mat. 9:36) Jehobah kuma fa, ya yake ji? Yesu ya ce: “Ba nufin Ubanku wanda yake cikin sama ba ne ɗaya daga cikin yara ƙananan nan ya ɓata.” (Mat. 18:14) Waɗannan kalmomin suna sa mu farin ciki! Yayin da muke daɗa sanin Yesu, za mu daɗa ƙaunar Jehobah.
7. Ta yaya yin cuɗanya da Kiristoci da suka manyanta zai taimaka maka?
7 Za ka iya koyan yadda za ka daɗa ƙaunar Jehobah kuma ka manyanta idan kana tarayya da ʼyan’uwa maza da mata da suka manyanta a ikilisiyarku. Ka lura da yadda suke farin ciki. Ba sa da-na-sani don shawarar bauta wa Jehobah da suka yanke. Ka tambaye su su ba ka labarin abubuwan da suka faru a hidimarsu ga Jehobah. Idan kana da shawara mai muhimmanci da kake so ka yanke, ka nemi shawararsu. Ka tuna cewa “yawan masu ba da shawara yakan kawo [“nasara,” NWT].”—K. Mag. 11:14.
8. Mene ne za ka iya yi idan ka soma shakkar koyarwar Littafi Mai Tsarki?
8 Ka daina shakka. Kamar yadda aka ambata a sakin layi na 2, Shaiɗan zai yi iya ƙoƙarinsa ya sa ka kasa samun ci gaba. Hanya ɗaya da zai yi hakan ita ce ta wajen sa ka soma shakkar koyarwar Littafi Mai Tsarki. Alal misali, mutane da yawa za su gaya maka cewa babu Mahalicci kuma abubuwa sun fito ne haka kawai. Wataƙila ba ka taɓa tunanin wannan batun a lokacin da kake ƙarami ba. Amma yanzu da ka yi girma, an soma koya muku hakan a makaranta. Malamanku za su iya ba da hujjoji da za su sa ka ga kamar koyarwar juyin halitta gaskiya ce. Amma wataƙila ba su taɓa mai da hankali ga abubuwan da suka nuna cewa akwai Mahalicci ba. Ka tuna ƙa’idar da ke Karin Magana 18:17, wurin ya ce: “Mai fara kawo ƙara, ana ganinsa kamar mai gaskiya ne, sai bayan da abokin shari’arsa ya kawo hujjarsa, za a gane shi.” Maimakon kawai ka amince da abubuwan da ka koya a makaranta, ka bincika Kalmar Allah don ka san gaskiyar batun. Ka yi bincike a cikin littattafanmu. Ka tattauna da ʼyan’uwa maza da mata da suka amince da koyarwar juyin halitta a dā. Ka tambaye su abubuwan da suka tabbatar musu cewa akwai Mahalicci da yake ƙaunar mu. Irin wannan tattaunawar za ta taimaka maka ka mai da hankali ga gaskiyar wannan batun.
9. Me ka koya daga labarin Melissa?
9 Wata ʼyar’uwa mai suna Melissa ta amfana sosai daga binciken da ta yi a kan koyarwar juyin halitta.b Ta ce: “A makaranta, ana koyar da juyin halitta a hanyar da mutum zai gaskata da hakan. Da farko, na ji tsoron yin bincike a kan wannan batun, domin ina ganin kamar idan na yi binciken, zan gano cewa koyarwar gaskiya ce. Amma na gaya wa kaina cewa Jehobah yana so mu yi imani da wanzuwarsa bisa ga hujjoji masu kyau. Don haka, sai na soma yin bincike. Na karanta littafin nan Is There a Creator Who Cares About You? da kuma ƙasidun nan Was Life Created? da The Origin of Life—Five Questions Worth Asking. Yin hakan ya taimaka mini sosai. Da na sani da na yi binciken nan tun da wuri.”
10-11. Mene ne zai taimaka maka ka kasance da ɗabi’a mai kyau? (1 Tasalonikawa 4:3, 4)
10 Ka guje wa halin da bai dace ba. Idan kai matashi ne, za ka iya soma sha’awar yin jima’i sosai, kuma mutane za su iya ƙarfafa ka ka yi hakan. Abin da Shaiɗan ma yake so ka yi ke nan. Mene ne zai taimaka maka ka guji jarrabar yin lalata? (Karanta 1 Tasalonikawa 4:3, 4.) Idan kana addu’a, ka gaya wa Jehobah yadda kake ji, kuma ka roƙe shi ya ba ka ƙarfin gwiwa. (Mat. 6:13) Ka tuna cewa Jehobah yana so ya taimaka maka, ba ya hukunta ka ba. (Zab. 103:13, 14) Ban da haka, Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka maka. Melissa wadda aka ambata ɗazu ta yi ƙoƙari sosai don ta guji yin tunanin lalata. Ta ce: “Karanta Littafi Mai Tsarki a kowace rana ya taimaka mini in guji yin tunanin lalata. Ya tuna min cewa ni na Jehobah ce kuma ina bukatar sa a rayuwata.”—Zab. 119:9.
