TALIFIN NAZARI NA 34
Ku Ci Gaba da “Bin Gaskiya”
Ku ci gaba da “bin gaskiya.”—3 YOH. 4.
WAƘA TA 111 Dalilan da Suke Sa Mu Murna
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1. Ta yaya kake amfana yayin da kake tattauna da wasu game da yadda ka zama Mashaidin Jehobah?
BA MAMAKI an sha yi maka tambayar nan, “Ta yaya ka koyi gaskiya?” Yana ɗaya daga cikin tambayoyin da ’yan’uwanmu sukan yi mana sa’ad da suke so su san game da mu. Muna farin cikin sanin yadda ’yan’uwanmu suka koya game da Jehobah kuma suka soma ƙaunar sa. Kuma mu ma muna farin cikin gaya musu yadda muka zama Shaidun Jehobah. (Rom. 1:11) Irin wannan tattaunawar yana taimaka mana mu tuna yadda muke farin ciki domin mu Shaidun Jehobah ne. Ƙari ga haka, yana sa mu ƙudiri niyyar ci gaba da “bin gaskiya,” wato mu ci gaba da yin irin rayuwar da za ta sa Jehobah ya amince da mu kuma ya yi mana albarka.—3 Yoh. 4.
2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
2 A wannan talifin, za mu tattauna wasu dalilai da suka sa muke son gaskiya. Sa’an nan za mu tattauna yadda za mu ci gaba da nuna ƙauna don wannan kyauta mai daraja da Jehobah ya ba mu. Hakan zai sa mu daɗa gode wa Jehobah domin yadda ya jawo mu cikin gaskiyar. (Yoh. 6:44) Zai kuma ƙarfafa mu mu gaya ma wasu game da gaskiyar.
ABIN DA YA SA MUKE SON GASKIYA
3. Wane dalili mafi muhimmanci ne ya sa muke son gaskiya?
3 Akwai dalilai da yawa da suka sa muke son gaskiya. Muhimmin dalili shi ne muna ƙaunar Jehobah wanda shi ne tushen gaskiyar. Ta wurin Kalmarsa Littafi Mai Tsarki, mun koyi cewa shi Uba ne mai ƙauna da ke kula da mu, ba mafi iko duka da ya halicci sama da ƙasa kawai ba. (1 Bit. 5:7) Mun san cewa Allahnmu “mai jinƙai ne, mai alheri, marar saurin fushi, mai yawan ƙauna marar canjawa, cike da aminci kuma.” (Fit. 34:6) Jehobah yana son adalci. (Isha. 61:8) Yana baƙin ciki idan ya ga muna shan wahala kuma yana marmarin kawo ƙarshen dukan wahalolinmu a lokacin da ya dace. (Irm. 29:11) Mu ma muna marmarin zuwan lokacin! Shi ya sa muke ƙaunar Jehobah sosai!
4-5. Me ya sa manzo Bulus ya kwatanta begenmu da anka?
4 Wane dalili ne kuma ya sa muke son gaskiya? Gaskiyar Littafi Mai Tsarki tana sa mu amfana sosai. Ka yi la’akari da wannan kwatanci. Gaskiyar Littafi Mai Tsarki ta ƙunshi bege da muke da shi. Manzo Bulus ya ba da kwatanci da ya nuna muhimmancin begen da muke da shi. Ya ce: “Begen nan kuwa da muke da shi, kamar anka yake ga rai, kafaffe, tabbatacce.” (Ibran. 6:19, Mai Makamantu Ayoyi) Kamar yadda anka take riƙe jirgin ruwa don kada iska ta tafi da shi, haka ma begen da muke da shi yana taimaka mana mu sami kwanciyar hankali a lokacin da muke fama da matsaloli.
5 A wannan ayar, manzo Bulus yana magana ne game da begen yin rayuwa a sama da shafaffu suke da shi. Amma abin da ya faɗa ya shafi Kiristoci da suke da begen yin rayuwa har abada a duniya. (Yoh. 3:16) Babu shakka abin da muka koya game da rayuwa har abada, ya sa muna yin rayuwa mai ma’ana.
