DARASI NA 10
Muryar da Ta Dace
Karin Magana 8:4, 7
ABIN DA ZA KA YI: Don saƙon ya taɓa zuciyar masu sauraro, ka riƙa canja murya, kana iya ɗaga murya, rage murya, ƙara sauri ko rage sauri.
YADDA ZA KA YI HAKAN:
Muryarka ta yi daidai da abin da kake faɗa. Ka ɗaga muryarka sa’ad da kake nanata muhimman darussa ko ƙarfafa masu sauraro su yi wani abu. Ka yi hakan yayin da kake karanta hukuncin da ke Littafi Mai Tsarki. Ka sauƙe muryarka sa’ad da kake magana a kan abin ban tsoro ko damuwa.
Ka riƙa canja murya. Yayin da kake magana a kan abu mai ban sha’awa ko kana so ka kwatanta girman wani abu ko kuma nisan wani wuri, ka ɗaga murya. Yayin da kuma kake bayyana abin baƙin ciki ko wata matsala, muryarka ta nuna hakan.
Ka yi magana da sauri ko kuma a hankali. Ka yi magana da sauri don ka nuna farin cikinka. Yayin da kuma kake bayyana muhimman darussa, ka yi hakan a hankali.