11 Kada ka yi ƙoƙarin magance matsalarka da kanka. Ka gaya wa iyayenka abubuwan da kake fuskanta. Tattauna irin waɗannan batutuwan bai da sauƙi, amma yana da muhimmanci ka yi hakan. Melissa ta ce: “Na yi addu’a Jehobah ya ba ni ƙarfin zuciya, sai na gaya wa mahaifina abin da ke damuna. Bayan hakan, na sami kwanciyar hankali kuma na san cewa Jehobah yana alfahari da ni.”
12. Me zai taimaka maka ka yanke shawarwari masu kyau?
12 Ka riƙa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Yayin da kake girma, iyayenka za su soma barin ka ka riƙa yanke shawara da kanka. Amma akwai abubuwa da yawa da ba ka sani ba. Ta yaya za ka guji yin abin da zai ɓata dangantakarka da Jehobah? (K. Mag. 22:3) Wata ʼyar’uwa mai suna Kari ta bayyana abin da ke taimaka mata ta yanke shawarwari masu kyau. Ta fahimci cewa Kiristoci da suka manyanta ba sa bukatar a ba su doka a kan kome da kome. Ta ce: “Na bukaci in fahimci ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba dokokin kawai ba.” Sa’ad da kake karanta Littafi Mai Tsarki, ka tambayi kanka: ‘Mene ne wannan ayar ta nuna mini game da yadda Jehobah yake yin tunani? Ayar tana ɗauke da ƙa’idodin da za su taimaka mini in kasance da ɗabi’u masu kyau? Idan haka ne, ta yaya zan amfana idan na bi ƙa’idodin?’ (Zab. 19:7; Isha. 48:17, 18) Ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin bimbini a kan ƙa’idodin da ke ciki, zai yi maka sauƙi ka yanke shawarwarin da za su faranta wa Jehobah rai. Yayin da kake daɗa manyanta, za ka gane cewa ba sai an ba ka doka a kan kowane batu ba, domin za ka san ra’ayin Jehobah a kan batutuwa dabam-dabam.
13. Ta yaya abokan kirki za su taimaka maka? (Karin Magana 13:20)
13 Ka zaɓi abokan da suke bauta wa Jehobah. Kamar yadda aka ambata ɗazu, abokanka za su iya taimaka maka ka zama Kirista da ya manyanta. (Karanta Karin Magana 13:20.) Akwai lokacin da wata ʼyar’uwa mai suna Sara ta soma baƙin ciki. Sai wani abu ya faru da ya taimaka mata. Sara ta ce: “Na sami ƙawayen kirki a lokacin da nake bukata. Ni da wata ʼyar’uwa matashiya mukan haɗu kowane mako don mu shirya talifin Hasumiyar Tsaro da za a yi nazarin sa. Wata ƙawata kuma ta taimaka mini in soma kalamai a taro. Da taimakon ƙawayena, na soma yin nazari da kuma addu’a da kyau, na soma ƙarfafa dangantakata da Jehobah kuma hakan ya sa na soma farin ciki.”
14. Ta yaya Julien ya sami abokan kirki?
14 Ta yaya za ka ƙulla abokantaka da mutanen da za su taimaka maka? Wani ɗan’uwa mai suna Julien wanda dattijo ne yanzu ya ce: “Sa’ad da nake matashi, na ƙulla abokantaka da ʼyan’uwa yayin da muke wa’azi tare. Suna da ƙwazo sosai, kuma sun taimaka mini in ga cewa yin wa’azi yana da daɗi sosai. Sai na kafa maƙasudin zama majagaba na kullum. Ƙari ga haka, na gano cewa dalilin da ya sa na rasa abokan kirki shi ne na mai da hankali ga neman abokai tsarana kawai. Ban da haka, na yi abokan kirki yanzu da nake Bethel. Misalinsu ya taimaka mini in riƙa zaɓan nishaɗi mai kyau, kuma hakan ya sa na kusaci Jehobah.”
