Jumma’a, 25 ga Nuwamba
Miji shi ne shugaban matarsa.—1 Kor. 11:3.
Miji ne zai ba da lissafi ga Jehobah da Yesu a kan yadda ya yi sha’ani da iyalinsa. (1 Bit. 3:7) Da yake Jehobah ne Maɗaukaki, yana da ikon kafa wa ’ya’yansa dokoki, kuma ya tabbata cewa sun bi dokokin. (Isha. 33:22) Yesu wanda shi ne shugaban ikilisiyar Kirista yana da ikon kafa dokoki. (Gal. 6:2; Kol. 1:18-20) Kamar Jehobah da Yesu, maigida Kirista yana da ikon tsai da shawarwari don iyalinsa. (Rom. 7:2; Afis. 6:4) Amma ikonsa yana da iyaka. Alal misali, ya kamata ya kafa dokoki da suka jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. (K. Mag. 3:5, 6) Kuma maigida bai da ikon kafa wa mutanen da ba ’yan iyalinsa ba dokoki. (Rom. 14:4) Ƙari ga haka, sa’ad da yaransa suka girma kuma suka bar gida, za su riƙa daraja shi amma ba shi da iko a kansu.—Mat. 19:5. w21.02 2-3 sakin layi na 3-5
Asabar, 26 ga Nuwamba
Ka kula da danginka.—1 Tim. 5:8.
Hanya ɗaya da magidanci zai nuna cewa yana ƙaunar iyalinsa ita ce ta wajen biyan bukatunsu. Amma yana bukatar ya tuna cewa taimaka wa iyalinsa ta kasance da dangantaka mai kyau da Allah shi ne ya fi muhimmanci. (Mat. 5:3) A lokacin da Yesu yake kan gungumen azaba, ya tabbatar cewa an kula da Maryamu. Duk da cewa Yesu yana cikin azaba sosai, ya yi shiri don manzo Yohanna ya riƙa kula da Maryamu. (Yoh. 19:26, 27) Ɗan’uwa wanda shi magidanci ne yana da ayyuka da yawa masu muhimmanci. Yana bukatar ya riƙa aiki tuƙuru a wurin aikinsa don a yabi Jehobah. (Afis. 6:5, 6; Tit. 2:9, 10) Kuma wataƙila yana da ayyuka a ikilisiya, kamar su zuwa ziyarar ƙarfafa da kuma yin ja-goranci a wa’azi. Ƙari ga haka, yana da muhimmanci ya riƙa yin nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai da matarsa da kuma yaransa. Za su nuna godiya domin dukan abubuwan da yake yi don su kasance da ƙoshin lafiya, su riƙa farin ciki kuma su ci gaba da bauta wa Jehobah.—Afis. 5:28, 29; 6:4. w21.01 12 sakin layi na 15, 17
Lahadi, 27 ga Nuwamba
[Macen kirki] tana lura da rayuwar gidanta sosai.—K. Mag. 31:27.
Kalmar Allah ta ce mace mai kirki za ta iya kula da gida, ta sayi gona ta yi shuki kuma ta riƙa kasuwanci. (K. Mag. 31:15, 16, 18) Ita ba baiwa ba ce da ba za ta iya faɗin ra’ayinta ba. Maimakon haka, mijinta yana amincewa da ita kuma ya saurare ta. (K. Mag. 31:11, 26) Idan miji yana daraja matarsa, za ta yi farin cikin yi masa biyayya. Duk da abubuwan da Yesu ya cim ma, bai yi tunanin ya fi ƙarfin yin biyayya ga Jehobah ba. (1 Kor. 15:28; Yoh. 14:28) Hakazalika, mace mai kirki da take yin koyi da Yesu ba za ta ɗauka cewa mijinta zai rena ta idan tana yi masa biyayya ba. Za ta tallafa wa mijinta ba domin tana ƙaunar shi kaɗai ba amma don tana ƙaunar Jehobah da kuma daraja shi. Mace mai yi wa mijinta biyayya ba za ta goyi bayan mijinta idan ya ce ta yi abin da bai jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ba. w21.02 11 sakin layi na 14-15; 12 sakin layi na 19