TALIFIN NAZARI NA 36
Bayin Jehobah Suna Son Adalci
“Masu albarka ne masu jin yunwa da ƙishin yin adalci.”—MAT. 5:6.
WAƘA TA 9 Jehobah Ne Sarkinmu!
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1. Wane jarrabawa ne Yusufu ya fuskanta, kuma mene ne ya yi?
ƊAN Yakubu mai suna Yusufu ya fuskanci wata babbar jarrabawa. Wata mata ta ce masa: “Ka kwana da ni!” Matar maigidansa Fotifar ce. Yusufu ya ƙi ya yi hakan. Wani a yau zai iya cewa, ‘Me ya sa Yusufu ya ƙi yin abin da matar ta ce masa ya yi?’ A lokacin, Fotifar ba ya nan. Ƙari ga haka, Yusufu bawa ne a gidan kuma babu shakka matar ta tsananta masa da yake ya ƙi yin abin da ta ce ya yi. Duk da haka, Yusufu ya ci gaba da ƙin yin abin da ta ce ya yi. Me ya sa? Ya ce: “Don me zan yi wannan babbar mugunta, in yi wa Allah zunubi?”—Far. 39:7-12.
2. Ta yaya Yusufu ya san cewa zina zunubi ne a idon Jehobah?
2 Ta yaya Yusufu ya san cewa zina “babbar mugunta” ce a idon Allahnsa? Bayan wajen shekaru ɗari biyu ne aka ba wa Isra’ilawa dokoki wanda ɗaya daga cikinsu ta ce “Ba za ka yi zina ba.” (Fit. 20:14) Duk da haka, Yusufu ya san Jehobah sosai kuma ya san cewa Jehobah ba zai amince da zina ba. Alal misali, Yusufu ya san cewa Jehobah ya shirya aure tsakanin namiji ɗaya da mace ɗaya ne. Ƙari ga haka, ba mamaki ya ji labarin yadda Jehobah ya kāre kakarsa Saratu har sau biyu domin kada a ci zarafinta. Haka ma, ya kāre matar Ishaku, wato Rifkatu. (Far. 2:24; 12:14-20; 20:2-7; 26:6-11) Yayin da Yusufu yake tunani a kan waɗannan labaran, ya gano abu mai kyau da marar kyau a idon Jehobah. Da yake Yusufu yana ƙaunar Jehobah, ya ƙudura cewa zai yi abin da ke da kyau a idon Jehobah.
3. Me za mu tattauna a wannan talifin?
3 Shin kana son adalci? Ba shakka kana so. Amma dukanmu ajizai ne, kuma idan ba mu yi hankali ba ra’ayin mutanen duniya game da abu mai kyau da marasa kyau zai iya shafan mu. (Isha. 5:20; Rom. 12:2) Don haka, za mu tattauna abin da adalci yake nufi da kuma yadda muke amfana idan muka yi adalci. Sa’an nan za mu tattauna abubuwa uku da za mu iya yi don mu daɗa son ƙa’idodin Jehobah na adalci.
ME ADALCI YAKE NUFI?
4. Wane ra’ayi da bai dace ba ne mutane da yawa suke da shi game da yin adalci?
4 Shugabannin addinai a zamanin Yesu sun ɗauka cewa suna yin abin da ya dace, amma Yesu ya yi tir da su domin suna shari’anta mutane kuma suna kafa nasu ƙa’idodi game da abu mai kyau da marar kyau. (M. Wa. 7:16; Luk. 16:15) Wasu mutane a zamaninmu suna yin hakan. A ganinsu, suna yin abin da ya dace, amma suna bin nasu ƙa’idodin ne game da abu mai kyau da marar kyau. A yawancin lokuta suna nuna girman kai, suna shari’anta wasu kuma suna ɗauka cewa sun fi wasu. Irin halayen nan ba sa faranta ma Jehobah rai, kuma ba su da alaƙa da yin adalci.
