TALIFIN NAZARI NA 35
“Ku Yi Ta Gina Juna”
“Ku ƙarfafa juna, ku yi ta gina juna, kamar dai yadda kuke yi yanzu.”—1 TAS. 5:11.
WAƘA TA 90 Mu Riƙa Ƙarfafa Juna
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1. Wane aiki ne muke da shi kamar yadda 1 Tasalonikawa 5:11 ta nuna?
IKILISIYARKU ta taɓa gina Majami’ar Mulki ko ta yi mata kwaskwarima? Idan haka ne, babu shakka ka tuna taro na farko da kuka yi a Majami’ar Mulkin bayan an gama gina shi. Ka yi wa Jehobah godiya sosai. Wataƙila saboda farin ciki, har ma ba ka iya yin waƙar buɗe taron da kyau ba. Yadda muke gina Majami’un Mulkinmu da kyau yana kawo ɗaukaka ga Jehobah. Amma akwai wani aikin da muke yi da yake kawo ɗaukaka sosai ga Jehobah fiye da hakan. Wannan aikin ya ƙunshi wani abu da ya fi gini na zahiri daraja. Ya ƙunshi gina ko kuma ƙarfafa mutanen da ke zuwa waɗannan Majami’un Mulkin. Irin ginin da Manzo Bulus yake nufi ke nan sa’ad da ya rubuta abin da ke 1 Tasalonikawa 5:11, wato nassin da aka ɗauko jigon wannan talifin.—Karanta.
2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
2 Manzo Bulus ya kafa misali mai kyau na ƙarfafa ʼyan’uwansa. Ya tausaya musu. A wannan talifin, za mu tattauna yadda ya taimaka wa ʼyan’uwansa maza da mata (1) su jimre jarrabawa, (2) su zauna lafiya da juna, kuma (3) su ƙarfafa bangaskiyarsu. Bari mu ga yadda za mu iya bin misalinsa, ta wajen ƙarfafa ʼyan’uwanmu maza da mata a yau.—1 Kor. 11:1.
BULUS YA TAIMAKA WA ʼYAN’UWANSA SU JIMRE JARRABAWA
3. Ta yaya Bulus ya kasance da ra’ayi mai kyau?
3 Bulus ya ƙaunaci ʼyan’uwansa sosai. Ya taɓa shan irin wahalar da suke sha, hakan ya sa ya tausaya musu sa’ad da suke fuskantar matsaloli. Akwai lokacin da Bulus ya rasa kuɗi, kuma ya bukaci ya yi aiki don ya taimaka wa kansa da kuma abokan aikinsa. (A. M. 20:34) Shi mai aikin ɗinka tanti ne. Da farko da ya isa Korinti, ya yi aiki tare da Akila da Biriskila waɗanda su ma masu ɗinka tanti ne. Duk da haka, a “Kowace Ranar Hutu ta Mako,” yakan yi wa Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba wa’azi. Amma da Sila da Timoti suka zo, sai “Bulus ya ba da dukan lokacinsa a kan yin wa’azi.” (A. M. 18:2-5) Bulus bai manta da abin da ya fi muhimmanci a rayuwarsa ba, wato bauta wa Jehobah. Domin Bulus ya kafa misali mai kyau na yin aiki tuƙuru a wa’azi da kuma yin aiki don biyan bukatunsa, ya ƙarfafa ʼyan’uwansa. Ya ƙarfafa su kada su bar matsalolin rayuwa, da ƙoƙarin da suke yi don su tanada wa iyalinsu ya sa su bar “abin da ya fi kyau” wato ibadarsu ga Jehobah.—Filib. 1:10.