6-7. Ta yaya Yvonne ta amfana don ta koyi game da abin da zai faru a nan gaba?
6 Ka yi la’akari da labarin wata ’yar’uwa mai suna Yvonne. Iyayenta ba Shaidun Jehobah ba ne, kuma sa’ad da take ƙarama, takan ji tsoron mutuwa. Ta tuna da wani abin da ta karanta da ta riƙa tunani a kansa, wato: “Wata rana sai labari.” Ta ce: “Kalmomin sun sa ba na iya barci da dare ina ta tunani game da nan gaba.” Yvonne ta tambayi kanta dalilin da ya sa muke rayuwa na ɗan lokaci sa’an nan mu mutu. Ba ta san dalilin da ya sa aka halicce mu ba, amma ba ta so ta mutu!
7 Daga baya sa’ad da ta zama matashiya, Yvonne ta haɗu da Shaidun Jehobah. Ta ce: “Na soma gaskata cewa zan iya samun begen yin rayuwa har abada a Aljanna a duniya.” Ta yaya ’yar’uwarmu ta amfana daga koyan gaskiya? Ta ƙara da cewa: “A yanzu ba na tashiwa da dare ina tunani game da nan gaba ko kuma mutuwa.” Ba shakka, Yvonne tana son gaskiyar da ta koya, kuma tana jin daɗin gaya ma wasu game da abin da zai faru a nan gaba.—1 Tim. 4:16.
8-9. (a) A wani kwatancin da Yesu ya yi, ta yaya wani mutum ya daraja dukiyar da ya samu? (b) Yaya kake daraja gaskiya game da Mulkin Allah?
8 Gaskiyar Littafi Mai Tsarki ta kuma ƙunshi albishiri game da Mulkin Allah. Yesu ya kwatanta gaskiya game da Mulkin Allah da dukiya da aka ɓoye. A Matiyu 13:44, Yesu ya ce: “Mulkin sama kamar dukiya ne wadda aka ɓoye a gona, wadda wani ya samu, ya sāke ɓoyewa. Saboda yawan murna ya je ya sayar da dukan abubuwan da yake da su, ya sayi gonar.” Ka lura cewa da farko ba wai mutumin yana neman dukiyar ba ne, amma da ya same ta, ya yi sadaukarwa sosai don ta zama tasa. Ya ma sayar da dukan abin da yake da shi. Me ya sa? Domin ya san cewa dukiyar tana da daraja sosai. Tana da daraja fiye da dukan abubuwan da ya sadaukar.
9 Haka kake ɗaukan gaskiya game da Mulkin Allah da daraja? Ba shakka haka kake ɗaukan sa! Mun san cewa babu abin da duniyar nan za ta ba mu da zai kai farin cikin da muke samu domin muna bauta wa Jehobah da kuma begen yin rayuwa har abada a duniya ƙarƙashin Mulkin Allah. Gatan da muke da shi na kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah ya fi duk wata sadaukarwa da muka yi. Abin da ya fi sa mu farin ciki shi ne “faranta masa rai.”—Kol. 1:10.
10-11. Me ya sa Michael ya canja salon rayuwarsa?
10 Yawancinmu mun yi sadaukarwa da yawa don mu sami amincewar Jehobah. Wasu sun bar aikin da ake biyan su albashi mai tsoka, wasu kuma sun daina ƙoƙarin su yi arziki. Ƙari ga haka, wasu sun canja yadda suke rayuwa sa’ad da suka koya game da Jehobah. Abin da Michael ya yi ke nan. Iyayensa ba Shaidun Jehobah ba ne. Tun yana ƙarami, an koya masa damben karate. Ya ce: “A dā, abin da ya fi muhimmanci a gare ni shi ne in kasance da ƙarfin jiki. A wasu lokuta, nakan ji kamar babu wanda ya isa ya ja da ni.” Amma sa’ad da ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki, Michael ya koya yadda Jehobah yake ji game da faɗa. (Zab. 11:5) Ga abin da Michael ya faɗa game da ma’aurata da suka yi nazari da shi: “Ba su taɓa ce min dole ne in daina yin damben karate ba, amma sun ci gaba da koya min gaskiyar Littafi Mai Tsarki.”