5. Me adalci yake nufi bisa ga Littafi Mai Tsarki? Ka ba da misalia.
5 Adalci hali ne mai kyau sosai. A taƙaice, adalci yana nufin yin abin da ya dace a idon Jehobah Allahnmu. A Littafi Mai Tsarki, kalmar da aka fassara zuwa “adalci” tana nufin yin rayuwa bisa ga ƙa’idodin Jehobah. Alal misali, Jehobah ya ba wa Isra’ilawa doka cewa ’yan kasuwa su yi amfani da “ma’auni na gaske.” (M. Sha. 25:15) Kalmar Ibrananci da aka fassara zuwa “gaske” tana iya nufin “adalci.” Don haka, idan Kirista yana so ya zama mai adalci a idon Jehobah, dole ne ya yi gaskiya a dukan harkokin kasuwancinsa. Mutum mai adalci ba ya jin daɗi idan ya ga an cuci wani. Kuma mutum mai adalci da yake so ya faranta ma Jehobah rai yakan yi tunani a kan yadda Jehobah zai ɗauki shawarwari da yake yankewa.—Kol. 1:10.
6. Me ya sa za mu iya gaskata cewa ƙa’idodin Jehobah game da abin da ya dace da abin da bai dace ba daidai ne? (Ishaya 55:8, 9)
6 Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah ne tushen adalci. Hakan ne ya sa ana kiran sa “mazaunin adalci.” (Irm. 50:7) Da yake Jehobah ne Mahalicci, shi ne kaɗai ya isa ya gaya mana abin da ya dace da abin da bai dace ba. Da yake mu ajizai ne, ba za mu iya sanin abin da ya dace da abin da bai dace ba, amma da yake Jehobah ba ajizi ba ne, ya san abin da ya dace da abin da bai dace. (K. Mag. 14:12; karanta Ishaya 55:8, 9.) Tun da yake an halicce mu a kamannin Allah, za mu iya yin rayuwa bisa ƙa’idodinsa na adalci. (Far. 1:27) Kuma muna jin daɗin yin hakan. Yadda muke ƙaunar Jehobah yana motsa mu mu yi koyi da shi iya gwargwadon ƙarfinmu.—Afis. 5:1.
7. Me ya sa muke bukatar ƙa’idodi masu kyau da aka amince da su? Ka ba da misali.
7 Muna amfana daga bin ƙa’idodin Jehobah game da abin da ya dace da abin da bai dace ba. Ta yaya? Ka yi tunanin abin da zai faru in a ce kowane banki yana da nasa tsari na sanin darajar kuɗi? Hakan zai jawo matsaloli sosai. Kuma idan ma’aikatan kiwon lafiya ba sa bin tsari na kula da marasa lafiya, hakan zai iya sa wasu marasa lafiya su rasa rayukansu. Babu shakka, kasancewa da tsarin da kowa ya amince da shi zai iya kāre mutane. Haka ma, ƙa’idodin Jehobah game da abin da ya dace da abin da bai dace ba suna kāre mu.
8. Wane albarka ne waɗanda suke son adalci za su samu?
8 Jehobah yana yi ma waɗanda suke yin rayuwa bisa ƙa’idodinsa albarka. Ya yi alkawari cewa: “Masu adalci za su gāji ƙasar, su zauna a ciki har abada.” (Zab. 37:29) Ka yi tunanin yadda ’yan Adam za su kasance da haɗin kai da farin ciki da kuma salama idan kowa da kowa yana bin ƙa’idodin Jehobah. Irin rayuwar da Jehobah yake so ka mora ke nan. Babu shakka dukanmu muna da dalilai masu kyau na son adalci! Ta yaya za mu daɗa son wannan halin? Bari mu ga abubuwa guda uku da za mu iya yi.
KA DAƊA SON ƘA’IDODIN JEHOBAH
9. Me zai taimaka mana mu so adalci?
9 Na 1: Ka ƙaunaci Wanda ya kafa ƙa’idodin. Idan muna so mu daɗa son adalci, dole ne mu ƙaunaci wanda ya kafa ƙa’idodi game da adalci. Yayin da muke daɗa ƙaunar Jehobah, haka ma za mu daɗa son ƙa’idodinsa. Alal misali, da a ce Adamu da Hauwa’u sun ƙaunaci Jehobah, da ba su taka dokokinsa ba.—Far. 3:1-6, 16-19.
