TALIFIN NAZARI NA 45
Yadda Jehobah Yake Taimaka Mana Mu Yi Nasara a Hidimarmu
“Za su sani cewa akwai annabi a cikinsu.”—EZEK. 2:5.
WAƘA TA 67 Mu Yi “Waꞌazin Kalmar Allah”
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1. Mene ne zai iya faruwa, kuma wane tabbaci ne za mu iya kasancewa da shi?
MUN san cewa za a iya yin adawa da mu yayin da muke yin wa’azi, kuma hakan zai iya daɗa yin muni a nan gaba. (Dan. 11:44; 2 Tim. 3:12; R. Yar. 16:21) Duk da haka, za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana. Me ya sa muka faɗi haka? A duk tarihi, Jehobah ya taimaka wa bayinsa su yi nasara a ayyukan da ya ba su ko da aikin yana da wuya. Bari mu kwatanta hakan ta wajen tattauna wasu abubuwan da suka faru da annabi Ezekiyel, wanda ya yi waꞌazi ga Yahudawa da suka yi zaman bauta a Babila.
2. Ta yaya Jehobah ya kwatanta mutanen da Ezekiyel ya yi musu waꞌazi, kuma mene ne za mu tattauna a wannan talifin? (Ezekiyel 2:3-6)
2 Waɗanne irin mutane ne aka umurci Ezekiyel ya yi musu waꞌazi? Jehobah ya kira su masu “taurin kai,” “masu taurin zuciya,” da “ꞌyan tawaye.” Suna da illa kamar ƙayoyi da kuma kunamai. Shi ya sa Jehobah ya gaya wa Ezekiyel sau da dama cewa: ‘Kada ka ji tsoro’! (Karanta Ezekiyel 2:3-6.) Ezekiyel ya iya yin nasara a hidimarsa domin (1) Jehobah ne ya aike shi, (2) ruhu mai tsarki ya ba shi ƙarfin zuciya, (3) Kalmar Allah ta ƙarfafa bangaskiyarsa. Ta yaya abubuwa ukun nan sun taimaka ma Ezekiyel? Kuma ta yaya suke taimaka mana a yau?
JEHOBAH NE YA AIKI EZEKIYEL
3. Waɗanne kalmomi ne da alama sun ƙarfafa Ezekiyel, kuma ta yaya Jehobah ya tabbatar masa cewa zai taimaka masa?
3 Jehobah ya gaya wa Ezekiyel cewa: “Na aike ka.” (Ezek. 2:3, 4) Hakika kalmomin nan sun ƙarfafa Ezekiyel. Me ya sa muka faɗi hakan? Babu shakka ya tuna cewa a lokacin da Jehobah ya naɗa Musa da Ishaya a matsayin annabawansa, Jehobah ya yi amfani da kalmomi kamar haka. (Fit. 3:10; Isha. 6:8) Ezekiyel ya kuma san yadda Jehobah ya taimaka ma annabawan nan guda biyu su iya yin nasara a aiki mai wuya da ya ba su. Saꞌad da Jehobah ya gaya wa Ezekiyel sau biyu cewa: “Na aike ka,” hakan ya ba shi dalilin gaskata cewa Jehobah zai taimaka masa. Ƙari ga haka, Ezekiyel ya rubuta sau da dama cewa: “Yahweh ya yi magana da ni ya ce.” (Ezek. 3:16; Ezek. 6:1) Babu shakka, Ezekiyel ya kasance da tabbaci cewa Jehobah ne ya aike shi. Da yake mahaifin Ezekiyel firist ne, ba mamaki ya koya masa yadda Jehobah ya tabbatar wa annabawansa cewa zai taimaka musu a duk tarihi. Jehobah ya gaya wa Ishaku da Yakubu da kuma Irmiya cewa yana tare da su.—Far. 26:24; 28:15; Irm. 1:8.