11 Yayin da Michael yake ci gaba da koya game da Jehobah, yadda yake ƙaunar Jehobah ya ci gaba da ƙaruwa. Abin da ya fi burge Michael shi ne yadda Jehobah yake tausaya ma bayinsa. Da shigewar lokaci, Michael ya gano cewa yana bukatar ya yanke shawara game da rayuwarsa. Ya ce: “Na san cewa daina yin wasan damben zai yi min wuya fiye da kome. Amma na kuma san cewa yin hakan zai sa Jehobah farin ciki, kuma bauta masa ta fi duk wata sadaukarwa da zan yi.” Michael ya san cewa gaskiyar da ya koya tana da daraja, shi ya sa a shirye yake ya yi canje-canje a rayuwarsa.—Yak. 1:25.
12-13. Ta yaya gaskiyar Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa Mayli?
12 Littafi Mai Tsarki ya kwatanta gaskiyar da ke cikinsa da fitila da ke haske a cikin duhu domin ya nuna mana darajar gaskiyar. (Zab. 119:105; Afis. 5:8) Wata ’yar’uwa mai suna Mayli daga ƙasar Azarbajan, tana farin ciki sosai domin yadda Littafi Mai Tsarki ya taimaka mata. Iyayenta mabiya addinai dabam-dabam ne. Babanta Musulmi ne, mamarta kuma Bayahudiya ce. Ta ce: “Ko da yake na san cewa Allah yana wanzuwa, amma akwai wasu tambayoyi da ban san amsoshinsu ba. Na yi tunanin dalilin da ya sa Allah ya halicci ’yan Adam, da kuma dalilin da zai sa mutum ya sha wahala a duk rayuwarsa kuma a ƙarshe ya sha azaba a cikin wutar jahannama. Da yake mutane sukan ce Allah ne yake ƙaddara abubuwan da ke faruwa, na yi ta tambayar kaina cewa, ‘Shin Allah ne yake sa mutane su yi abubuwa, sa’an nan ya yi farin ciki sa’ad da suke shan wahala?’ ”
13 Mayli ta ci gaba da neman amsoshin tambayoyinta. Da shigewar lokaci, ta yarda a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita kuma ta zama Mashaidiyar Jehobah. Ta ce: “Gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki ta taimaka min in yi farin ciki fiye da dā. Bayanai masu gamsarwa da na samu a cikin Kalmar Allah, sun ba ni kwanciyar hankali.” Kamar Mayli dukanmu muna yabon Jehobah ‘wanda ya kiraye mu daga cikin duhu zuwa cikin haskensa mai-ban al’ajabi.’—1 Bit. 2:9, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.
14. Ta yaya za mu daɗa son gaskiya? (Ka duba akwatin nan “Ƙarin Abubuwan da Za Mu Iya Kwatanta Littafi Mai Tsarki da Su.”)
14 Waɗannan kaɗan ne daga cikin misalan da suka nuna amfanin kasancewa cikin ƙungiyar Jehobah. Babu shakka za ka iya tunanin ƙarin wasu misalai. Za ka iya yin bincike don ka ga wasu dalilai kuma da suka sa ya kamata mu so gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki. Yin hakan zai sa mu daɗa son gaskiya. Yayin da muke daɗa son gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki, za mu ci gaba da neman hanyoyi da za mu nuna hakan.