10. Ta yaya Ibrahim ya daɗa fahimtar yadda Jehobah yake tunani?
10 Hakika, ba ma so mu yi irin kuskuren da Adamu da Hauwa’u suka yi a lambun Adnin. Za mu iya guje ma hakan idan mun ci gaba da koya game da Jehobah, muka ci gaba da son halayensa kuma muka ƙoƙarta mu san yadda yake tunani. Hakan zai sa mu daɗa ƙaunar Jehobah. Ka yi la’akari da misalin Ibrahim. Akwai lokacin da Ibrahim bai fahimci dalilin da ya sa Jehobah ya ɗauki wani mataki ba. Amma duk da hakan, bai yi ma Jehobah rashin biyayya ba. A maimakon haka, ya yi ƙoƙari ya daɗa sanin Jehobah. Alal misali, sa’ad da ya ji cewa Jehobah ya yanke shawarar hallaka Sodom da Gomora, da farko, Ibrahim ya ɗauka cewa “mai shari’ar dukan duniya” zai hallaka masu adalci tare da marasa adalci. A ganin Ibrahim hakan bai dace ba, sai ya yi wa Jehobah tambayoyi. Jehobah ya amsa masa ba tare da ɓata rai ba. A ƙarshe, Ibrahim ya gano cewa Jehobah yana bincika zuciyar kowane ɗan Adam, kuma ba zai taɓa hukunta masu adalci tare da marasa adalci ba.—Far. 18:20-32.
11. Ta yaya Ibrahim ya nuna cewa yana ƙaunar Jehobah kuma ya dogara gare shi?
11 Tattaunawar da Jehobah ya yi da Ibrahim game da biranen Sodom da Gomora sun shafe shi sosai. Babu shakka hakan ya sa ya daɗa ƙaunar Ubansa na sama. Bayan wasu shekaru, wani abu ya faru da ya gwada yadda Ibrahim ya dogara ga Jehobah. Jehobah ya gaya masa ya yi hadaya da ɗansa Ishaku. Amma a wannan karon, Ibrahim ya riga ya san Allahnsa sosai. Don haka, bai yi masa tambayoyi ba. Nan tāke, Ibrahim ya soma shirin yin abin da Jehobah ya ce masa ya yi. Duk da haka, ka yi tunanin baƙin cikin da Ibrahim ya yi sa’ad da yake tunanin yin abin da Jehobah ya ce masa ya yi! Ba shakka, Ibrahim ya yi tunanin abubuwa da ya koya game da Jehobah. Ya san cewa Jehobah ba zai taɓa yin rashin adalci ko kuma mugunta ba. Manzo Bulus ya ce Ibrahim ya yi tunanin cewa Jehobah zai iya tā da ɗansa Ishaku daga mutuwa. (Ibran. 11:17-19) A lokacin, Jehobah ya riga ya yi alkawari cewa Ishaku zai zama baban al’umma, kuma a lokacin Ishaku bai haifi yara ba tukun. Ibrahim ya ƙaunaci Jehobah, don haka ya ba da gaskiya cewa Jehobah zai yi adalci. Bangaskiyarsa ta sa ya yi biyayya duk da cewa hakan bai yi masa sauƙi ba.—Far. 22:1-12.
12. Ta yaya za mu yi koyi da Ibrahim? (Zabura 73:28)
12 Ta yaya za mu yi koyi da Ibrahim? Mu ma muna bukatar mu ci gaba da koya game da Jehobah. Yayin da muke yin hakan, za mu yi kusa da shi kuma za mu daɗa ƙaunarsa. (Karanta Zabura 73:28.) Hakan zai horar da zuciyarmu kuma za mu soma tunani yadda Jehobah yake yi. (Ibran. 5:14) A sakamakon haka, idan wani yana so ya sa mu yi abin da bai dace ba, za mu guji yin hakan. Ba za mu ma yi tunanin yin abin da zai ɓata ma Jehobah rai ko ya ɓata dangantakarmu da shi ba. A wace hanya ce kuma za mu nuna cewa muna son adalci?
13. Me zai taimake mu mu ci gaba da yin adalci? (Karin Magana 15:9)
13 Na 2: Ka yi ƙoƙari ka ci gaba da son adalci. Idan muna so mu ƙara ƙarfin jikinmu, dole ne mu yi ƙoƙari mu riƙa motsa jiki. Haka ma, muna bukatar mu yi ƙoƙari sosai don mu daɗa son ƙa’idodin Jehobah. Hakan abu ne da za mu iya yi. Jehobah ya san iya ƙarfinmu, kuma ba zai taɓa ce mu yi abin da ya fi ƙarfinmu ba. (Zab. 103:14) Ya gaya mana cewa ‘duk wanda ya nemi adalci . . . zai sami . . . adalci.’ (Karanta Karin Magana 21:21.) Idan akwai maƙasudin da muke so mu cim ma a hidimarmu ga Jehobah, muna yin iya ƙoƙarinmu don mu cim ma hakan. Jehobah zai taimaka mana mu daɗa son adalci kuma mu ci gaba da yin hakan.—Zab. 84:5, 7.