15. Mene ne Bulus ya gaya wa Timoti game da abokai? (2 Timoti 2:20-22)
15 Mene ne za ka yi idan ka gano cewa yin tarayya da wani a ikilisiya zai ɓata dangantakarka da Jehobah? Bulus ya san cewa wasu ʼyan’uwa a cikin ikilisiya ba sa yin tunani ko kuma abubuwa kamar Kiristoci. Don haka, ya gaya wa Timoti ya guje wa irin mutanen nan. (Karanta 2 Timoti 2:20-22.) Dangantakarmu da Jehobah tana da muhimmanci sosai. Mun riga mun yi iya ƙoƙarinmu mu kusaci Jehobah. Don haka, bai kamata mu bar abokai su ɓata wannan dangantakar ba.—Zab. 26:4.
TA YAYA KAFA MAƘASUDAI ZAI TAIMAKA MAKA KA MANYANTA?
16. Waɗanne irin maƙasudai ne ya kamata ka kafa?
16 Ka kafa maƙasudan da za su amfane ka. Ka kafa maƙasudan da za su ƙarfafa bangaskiyarka kuma su taimaka maka ka manyanta. (Afis. 3:16) Alal misali, za ka iya kafa maƙasudin inganta yadda kake yin nazari da kuma karanta Littafi Mai Tsarki. (Zab. 1:2, 3) Ko kuma za ka iya kafa maƙasudin ƙara yawan lokutan da kake yin addu’a kuma ka riƙa yin sa daga zuciya. Za ka ma iya kafa maƙasudin mai da hankali ga irin nishaɗin da kake yi, da kuma yadda kake amfani da lokacinka. (Afis. 5:15, 16) Idan Jehobah ya ga kana yin iya ƙoƙarinka don ka sami ci gaba, zai yi farin ciki.
17. Ta yaya za ka amfana idan kana taimaka wa mutane?
17 Za ka manyanta a matsayin Kirista idan kana taimaka wa mutane. Yesu ya ce: “Ya fi albarka a bayar da a karɓa.” (A. M. 20:35) Za ka amfana sosai idan ka yi amfani da lokacinka da kuma kuzarinka don ka taimaka ma wasu. Alal misali, za ka iya kafa maƙasudin taimaka wa tsofaffi a ikilisiyarku ko kuma waɗanda suke rashin lafiya. Za ka iya zuwa musu aika ko kuma ka koya musu amfani da na’urori. Idan kai ɗan’uwa ne, za ka iya kafa maƙasudin zama bawa mai hidima domin ka taimaka wa ʼyan’uwanka. (Filib. 2:4) Ban da haka, za ka nuna cewa kana ƙaunar mutane idan kana yin wa’azin Mulkin Allah. (Mat. 9:36, 37) Idan zai yiwu, ka kafa maƙasudin yin hidima ta cikakken lokaci.
18. Ta yaya yin hidima ta cikakken lokaci zai taimaka maka ka sami ci gaba?
18 Hidima ta cikakken lokaci za ta taimaka maka ka kusaci Jehobah. Idan kai majagaba ne, za ka iya halartan Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki. Za ka iya yin hidima a Bethel ko kuma ka taimaka da wuraren ibadarmu. Wata ʼyar’uwa majagaba mai suna Kaitlyn ta ce: “Yin wa’azi tare da ʼyan’uwa maza da mata da suka manyanta ya taimaka mini sosai in sami ci gaba bayan na yi baftisma. Misalinsu ya taimaka mini in daɗa nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma inganta yadda nake koyarwa.”
19. Waɗanne albarku ne za ka samu yayin da kake manyanta?
19 Yayin da ka ci gaba da manyanta, za ka more albarku da yawa. Ba za ka yi amfani da kuzarinka wajen neman abubuwan da ba za su amfane ka ba. (1 Yoh. 2:17) Ba za ka sha wahala domin ka yanke shawarwarin da ba su dace ba. A maimakon haka, za ka yi farin ciki kuma za ka yi nasara. (K. Mag. 16:3) Misalinka mai kyau zai ƙarfafa ʼyan’uwa manya da ƙanana. (1 Tim. 4:12) Abu mafi muhimmanci ma, za ka more salama da kuma gamsuwa don kana faranta wa Jehobah rai kuma kana da dangantaka mai kyau da shi.—K. Mag. 23:15, 16.
WAƘA TA 88 Ka Koya Mini Hanyoyinka
a Muna farin ciki a duk lokacin da muka ga matasa sun yi baftisma. Hakika bayan sun yi baftisma, matasa suna bukatar su ci gaba da manyanta. Don amfanin kowa a ikilisiya, wannan talifin zai tattauna hanyoyin da waɗanda ba su daɗe da yin baftisma ba, za su ci gaba da manyanta a matsayin Kiristoci.
b An canja wasu sunayen.