4. Ta yaya Bulus da Timoti suka taimaka wa ʼyan’uwan da ke fuskantar tsanantawa?
4 Ba da daɗewa ba bayan an kafa ikilisiyar Tasalonika, ʼyan’uwan sun fuskanci tsanantawa sosai. Taron ʼyan adawa sun yi ƙoƙarin kama Bulus da Sila, amma ba su same su ba. Sai suka kama “waɗansu masu bi, suka kai su har gaban masu shari’a, suna ihu suna cewa, ‘Mutanen nan . . . suna karya dokokin Kaisar.’ ” (A. M. 17:6, 7) Ka yi tunanin irin tsoron da sabbin Kiristocin nan suka ji sa’ad da mutanen birnin suka auko musu. Da hakan ya sa sun yi sanyin gwiwa a ibadarsu ga Jehobah, amma Bulus ba ya son hakan ya faru. Ko da yake shi da Sila sun bar birnin, Bulus ya tabbata cewa ikilisiyar ta ci gaba da samun kulawa. Bulus ya tuna wa ʼyan’uwan cewa: “Mun aiki Timoti ɗan’uwanmu . . . , ya kafa ku, ya kuma ƙarfafa ku cikin bangaskiyarku, domin kada tsananin nan ya sa wani ya fid da zuciya.” (1 Tas. 3:2, 3) Da alama Timoti ma ya fuskanci tsanantawa a garinsu, wato Listira. Ya ga yadda Bulus ya ƙarfafa ʼyan’uwa a wurin. Da yake ya ga yadda Jehobah ya taimaka wa ʼyan’uwa a Listira, Timoti ya tabbatar wa ʼyan’uwan da ke Tasalonika cewa su ma Jehobah zai taimaka musu.—A. M. 14:8, 19-22; Ibran. 12:2.
5. Ta yaya Bryant ya amfana daga taimakon wani dattijo?
5 Ta wace hanya ce kuma Bulus ya ƙarfafa ʼyan’uwansa? Sa’ad da Bulus da Barnaba suka sake ziyartar Listira da Ikoniya da kuma Antakiya, sun “zaɓa musu dattawa a kowace” ikilisiya. (A. M. 14:21-23) Hakika waɗannan ʼyan’uwa da aka naɗa, sun ƙarfafa ikilisiyoyin kamar yadda dattawa suke yi a yau. Ka yi la’akari da abin da wani ɗan’uwa mai suna Bryant ya faɗa, ya ce: “A lokacin da na kai shekara 15, mahaifina ya bar gida, mahaifiyata kuma aka yi mata yankan zumunci. Hakan ya sa na ji kamar sun yashe ni.” Mene ne ya taimaka wa Bryant ya jimre wannan mawuyacin lokaci? Ya ce: “Wani dattijo mai suna Tony yakan tattauna da ni a taro da kuma a wasu lokuta, yakan faɗa mini game da waɗanda suka fuskanci matsaloli amma duk da haka sun yi farin ciki. Ya karanta mini Zabura 27:10. Ƙari ga haka, yakan gaya mini game da Hezekiya, wanda ya bauta wa Jehobah da aminci duk da cewa mahaifinsa bai yi hakan ba.” Ta yaya hakan ya taimaka wa Bryant? Ya ce: “Ƙarfafa da Tony ya yi mini ya taimaka mini in soma hidima ta cikakken lokaci, kuma ina jin daɗin hakan sosai.” Dattawa, ku kasance a shirye kullum, don ku taimaka ma waɗanda suke bukatar “kalmar ƙarfafawa” kamar Bryant.—K. Mag. 12:25.
6. Ta yaya Bulus ya yi amfani da labarai don ya ƙarfafa ʼyan’uwa?
6 Bulus ya tuna wa ʼyan’uwa cewa akwai “taron shaidu masu yawa” da suka jimre matsaloli da taimakon Jehobah. (Ibran. 12:1) Bulus ya san cewa labaran waɗanda suka iya jimre matsaloli a dā zai iya ba ʼyan’uwansa masu bi ƙarfin zuciya kuma ya taimaka musu su mai da hankali ga “birnin Allah Mai Rai.” (Ibran. 12:22) Abin da yake faruwa a yau ma ke nan. Hakika labarin Gidiyon da Barak da Sama’ila da kuma masu aminci da yawa yana ƙarfafa duk waɗanda suka karanta su. (Ibran. 11:32-35) Haka ma yake da misalin bayin Allah da yawa masu aminci a yau. A hedkwatarmu, muna yawan samun wasiƙu daga ʼyan’uwa maza da mata da suka sami ƙarfafa daga karanta labarin wani bawan Jehobah mai aminci a zamaninmu.
