DARASI NA 1
Gabatarwa Mai Daɗi
Ayyukan Manzanni 17:22
ABIN DA ZA KA YI: Gabatarwarka ta zama wadda za ta jawo hankali, ta yi daidai da jigon jawabin ta kuma nuna wa masu sauraron yadda za su amfana daga batun.
YADDA ZA KA YI HAKAN:
Ka ja hankalin mutane. Ka yi amfani da tambaya ko labarin wani ko abin da ka ji a rediyo ko talabijin da zai ja hankalin masu sauraronka.
Ka bayyana jigon jawabin. Ka tabbata cewa gabatarwarka ta yi daidai da jigon jawabinka da kuma saƙon da ke ciki.
Ka nuna yadda batun yake da muhimmanci. Ka faɗi abin da ya fi damun masu sauraronka. Ka sa su fahimci yadda batun zai iya taimaka musu.