4. Waɗanne kalmomi ne suka ƙarfafa Ezekiyel?
4 Yaya yawancin Isra’ilawa za su ɗauki saƙon Ezekiyel? Jehobah ya ce: “Gidan Isra’ila ba su da niyya su ji ka, gama ba su da niyya su ji ni.” (Ezek. 3:7) Da yake Isra’ilawan sun ƙi su ji Ezekiyel, hakan yana nufin cewa sun ƙi su ji Jehobah ne. Kalmomin nan sun nuna wa Ezekiyel cewa ko da yake mutanen sun ƙi jin sa, hakan ba ya nufin cewa bai yi nasara a waꞌazinsa ba. Jehobah ya kuma gaya wa Ezekiyel cewa sa’ad da annabcin da ya yi ya cika, mutanen “za su sani cewa akwai annabi a cikinsu.” (Ezek. 2:5; 33:33) Babu shakka kalmomin nan sun ƙarfafa Ezekiyel, kuma sun ba shi ƙarfin da yake bukata don ya yi nasara a hidimarsa.
JEHOBAH NE YA AIKE MU
5. Bisa ga Ishaya 44:8, mene ne yake ƙarfafa mu?
5 Mu ma sanin cewa Jehobah ne ya aike mu yana ƙarfafa mu. Ya daraja mu ta wajen kiran mu ꞌshaidunsa.ꞌ (Isha. 43:10) Wannan babban gata ne! Kamar yadda Jehobah ya gaya wa Ezekiyel cewa: ‘Kada ka ji tsoro,’ haka ma yana gaya mana cewa: “Kada ku ji tsoro.” Me ya sa bai kamata mu ji tsoron waɗanda suke adawa da mu ba? Kamar Ezekiyel, Jehobah ne ya aike mu kuma yana goyon bayan mu.—Karanta Ishaya 44:8.
6. (a) Ta yaya Jehobah ya tabbatar mana cewa zai taimaka mana? (b) Mene ne yake ƙarfafa mu?
6 Jehobah ya yi mana alkawari cewa zai taimaka mana. Alal misali, kafin Jehobah ya ce: “Ku ne shaiduna,” ya ce: “Saꞌad da ka bi ta ruwa mai zurfi, ina tare da kai, ko ka bi ta tsakiyar koguna, ba za su kwashe ka ba. Ko ka bi ta cikin wuta, ba za ta ƙone ka ba, harshen wuta kuma ba zai cinye ka ba.” (Isha. 43:2) Yayin da muke yin waꞌazi, a wasu lokuta, mukan fuskanci wasu ƙalubale da ke kamar ambaliyar ruwa, ko kuma matsaloli da ke kama da wuta. Duk da haka, Jehobah yana taimaka mana mu ci gaba da yin nasara a waꞌazinmu. (Isha. 41:13) Yawancin mutane a yau ba sa jin saƙonmu kamar yadda mutane suka ƙi ji a zamanin Ezekiyel. Amma hakan ba ya nufin cewa ba mu iya yin wa’azi ba. Sanin cewa Jehobah yana farin ciki yayin da muke yin iya ƙoƙarinmu mu yi wa’azi yana ƙarfafa mu. Manzo Bulus ya ce: “Kowanne zai sami ladansa bisa ga aikinsa.” (1 Kor. 3:8; 4:1, 2) Wata ꞌyarꞌuwa da ta jima tana hidimar majagaba ta ce: “Ina farin cikin sanin cewa Jehobah yana yi mana albarka domin ƙoƙarin da muka yi ne.”
RUHU MAI TSARKI YA BA WA EZEKIYEL ƘARFIN ZUCIYA DA YAKE BUKATA
7. Yaya Ezekiyel ya ji a duk lokacin da ya tuna wahayin da ya gani? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)
7 Ezekiyel ya ga yadda ruhu mai tsarki yake da iko sosai. Abin da Ezekiyel ya gani a wahayi, ya taimaka masa ya gane cewa ruhu mai tsarki yana taimaka wa malaꞌiku masu iko, kuma yana sa manyan ƙafafun karusai da ke sama su yi tafiya. (Ezek. 1:20, 21) Mene ne Ezekiyel ya yi da ya ga wahayin? Ya rubuta cewa: “Sa’ad da na gani, na fāɗi da fuskata har ƙasa.” Abin ya burge shi sosai har ya faɗi a ƙasa. (Ezek. 1:28) Daga baya, a duk lokacin da Ezekiyel ya yi tunani game da wannan wahayi, babu shakka hakan yana tabbatar masa cewa da taimakon ruhu mai tsarki, zai iya yin nasara a hidimarsa.