14. Mene ne rigar ƙarfe ta adalci, kuma me ya sa muke bukatar sa?
14 Jehobah yana nuna mana ƙauna ta wajen tuna mana cewa yin adalci bai fi ƙarfinmu ba. (1 Yoh. 5:3) A maimakon haka, yin adalci yana kāre mu kuma muna bukatar hakan a kullum. Ka tuna kayan kāriya na yaƙi da manzo Bulus ya yi magana a kai. (Afis. 6:14-18) Wanne ne daga cikinsu yake kāre zuciyar Kirista? Ita ce rigar ƙarfe ta adalci, kuma tana wakiltar ƙa’idodin Jehobah game da abu mai kyau da marar kyau. Kamar yadda rigar ƙarfe take kāre zuciya, haka ma ƙa’idodin Jehobah game da abu mai kyau da marar kyau za su kāre sha’awoyinmu da kuma tunaninmu zuciyarmu. Shi ya sa yake da muhimmanci mu tabbata cewa kayan kāriyarmu na yaƙi sun ƙunshi rigar ƙarfe ta adalci.—K. Mag. 4:23.
15. Ta yaya za ka iya saka rigar ƙarfe ta adalci?
15 Ta yaya za ka saka rigar ƙarfe ta adalci? Za ka iya yin hakan ta wajen bin ƙa’idodin Jehobah a shawarwarin da kake yankewa kullum. Kafin ka yi magana, ko ka kalli wani bidiyo, ko kuma ka karanta wani littafi, zai dace ka tambayi kanka: ‘Yaya hakan zai shafe ni? Shin Jehobah zai amince da hakan? Ya ƙunshi lalata ko faɗa ko haɗama ko son kai, wato abubuwan da Jehobah ba ya so?’ (Filib. 4:8) Idan shawarar da ka yanke ta jitu da ƙa’idodin Jehobah, hakan zai nuna cewa kana barin ƙa’idodinsa su kāre zuciyarka.
16-17. Ta yaya Ishaya 48:18 ta tabbatar mana da cewa za mu iya ci gaba da bin ƙa’idodin Jehobah?
16 Shin kana tsoron cewa ba zai yiwu ka ci gaba da bin ƙa’idodin Jehobah a kullum ba? Ka yi la’akari da kwatanci da Jehobah ya yi amfani da shi a Ishaya 48:18. (Karanta.) Jehobah ya yi mana alkawari cewa adalcinmu zai iya zama kamar “raƙuman ruwan teku.” Ka yi tunanin wannan, a ce kana tsaye a bakin teku kuma kana ganin yadda raƙuman ruwa suke ɓullowa ɗaya bayan ɗaya babu iyaka. Shin za ka yi tunani cewa rana ɗaya raƙuman ruwan za su daina ɓullowa? A’a! Ka san cewa raƙuman ruwan sun yi shekaru dubbai suna fitowa a tekun, kuma babu abin da zai hana su ɓullowa.
17 Adalcinka zai iya zama kamar raƙuman ruwa! Ta yaya? Kafin ka yanke wata shawara, ka yi tunani a kan abin da Jehobah yake so ka yi kuma ka yi shi. Ko da yanke shawarar ya yi maka wuya, Ubanka na sama yana tare da kai kuma zai ba ka ƙarfi da kake bukata domin ka ci gaba da yin abin da ke da kyau.—Isha. 40:29-31.
18. Me ya sa zai dace mu guji shari’anta wasu bisa namu ƙa’idodi?
18 Na 3: Ka bar Jehobah ya yi shari’ar. Yayin da muke ƙoƙari mu yi rayuwa bisa ga ƙa’idodin Jehobah, dole ne mu guji shari’anta wasu da kuma nuna kamar mun fi wasu. Maimakon mu riƙa shari’anta wasu bisa namu ƙa’idodi, zai dace mu tuna cewa Jehobah ne “mai shari’ar dukan duniya.” (Far. 18:25) Jehobah bai ba mu ikon shari’anta wasu ba. Ban da haka, Yesu ya umurce mu cewa: “Kada ku yanke wa kowa hukunci, domin kada a yanke muku.”—Mat. 7:1.b