YADDA ZA MU NUNA CEWA MUNA SON GASKIYA
15. Ta yaya za mu nuna cewa muna son gaskiya?
15 Za mu iya nuna cewa muna son gaskiya ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki da kuma littattafanmu a kullum. Domin kome yawan shekarun da muka yi muna bauta ma Jehobah, muna koyan sabbin abubuwa a ko da yaushe. Mujallar Hasumiyar Tsaro ta farko ta ce gaskiyar Littafi Mai Tsarki tana kamar “furen da ciyawa ya rufe shi. Idan muna son mu ga wannan furen, sai mun neme shi a hankali. Idan mutum ya gan shi, zai so ya ƙara neman wasu kuma ba zai daina nema ba. Hakazalika, idan muka fahimci wata koyarwar Littafi Mai Tsarki, bai kamata mu daina nazari ba. Babu shakka, zai dace mu yi marmarin cika zuciyarmu da koyarwar Littafi Mai Tsarki.” Yin nazari bai da sauƙi, amma idan mun yi hakan, za mu amfana.
16. Wane salon nazarin Littafi Mai Tsarki ne ka fi jin daɗin sa? (Karin Magana 2:4-6)
16 Ba dukanmu ne muke jin daɗin yin karatu da kuma nazari ba. Amma Jehobah yana so mu ci gaba da yin hakan don mu daɗa fahimtar gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki. (Karanta Karin Magana 2:4-6.) A duk lokacin da muka yi hakan, muna amfana. Wani ɗan’uwa mai suna Corey ya ce yakan yi nazarin aya ɗaya bayan ɗaya. Ya ce: “Nakan karanta duk ƙarin bayanin da ke ayar, da kuma wasu ayoyi da suke da alaƙa da ayar kuma in yi ƙarin bincike a kan ayar. . . . Ina amfana sosai daga wannan salon nazarin Littafi Mai Tsarki!” Ko da muna bin wannan salon ko kuma wani salo dabam, idan muna yin iya ƙoƙarinmu don mu yi nazarin Kalmar Allah, za mu nuna cewa muna son gaskiya.—Zab. 1:1-3.
17. Me kuma muke bukatar mu yi ban da nazarin Littafi Mai Tsarki? (Yakub 1:25)
17 Mun san cewa ba nazarin Littafi Mai Tsarki ne kawai muke bukatar mu yi ba. Amma don mu amfana sosai, muna bukatar mu aikata abubuwan da muka koya. Sai mun yi hakan ne za mu yi farin ciki a rayuwa. (Karanta Yakub 1:25.) Ta yaya za mu san cewa muna aikata abubuwan da muke koya? Wani ɗan’uwa ya ce za mu iya yin hakan ta wajen bincika kanmu don mu san inda muke ƙoƙari da kuma inda muke bukatar gyara. Ga yadda manzo Bulus ya bayyana hakan, ya ce: “Babban abin shi ne duk inda muka kai, mu ci gaba daga nan.”—Filib. 3:16.
18. Me ya sa muke yin iya ƙoƙarinmu domin mu ci gaba da “bin gaskiya”?
18 Ka yi tunanin yadda muke amfana domin muna yin iya ƙoƙarinmu mu ci gaba da “bin gaskiya”! Hakan yana inganta rayuwarmu, kuma Jehobah da ’yan’uwanmu suna yin farin ciki. (K. Mag. 27:11; 3 Yoh. 4) Hakika, waɗannan su ne dalilai mafi muhimmanci da suka sa muke bukatar mu so gaskiya kuma mu yi rayuwa da ta jitu da hakan.
WAƘA TA 144 Mu Riƙa Ɗokin Samun Ladan!
a A yawancin lokuta, muna kiran imaninmu da kuma salon rayuwarmu hanyar gaskiya. Ko da ba mu jima da samun gaskiya ba, ko kuma an haife mu a cikin gaskiya, dukanmu za mu iya amfana daga tattauna dalilan da suka sa muke son gaskiya. Yin hakan zai sa mu ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu don mu sami amincewar Jehobah.