8-9. (a) Mene ne ya faru da Ezekiyel sa’ad da Jehobah ya umurce shi ya tashi tsaye? (b) Ta yaya Jehobah ya ƙara ƙarfafa Ezekiyel don ya iya yin hidima da aka ba shi?
8 Jehobah ya umurci Ezekiyel cewa: “Ya kai ɗan mutum, tashi tsaye, zan yi magana da kai.” Wannan umurnin da kuma “ruhu” mai tsarki ya ba Ezekiyel ƙarfin zuciya da yake bukata don ya tashi tsaye. Ezekiyel ya rubuta cewa: “Ruhu kuwa ya shigo cikina, ya tā da ni tsaye.” (Ezek. 2:1, 2) Daga baya, har ya kammala hidimarsa, hannun Yahweh, wato ruhu mai tsarki ya ci gaba da yi masa ja-goranci. (Ezek. 3:22; 8:1; 33:22; 37:1; 40:1) Ruhu mai tsarki ya ƙarfafa Ezekiyel kuma ya taimaka masa ya iya yin hidimar da aka ba shi, wato yin wa’azi ga mutane masu “taurin kai” da “taurin zuciya.” (Ezek. 3:7) Jehobah ya gaya wa Ezekiyel cewa: “Na mai da kanka mai tauri kamar nasu, zuciyarka kuma mai tauri kamar tasu. Na mai da kanka kamar baƙin dutse mai ƙarfi, har ma da tauri fiye da wannan. Kada ka ji tsoron su ko ka firgita saboda irin kallon da za su yi maka, gama su ꞌyan tawaye ne.” (Ezek. 3:8, 9) Kamar dai Jehobah yana ce wa Ezekiyel ne: ‘Kada ka bar taurin kan mutanen ya sa ka sanyin gwiwa. Zan ƙarfafa ka.’
9 Daga baya, ruhu mai tsarki ya ɗauke Ezekiyel zuwa inda zai yi wa’azi. Annabin ya rubuta cewa: “Hannun Yahweh yana kaina da ƙarfi.” Ya ɗauki annabin mako ɗaya kafin ya fahimci saƙon da kyau don ya iya bayyana wa mutanen da tabbaci. (Ezek. 3:14, 15) Sai Jehobah ya gaya masa ya je wani kwari inda ruhu ‘ya shiga cikinsa.’ (Ezek. 3:23, 24) Da hakan, Ezekiyel ya kasance a shirye ya ci gaba da hidimarsa.
RUHU MAI TSARKI YANA BA MU ƘARFIN ZUCIYA DA MUKE BUKATA
10. Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da yin waꞌazi, kuma me ya sa?
10 Me zai taimaka mana mu ci gaba da yin waꞌazi? Don mu sami amsar tambayar, bari mu tuna da abin da ya faru da Ezekiyel. Kafin ya soma yin hidimarsa, ruhu mai tsarki ya ba shi ƙarfin zuciya da yake bukata. Kamar yadda ruhu mai tsarki ya taimaka wa Ezekiyel, mu ma ruhu mai tsarki ne yake taimaka mana mu yi waꞌazi. Me ya sa muka faɗi hakan? Mun faɗi hakan ne domin Shaiɗan yana yaƙi da mu kuma niyyarsa ne ya hana mu yin waꞌazi. (R. Yar. 12:17) Mutane da yawa suna gani kamar Shaiɗan yana da iko sosai, don haka ba za mu iya yin nasara a kansa ba. Amma ta wajen waꞌazin da muke yi, muna yin nasara a kansa! (R. Yar. 12:9-11) Yayin da muke yin waꞌazi, muna nuna cewa ba ma jin tsoron barazana da Shaiɗan yake yi mana. A duk lokacin da muka yi waꞌazi, muna yin nasara a kan Shaiɗan. Tun da muna iya ci gaba da yin waꞌazi duk da adawa da ake yi mana, mene ne hakan yake nunawa? Hakan yana nuna mana cewa Jehobah yana ba mu ƙarfin zuciya ta wajen ruhu mai tsarki kuma ya amince da mu.—Mat. 5:10-12; 1 Bit. 4:14.