BULUS YA NUNA WA ʼYAN’UWANSA YADDA ZA SU YI ZAMAN LAFIYA
7. Me ka koya daga gargaɗin da Bulus ya bayar a Romawa 14:19-21?
7 Za mu ƙarfafa ʼyan’uwanmu idan muna faɗa da kuma yin abin da zai kawo zaman lafiya a ikilisiya. Ba za mu bar bambancin ra’ayi ya raba kanmu ba. Ba ma nacewa a kan ra’ayinmu idan ba a taka ƙa’idar Littafi Mai Tsarki ba. Ka yi la’akari da wannan misalin. A ikilisiyar Roma, akwai Yahudawa da waɗanda ba Yahudawa ba. Bayan da aka kawar da Dokar Musa, bayin Jehobah ba su bukaci su bi dokar da ke hana cin wasu irin abinci ba. (Mar. 7:19) Tun daga lokacin, wasu Kiristoci Yahudawa sun fara cin kowane irin abinci. Amma wasu Kiristoci Yahudawa kuma sun ɗauka cewa bai dace a yi hakan ba. Hakan ya raba kan ikilisiyar. Bulus ya nanata muhimmancin zaman lafiya, kuma ya ce musu: “Ya fi kyau kada ka ci nama, ko ka sha ruwan inabi, ko ka aikata kowane irin abu idan zai sa ɗan’uwanka ya faɗi.” (Karanta Romawa 14:19-21.) Bulus ya taimaka musu su gane cewa irin wannan gardamar tana yin mummunan tasiri a kan ʼyan’uwa a ikilisiya. Shi ma ya kasance a shirye ya canja salon rayuwarsa don kada ya sa wasu su yi tuntuɓe. (1 Kor. 9:19-22) Haka ma, za mu iya ƙarfafa ʼyan’uwa kuma mu sa ikilisiya ta zauna lafiya idan ba ma nacewa a kan ra’ayinmu.
8. Mene ne Bulus ya yi sa’ad da wani batu mai muhimmanci ya so ya raba kan ikilisiya?
8 Bulus ya kafa misali mai kyau na zaman lafiya da waɗanda suke da bambancin ra’ayi da shi a kan wasu muhimman batutuwa. Alal misali, wasu Kiristoci a ƙarni na farko sun nace cewa dole ne Kiristocin da ba Yahudawa ba su yi kaciya. Wataƙila sun faɗi hakan ne domin suna tsoro kada Yahudawa su tsananta musu. (Gal. 6:12) Bulus bai amince da ra’ayinsu ba, amma maimakon ya nace su bi na shi ra’ayin, ya nuna sauƙin kai kuma ya nemi shawarar manzanni da kuma dattawa da ke Urushalima. (A. M. 15:1, 2) A sakamakon haka, halinsa ya taimaka ma waɗannan Kiristoci su ci gaba da farin ciki kuma su yi zaman lafiya a ikilisiya.—A. M. 15:30, 31.
9. Ta yaya za mu bi misalin Bulus?
9 Idan aka sami bambancin ra’ayi game da wani batu mai muhimmanci, zai dace mu nemi shawarar waɗanda aka naɗa su su kula da ikilisiya. Hakan zai sa a sami zaman lafiya a ikilisiya. Alal misali, za mu iya samun shawarwari daga littattafai da ƙungiyar Jehobah ta wallafa. Idan muka bi waɗannan umurnan maimakon nacewa a kan ra’ayinmu, za mu sa a yi zaman lafiya a ikilisiya.
10. Mene ne kuma Bulus ya yi don ya sa ʼyan’uwa a ikilisiya su daɗa zauna lafiya da juna?
10 Bulus ya sa zaman lafiya ta daɗa kasancewa a ikilisiya ta wajen mai da hankali ga halayen ʼyan’uwansa masu kyau. Alal misali, da ya kusan kammala wasiƙarsa ga Romawa, Bulus ya ambata sunayen ʼyan’uwa da yawa, kuma a yawancin lokuta ya faɗi abubuwa masu kyau game da su. Za mu iya bin misalin Bulus ta wajen ambata halayen ʼyan’uwanmu masu kyau ga wasu. Hakan zai sa su daɗa kusantar juna kuma su ƙaunaci juna.
11. Ta yaya za mu sa a yi zaman lafiya idan aka sami saɓani?
11 A wasu lokuta, har Kiristocin da suka manyanta ma za su iya samun saɓani tsakaninsu. Abin da ya faru da Bulus da abokinsa Barnaba ke nan. Ɗaya ya ce Markus ya sake bin su yin wa’azi a ƙasar waje amma ɗayan bai yarda ba. “Rashin yardar ya yi zafi har ya kai su ga rabuwa.” (A. M. 15:37-39) Amma Bulus da Barnaba da Markus sun sasanta, kuma abin da suka yi ya nuna cewa suna son salama da haɗin kai su ci gaba da kasancewa a ikilisiya. Daga baya, Bulus ya faɗi abubuwa masu kyau game da Barnaba da Markus. (1 Kor. 9:6; Kol. 4:10) Mu ma muna bukatar mu sasanta duk wani saɓani da ke tsakaninmu da ʼyan’uwa a ikilisiya kuma mu ci gaba da mai da hankali ga halayensu masu kyau. Ta yin hakan, za mu sa a daɗa kasancewa da salama da haɗin kai a ikilisiya.—Afis. 4:3.
