DARASI NA 47
Jehobah Ya Ƙarfafa Iliya
Jezebel ta ji abin da ya faru da annabawan Baal kuma hakan ya sa ta fushi sosai. Sai ta ce a gaya wa Iliya cewa: ‘Gobe, kai ma za ka mutu kamar annabawan nan.’ Hakan ya sa Iliya ya ji tsoro sosai har ya gudu zuwa cikin jeji. Sai ya yi addu’a: ‘Jehobah, na gaji. Ka bar ni in mutu kawai.’ Da yake Iliya ya gaji, sai barci ya kwashe shi a ƙarƙashin wata bishiya.
Wani mala’ika ya tashe shi a hankali ya ce: ‘Tashi ka ci abinci.’ Iliya ya ga gurasa a kan murhu da kuma ruwa a cikin gora. Sai ya ci ya sha kuma ya koma barci. Mala’ikan ya sake tashe shi, ya ce: ‘Gashi ka ci. Kana bukatar ƙarfi don tafiyar da za ka yi.’ Sai Iliya ya sake ci. Bayan haka, ya yi tafiya zuwa Dutsen Horeb kuma ya yi kwana 40 kafin ya kai wurin. Da ya kai, sai ya je wani kogon dutse don ya yi barci. Sai Jehobah ya ce masa: ‘Iliya, me kake nema a nan?’ Iliya ya ce: ‘Isra’ilawa sun daina bauta maka. Sun halaka bagadanka kuma sun kashe annabawanka. Ga shi kuma yanzu, suna so su kashe ni.’
Jehobah ya ce masa: ‘Ka hau dutsen.’ Sai aka yi iska mai ƙarfi sosai a gaban kogon. Bayan haka, aka yi girgizar ƙasa kuma wuta ta sauko. A ƙarshe, Iliya ya ji wata ƙaramar murya. Sai ya rufe fuskarsa da rigarsa kuma ya tsaya a baƙin kogon. Sai Jehobah ya tambaye shi dalilin da ya sa ya gudu. Iliya ya ce: ‘Ni kaɗai ne nake bauta maka.’ Amma Jehobah ya ce masa: ‘Ba kai kaɗai ba ne. Akwai mutane 7,000 a Isra’ila da suke bauta mini har yanzu. Je ka shafe Elisha a matsayin annabi.’ Nan da nan, sai Iliya ya je ya yi abin da Jehobah ya gaya masa. Shin kana tunanin cewa Jehobah zai taimaka maka? Ƙwarai kuwa. Bari mu ga abin da ya faru sa’ad da ba a yi ruwan sama a ƙasar ba.
“Kada ku yi alhini cikin kowane abu; amma cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah.”—Filibiyawa 4:6