11. Wane taimako ne ruhu mai tsarki zai ba mu, kuma ta yaya za mu ci gaba da samun sa?
11 Wane abu ne kuma muka koya yayin da muke tunanin yadda Jehobah ya ba Ezekiyel ƙarfin zuciya da yake bukata don ya iya yin waꞌazi? Ruhu mai tsarki zai iya ba mu ƙarfin zuciya don mu iya shawo kan duk wata matsala da za mu fuskanta a waꞌazi. (2 Kor. 4:7-9) To mene ne za mu iya yi don mu ci gaba da samun ruhu mai tsarki? Muna bukatar mu ci gaba da roƙon Allah ya ba mu ruhu mai tsarki da tabbacin cewa zai amsa mana. Yesu ya koya wa almajiransa cewa: “Ku yi ta roƙo. . . . Ku yi ta nema. . . . Ku yi ta ƙwanƙwasawa.” Idan mun yi hakan, Jehobah “zai ba [mu] Ruhu Mai Tsarki.”—Luk. 11:9, 13; A. M. 1:14; 2:4.
KALMAR ALLAH TA ƘARFAFA BANGASKIYAR EZEKIYEL
12. Bisa ga Ezekiyel 2:9–3:3, daga ina ne naɗaɗɗen littafin ya fito, kuma wane saƙo ne yake cikinsa?
12 Ruhu mai tsarki ya ba wa Ezekiyel ƙarfin zuciya da yake bukata, amma bai ƙare a nan ba. Kalmar Allah ta ƙarfafa bangaskiyarsa. (Karanta Ezekiyel 2:9–3:3.) Wane ne ya ba annabin wannan naɗaɗɗen littafin? Mene ne ke cikin littafin? Kuma ta yaya saƙon ya ƙarfafa Ezekiyel? Bari mu gani. Da alama, Jehobah ya yi amfani da ɗaya daga cikin mala’iku huɗun da Ezekiyel ya gani ya miƙa masa naɗaɗɗen littafin. (Ezek. 1:8; 10:7, 20) A cikin naɗaɗɗen littafin, an rubuta hukunci da ya kamata Ezekiyel ya gaya ma Isra’ilawa masu taurin kai da aka kai su bauta. (Ezek. 2:7) An rubuta saƙon a cikin littafin gaba da baya.
13. Mene ne Jehobah ya gaya wa Ezekiyel ya yi da naɗaɗɗen littafin, kuma me ya sa yake da zaƙi?
13 Jehobah ya gaya wa annabin ya ci naɗaɗɗen littafin kuma ya ‘cika cikinsa da shi.’ Ezekiyel ya yi biyayya ga Jehobah, kuma ya cinye naɗaɗɗen littafin gabaki ɗaya. Mene ne wannan sashe na wahayin yake nufi? Ezekiyel ya bukaci ya fahimci saƙon da zai idar da kyau. Yana bukatar ya gaskata saƙon don ya iya idar da saƙon da tabbaci. Sai wani abin mamaki ya faru. Ezekiyel ya gano cewa naɗaɗɗen littafin “yana da zaƙi kamar zuma.” (Ezek. 3:3) Me ya sa? A wurin Ezekiyel, aikin da aka ba shi na zama wakilin Jehobah babban gata ne, shi ya sa littafin ya yi masa zaƙi kamar zuma. (Zab. 19:8-11) Ya yi farin ciki domin Jehobah ya naɗa shi ya zama annabinsa.
14. Mene ne ya taimaka ma Ezekiyel ya kasance a shirye ya yi hidimar da aka ba shi?
14 Daga baya, Jehobah ya gaya wa Ezekiyel cewa: “Dukan maganata wanda nake faɗa maka, ka kasa kunne ka kuma karɓa a zuciyarka.” (Ezek. 3:10) Da wannan umurnin, Jehobah ya gaya wa Ezekiyel ya yi ƙoƙari ya tuna kalmomin da aka rubuta a cikin naɗaɗɗen littafin kuma ya yi bimbini a kansu. Da Ezekiyel ya yi hakan, bangaskiyarsa ta daɗa ƙarfi, kuma ya sami saƙo mai tsanani da zai idar wa mutanen Israꞌila. (Ezek. 3:11) Saꞌad da Ezekiyel ya fahimci saƙon Allah da kyau kuma ya gaskata da saƙon, ya kasance a shirye ya yi waꞌazi kuma ya ci gaba da yin hakan har sai da ya kammala hidimarsa.—Zab. 19:14.