BULUS YA ƘARFAFA BANGASKIYAR ʼYAN’UWANSA
12. Waɗanne matsaloli ne ʼyan’uwa suke fuskanta a yau?
12 Za mu ƙarfafa ʼyan’uwanmu idan muna taimaka musu su daɗa kasancewa da bangaskiya. Iyalan ʼyan’uwanmu da ba Shaidu ba, ko abokan aikinsu ko kuma ʼyan makarantarsu za su iya yi musu ba’a domin imaninsu. Wasu suna fama da rashin lafiya mai tsanani ko suna ƙoƙari su daina fushi domin laifin da aka yi musu. Wasu kuma sun yi shekaru da yawa da yin baftisma kuma suna jiran wannan zamanin ya ƙare. Irin waɗannan yanayoyin za su iya gwada bangaskiyar Kiristoci a yau. Kiristoci a ƙarni na farko ma sun fuskanci irin wannan yanayin. Mene ne Bulus ya yi don ya ƙarfafa ʼyan’uwansa?
13. Ta yaya Bulus ya taimaka ma waɗanda aka yi musu ba’a don imaninsu?
13 Bulus ya yi amfani da Littafi Mai Tsarki don ya ƙarfafa ʼyan’uwansa. Alal misali, mai yiwuwa iyalan Yahudawa da suka zama Kiristoci sukan gaya musu cewa addinin Yahudanci ya fi Kiristanci, kuma wataƙila Kiristocin ba su san yadda za su mayar da martani ga iyalansu ba. Hakika saƙon da Bulus ya tura wa Ibraniyawa ya ƙarfafa waɗannan Kiristocin sosai. (Ibran. 1:5, 6; 2:2, 3; 9:24, 25) Za su iya yin amfani da hujjoji masu kyau da ya bayar don su san abin da za su faɗa. A yau, za mu iya koya wa ʼyan’uwanmu yadda za su yi amfani da littattafan da ƙungiyar Jehobah ke wallafawa don su san yadda za su mai da martani ga waɗanda suke musu ba’a. Kuma idan ana yi wa ʼyan’uwanmu matasa ba’a domin ba sa yin wasu bukukuwa kamar bikin ranar haifuwa, za mu iya taimaka musu su sami bayanai a littafin nan Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!, darasi na 44 don su bayyana dalilin da ya sa ba sa yin bukukuwan.
14. Duk da cewa Bulus ya shagala da yin wa’azi da kuma koyarwa, mene ne ya yi?
14 Bulus ya ƙarfafa ʼyan’uwansa su riƙa nuna ƙauna ta wajen “aikin nagarta.” (Ibran. 10:24) Ya taimaka wa ʼyan’uwansa ta wajen furucinsa da kuma ayyukansa. Alal misali, a lokacin da aka yi yunwa a Yahudiya, Bulus ya taimaka da rarraba kayan agaji ga ʼyan’uwansa masu bi a wurin. (A. M. 11:27-30) Duk da cewa Bulus ya shagala da yin wa’azi da kuma koyarwa, ya nemi hanyoyin taimaka ma waɗanda suke da bukata. (Gal. 2:10) Ta yin hakan, ya taimaka wa ʼyan’uwansa su kasance da ƙarfin gwiwa cewa Jehobah zai kula da su. A yau ma, idan muka yi amfani da ƙarfinmu da lokacinmu da kuma ƙwarewarmu don taimaka wa ʼyan’uwanmu da suke bukatar agaji, za mu ƙarfafa bangaskiyarsu. Ƙari ga haka, za mu iya ƙarfafa ʼyan’uwanmu ta wajen ba da gudummawa don ayyukan da muke yi a faɗin duniya. Ta hakan da kuma wasu hanyoyi, muna nuna wa ʼyan’uwanmu cewa Jehobah ba zai taɓa yasar da su ba.
15-16. Ta yaya za mu taimaka ma waɗanda suka yi sanyin gwiwa?
