DARASI NA 12
Ka Nuna Ƙauna da Tausayi
1 Tasalonikawa 2:7, 8
ABIN DA ZA KA YI: Ka nuna wa masu sauraronka cewa kana ƙaunarsu kuma ka damu da su.
YADDA ZA KA YI HAKAN:
Ka yi tunani game da masu sauraronka. A lokacin da kake yin shiri, ka yi tunani sosai game da matsalolin da masu sauraronka suke fuskanta, kuma ka ɗauka kana cikin yanayinsu.
Ka yi amfani da kalaman da suka dace. Ka nemi yadda za ka ƙarfafa da kuma faranta zuciyar masu sauraronka. Ka guji yin amfani da kalaman da za su sa su fushi kuma kada ka yi maganar da ba ta dace ba game da waɗanda ba sa bauta wa Jehobah.
Ka nuna ka damu da su. Ka yi amfani da murya mai daɗi kuma ka motsa hannayenka yadda suka dace, don masu sauraronka su ga cewa ka damu da su. Kuma ka riƙa fara’a.