Laraba, 15 ga Yuli
Ubangiji mai taimakona ne, ba zan ji tsoro ba.—Ibran. 13:6.
Ba shakka, wasiƙar manzo Bulus ta taimaka wa Ibraniyawan su yi shiri don wahalar da za su sha a lokacin. Bulus ya ƙarfafa su su yi nazarin Kalmar Allah da kyau don su fahimce ta sosai. Hakan zai sa su gane koyarwa da ba daidai ba kuma su guje mata, don irin koyarwar nan za ta iya sa su yi sanyin gwiwa. Ya kuma ƙarfafa su su yi ƙoƙari su ƙara zama masu bangaskiya don su yi saurin bin ja-gorancin Yesu da na dattawa a ikilisiya. Ƙari ga haka, Bulus ya taimaka wa Kiristocin su zama da raꞌayin da ya dace game da tsanantawa. Ya ce su ɗauke shi a matsayin horarwa. Wato Ubanmu mai ƙauna zai iya amfani da wannan damar ya koya musu wasu halaye masu kyau. Bari mu ma mu bi waɗannan shawarwarin da Allah ya sa a rubuta. Abin da zai taimaka mana mu jimre har zuwa ƙarshe ke nan.—Ibran. 3:14. w24.09 13 sakin layi na 17, 19
Alhamis, 16 ga Yuli
An mai da mu tsarkaka ta wurin hadayar jikinsa wadda Yesu Almasihu ya miƙa sau ɗaya tak ba ƙari.—Ibran. 10:10.
Bisa ga Littafi Mai Tsarki, Jehobah ya tsai da shawara cewa za a biya fansa don a iya gafarta mana, kuma mu zama aminansa. Me ake bukatar a biya domin ꞌyan Adam su sami abin da Adamu ya rasa? Ana bukatar a biya abin da ya yi daidai da wanda aka rasa. (1 Tim. 2:6) Ka tuna cewa Adamu da Hauwaꞌu sun rasa gatan yin rayuwa har abada, kuma sun zama masu zunubi. Mene ne zai yi daidai da abin da suka rasa? Ana bukatar mutum, wanda (1) bai da zunubi; (2) zai iya yin rayuwa har abada a duniya; kuma (3) zai yarda ya ba da ransa a madadinmu. Me ya sa Yesu ne zai iya biyan wannan fansar? Ga dalilai uku: (1) An haife shi bai da zunubi, kuma “bai taɓa yin laifi ba ko kaɗan.” (1 Bit. 2:22) (2) Zai iya yin rayuwa har abada a duniya don bai da zunubi. (3) Ya yarda ya ba da ransa a madadinmu.—Ibran. 10:9. w25.02 4-5 sakin layi na 11-12
Jummaꞌa, 17 ga Yuli
[Yana] ba shi ruhunsa babu iyaka.—Yoh. 3:34.
Jehobah yana ƙaunar ka kuma yana so ka kasance cikin iyalinsa. Yesu ya gaya ma wasu mabiyansa a ƙarni na farko cewa: “Idan kuna da bangaskiyar da ta yi ƙanƙanta kamar ƙwayar mastad, za ku iya ce wa tudun nan ya tashi daga nan zuwa can, kuma zai tashi. Ba kuwa abin da zai gagare ku.” (Mat. 17:20) Waɗanda Yesu yake yi wa magana sun yi ꞌyan shekaru ne kawai tare da shi, saboda haka, suna bukatar su ci-gaba da ƙarfafa bangaskiyarsu. Amma Yesu ya tabbatar musu cewa, idan sun kasance da bangaskiya, Jehobah zai taimaka musu su yi nasara, ko da wace irin matsala ce suke fuskanta. Kai ma Jehobah zai taimaka maka ka yi hakan! Idan akwai wani abin da zai iya hana ka yin baftisma, ka yi iya ƙoƙarinka ka kawar da shi nan da nan. Ka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma. Wannan ita ce shawara mafi kyau da za ka taɓa yankewa a rayuwa! w25.03 7 sakin layi na 18-20