15 Bulus bai fid da rai a kan waɗanda suka yi sanyin gwiwa ba. Ya nuna cewa yana tausaya musu kuma ya yi musu magana a hanyar da za ta ƙarfafa su. (Ibran. 6:9; 10:39) Alal misali, a wasiƙarsa ga Ibraniyawa, ya yi amfani da kalmar nan “mu” kuma hakan ya nuna cewa ya san shi ma yana bukatar ya bi shawarar da ya bayar. (Ibran. 2:1, 3) Kamar Bulus, ba za mu fid da rai a kan waɗanda suka yi sanyin gwiwa ba. Maimakon haka, za mu yi ƙoƙari mu ƙarfafa su ta wajen nuna cewa mun damu da su. Ta yin hakan, za mu nuna musu cewa muna ƙaunar su. Ƙari ga haka, yadda muke yi wa ʼyan’uwanmu magana zai iya ƙarfafa su.
16 Bulus ya tabbatar wa ʼyan’uwansa cewa Jehobah yana lura da ayyukansu masu kyau. (Ibran. 10:32-34) Mu ma za mu iya yin hakan sa’ad da muke ƙoƙarin taimaka wa ɗan’uwan da ya yi sanyin gwiwa. Za mu iya tambayarsa ya gaya mana yadda ya koyi gaskiya, kuma mu ƙarfafa shi ya yi tunanin yadda Jehobah ya taimaka masa a dā. Za mu iya yin amfani da wannan damar don mu tabbatar masa cewa Jehobah ba zai taɓa manta da ayyukansa masu kyau da ya yi a dā ba, kuma ba zai taɓa yasar da shi ba. (Ibran. 6:10; 13:5, 6) Irin wannan tattaunawar tana iya ƙarfafa ʼyan’uwan da suka yi sanyin gwiwa su ci gaba da bauta wa Jehobah.
KU CI GABA DA “ƘARFAFA JUNA”
17. Mene ne ya kamata mu ƙware a yin sa?
17 Kamar yadda magini zai daɗa ƙwarewa yayin da yake aiki, idan muna ƙarfafa juna a kai a kai za mu ƙware a yin hakan. Za mu iya taimaka wa ʼyan’uwanmu su jimre matsaloli idan muna gaya musu labaran ʼyan’uwa da suka jimre a dā. Za mu iya sa ikilisiya ta daɗa kasancewa da salama idan muna ambata halaye masu kyau na ʼyan’uwanmu, muna guje wa yin ko faɗin abin da zai sa a sami tashin hankali, kuma idan aka sami saɓani, muna ƙoƙari don mu sasanta matsalar. Kuma za mu iya ci gaba da ƙarfafa bangaskiyar ʼyan’uwanmu ta wajen tuna musu muhimman koyarwar Littafi Mai Tsarki, ta wajen ba su abubuwan biyan bukata da kuma ƙarfafa waɗanda suka yi sanyin gwiwa.
18. Mene ne ka ƙuduri niyyar yi?
18 Waɗanda suke aikin gina wuraren ibadarmu suna farin ciki kuma suna samun gamsuwa. Za mu iya yin farin ciki kamar su kuma mu sami gamsuwa idan muna gina bangaskiyar ʼyan’uwanmu. Idan aka yi gini, zai iya lalacewa. Amma idan muka gina bangaskiyar ʼyan’uwanmu, bangaskiyar za ta iya kasancewa har abada! Bari mu ƙuduri niyyar “ƙarfafa juna” da kuma “gina juna.”—1 Tas. 5:11.
WAƘA TA 100 Mu Riƙa Marabtar Baƙi
a Rayuwa a wannan zamanin tana da wuya sosai. ʼYan’uwanmu suna fuskantar matsaloli da yawa. Za mu iya taimaka musu idan muka nemi hanyoyin ƙarfafa su. Saboda haka, a wannan talifin, za mu tattauna misalin manzo Bulus.
b BAYANI A KAN HOTUNA: Wani mahaifi yana taimaka wa ʼyarsa ta yi amfani da shawarwarin da ke littattafanmu game da yadda Kirista zai shawo kan matsin yin bikin Kirismati.
c BAYANI A KAN HOTUNA: Wasu ma’aurata sun je wani wuri a ƙasarsu don su taimaka da ba da agaji.
d BAYANI A KAN HOTUNA: Wani dattijo ya ziyarci wani ɗan’uwa da ya yi sanyin gwiwa. Ya nuna wa ɗan’uwan hotunan da suka ɗauka a Makarantar Hidima ta Majagaba da suka halarta shekaru da yawa da suka shige. Hotunan sun taimaka wa ɗan’uwan ya tuna yadda suke farin ciki a lokacin. Ɗan’uwan ya soma marmarin yadda yake farin ciki a dā. Da shigewar lokaci ya komo ikilisiya.