19. Ta yaya Yusufu ya nuna cewa ya yarda da hukuncin Jehobah?
19 Bari mu sake yin la’akari da misalin mutumin nan mai adalci, wato Yusufu. Ya guji shari’anta mutane har ma da waɗanda suka yi masa mugunta. ’Yan’uwansa sun ci zalinsa, sun sayar da shi a matsayin bawa, kuma suka ruɗi babansu cewa ya mutu. Shekaru da yawa bayan haka, Yusufu ya sake haɗuwa da iyalinsa. A lokacin ya riga ya zama mai iko a ƙasar, kuma da ya so da ya rama abin da suka yi masa ta wajen yanke musu hukunci mai tsanani. ’Yan’uwan Yusufu sun ji tsoro domin sun ɗauka cewa abin da zai yi ke nan duk da cewa sun tuba da gaske. Amma Yusufu ya ce musu: “Kada ku ji tsoro! Ni Allah ne?” (Far. 37:18-20, 27, 28, 31-35; 50:15-21) Yusufu ya nuna sauƙin kai ta wajen barin Jehobah ya yi musu shari’a.
20-21. Ta yaya za mu guji nuna cewa mu muka fi adalci?
20 Mu ma muna barin Jehobah ya yi mana shari’a kamar yadda Yusufu ya yi. Ba za mu ce mun san dalilin da ya sa ’yan’uwanmu suka yi wasu abubuwa ba. Ba za mu iya sanin abin da ke zuciyarsu ba, domin Jehobah ne kaɗai ‘mai auna nufin zuciya.’ (K. Mag. 16:2) Yana ƙaunar mutane daga kowace irin al’ada da kuma al’umma. Kuma Jehobah ya ƙarfafa mu mu riƙa nuna ƙauna. (2 Kor. 6:13) Ya kamata mu ƙaunaci dukan ’yan’uwanmu, maimakon mu shari’anta su.
21 Ko waɗanda ba Shaidu ba ma bai kamata mu shari’anta su ba. (1 Tim. 2:3, 4) Shin zai dace ka ɗauka cewa wani danginka da ba ya bauta ma Jehobah ba zai taɓa yin hakan ba? Babu. Idan ka yi hakan, ka wuce gona da iri ke nan, kuma kana nuna cewa kai ka fi adalci. Har yanzu, Jehobah yana ba wa “dukan mutane a ko’ina” zarafin tuba. (A. M. 17:30) A kullum, ka tuna cewa nuna kamar kai ne ka fi adalci shi ma rashin adalci ne.
22. Me ya sa ka ƙudiri niyyar son adalci?
22 Fatanmu shi ne yadda muke son ƙa’idodin Jehobah na adalci ya sa mu farin ciki, kuma ya kafa misali mai kyau wa ’yan’uwanmu don su daɗa ƙaunar mu da kuma Allah. Bari dukanmu mu ci gaba da “jin yunwa da ƙishin yin adalci.” (Mat. 5:6) Ka tabbata cewa Jehobah yana farin ciki don ƙoƙarin da kake yi ka daɗa yin abubuwan da suka dace. Ka ƙarfafa duk da cewa mutane a duniya suna ci gaba da yin rashin adalci! Ka riƙa tunawa cewa Jehobah “yana ƙaunar masu-adalci.”—Zab. 146:8, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.
WAƘA TA 139 Rayuwa a Cikin Aljanna
a Da wuya ake samun masu adalci a wannan muguwar duniya. Amma akwai miliyoyin mutane a yau da suke yin adalci. Babu shakka kana cikin su. Kana yin adalci ne domin kana ƙaunar Jehobah kuma Jehobah yana son adalci. Ta yaya za mu daɗa son adalci? Wannan talifin zai taimaka mana mu san abin da adalci yake nufi da kuma yadda za mu amfana idan muna yin sa. Za mu kuma tattauna abubuwan da za mu iya yi don mu daɗa son adalci.
b A wasu lokuta, dattawa za su bukaci su yi shari’a idan wani ya yi zunubi mai tsanani ko kuma ya tuba. (1 Kor. 5:11; 6:5; Yak. 5:14, 15) Amma ya kamata su tuna cewa ba za su iya sanin abin da ke zuciyar mutumin ba, kuma shari’ar da suke yi ta Jehobah ce. (Ka duba misalin da ke 2 Tarihi 19:6.) Zai dace su yi koyi da Jehobah ta wajen nuna sanin ya kamata da jinƙai da kuma adalci.