KALMAR ALLAH TANA ƘARFAFA BANGASKIYARMU
15. Mene ne muke bukatar mu “kasa kunne” a kai don mu iya jimre?
15 Idan muna so mu iya ci gaba da yin hidimarmu, dole ne mu bar Kalmar Allah ta ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarmu. Muna bukatar mu “kasa kunne” ga dukan abubuwan da Allah yake gaya mana. A yau, Allah yana ba mu umurni ta wajen Kalmarsa Littafi Mai Tsarki. Ta yaya za mu tabbata cewa Kalmar Allah tana shafan yadda muke tunani da yadda muke ji da kuma abubuwan da muke yi?
16. Mene ne ya kamata mu yi da Kalmar Allah, kuma ta yaya za mu fahimce ta da kyau?
16 Kamar yadda cin abinci yake sa mu sami ƙarfin jiki, haka ma yin nazarin Kalmar Allah da yin tunani a kan abin da muka karanta yana ƙarfafa bangaskiyarmu. Darasin da Jehobah yake so mu koya ke nan. Idan ya zo ga Kalmar Allah, Jehobah yana so mu ‘cika cikinmu da shi,’ wato mu fahimce ta da kyau. Za mu iya yin hakan ta wajen yin adduꞌa da karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin bimbini. Da farko za mu yi adduꞌa don mu shirya zukatanmu, sai mu karanta Littafi Mai Tsarki. Bayan haka, sai mu ɗan dakata kuma mu yi tunani mai zurfi a kan abin da muka karanta. Mene ne zai zama sakamakon hakan? Yayin da muke ci gaba da yin tunanin abin da muka karanta, za mu fahimci Kalmar Allah da kyau kuma bangaskiyarmu za ta daɗa yin ƙarfi.
17. Me ya sa yake da muhimmanci mu yi bimbini a kan abin da muka karanta daga Littafi Mai Tsarki?
17 Me ya sa yake da muhimmanci mu karanta Littafi Mai Tsarki kuma mu yi tunani a kansa? Yin hakan zai ba mu ƙarfin zuciya da muke bukata don mu ci gaba da yin waꞌazi yanzu, kuma mu iya yin shelar hukunci a nan gaba. Ƙari ga haka, idan muka yi bimbini a kan halayen Jehobah masu kyau, dangantakarmu da shi za ta daɗa yin ƙarfi. A sakamakon haka, za mu sami wani abu mai daɗi ko zaƙi kamar zuma, wato kwanciyar hankali da kuma gamsuwa.—Zab. 119:103.
ABIN DA KE SA MU JIMRE
18. Mene ne mutanen da ke yankinmu za su gane, kuma me ya sa?
18 Ezekiyel annabi ne, amma mu ba annabawa ba ne. Duk da hakan, mun ƙudiri niyyar ci gaba da yin shelar saƙon da Jehobah ya sa a rubuta a Littafi Mai Tsarki har sai lokacin da Jehobah ya ce aikin waꞌazin ya isa. A lokacin da Jehobah zai zartar da hukuncinsa, mutane da ke yankinmu ba za su kasance da wata hujja na cewa ba a gaya musu saƙon Jehobah ba ko kuma su ce Jehobah ya yi watsi da su. (Ezek. 3:19; 18:23) A maimakon haka, za su gane cewa saƙon da muka idar musu daga wurin Jehobah ne.
19. Me zai ba mu ƙarfin zuciyar da muke bukata don mu iya cim ma hidimarmu?
19 Mene ne zai ba mu ƙarfin zuciya da muke bukata don mu yi nasara? Abubuwa uku da suka taimaka wa Ezekiyel za su iya taimaka mana. Muna ci gaba da yin waꞌazi domin mun san cewa Jehobah ne ya aike mu, ruhunsa mai tsarki yana ba mu ƙarfin zuciya, kuma Kalmarsa Littafi Mai Tsarki tana ƙarfafa bangaskiyarmu. Da taimakon Jehobah, muna a shirye mu ci gaba da yin hidimarmu kuma mu jimre har “zuwa ƙarshe.”—Mat. 24:13.
WAƘA TA 65 Mu Riƙa Samun Ci Gaba!
a A wannan talifin, za mu tattauna abubuwa guda uku da suka taimaka wa annabi Ezekiyel ya yi nasara a hidimarsa. Yayin da muke hakan, za mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana mu yi nasara a hidimarmu.