Rahoto Daga Masu Shelar Mulki
Wasiƙar Alejandra
DA DAƊEWA wasiƙa hanya ce mai kyau na yin wa’azi. Ko da yake a wani lokaci ba a sanin sakamakonsa, waɗanda suka nace da yin amfani da ita sun sami albarka. Sun tuna da gargaɗi mai kyau na Littafi Mai Tsarki: “Ka shuka iri da safe, da yamma kuma kada ka janye hannunka, gama ba ka san wanda zai yi albarka ba, ko wannan ko wancan, ko kuma duka biyunsu su yi albarka.”—Mai Hadishi 11:6.
Alejandra, wata Mashaidiya matashiya ce da take hidima a ofishin reshe na Shaidun Jehobah a Mexico. Tana shan magani na ciwon daji misalin shekara goma. Yanayinta ya daɗa muni, kuma ta raunana ainun da ba ta iya yin aikinta kuma. Da yake tana son ta ci gaba da hidimarta, Alejandra ta tsai da shawarar rubuta wasiƙu. Ta rubuta game da tsarin nazarin Littafi Mai Tsarki a gida kyauta kuma ta haɗa lambar tarho na mamarta. Sai ta ba mamarta wasiƙun don ta saka a gidajen da mutane ba sa gida lokacin da mamar take hidima ta kofa kofa.
Diojany wata yarinya a garin Guatemala, ta je aikin kula da gida a garin Cancún, a Mexico. Sa’ad da take wajen ta sadu da Shaidun Jehobah kuma ta ji daɗin tattauna Littafi Mai Tsarki da su. Daga baya waɗanda take wa aiki suka tsai da shawarar ƙaura zuwa Birnin Mexico kuma suna son ta bi su. Diojany ta yi jinkirin binsu domin ba za ta riƙa saduwa da Shaidun ba.
Waɗanda take wa aiki suka tabbatar mata cewa “kada ki damu, Shaidu suna ko’ina. Za mu neme su muddin muka isa wajen.” Da wannan a zuciya Diojany ta yarda ta bi su. Da suka kai Birnin Mexico, waɗanda Diojany take wa aiki suka nemi Shaidun. Amma domin wasu dalilai ba su same su ba ko da yake a birnin akwai Shaidu fiye da 41,000 da kuma ikilisiyoyi 730.
Ba da daɗewa ba Diojany ta soma sanyin gwiwa domin ba ta sami Shaidu don ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki ba. Wata rana, wadda take wa aiki ta dawo gida tana cewa: “Abin mamaki! Allahn ki ya ji addu’arki.” Ta ba ta wata wasiƙa, ta ce: “Shaidun sun bar miki wannan wasiƙar.” Wasiƙar Alejandra ce.
Diojany ta sadu da mamar Alejandra da kuma ƙanwarta da ake kira Blanca. Ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Bayan wasu makonni, ta sadu da Alejandra kuma suka yi farin cikin sanin juna. Alejandra ta ƙarfafata ta ci gaba da nazarin Littafi Mai Tsarki domin ta samu ci gaba ta ruhaniya.
Bayan wasu watanni, a Yuli ta shekara ta 2003, Alejandra ta rasu. Ta nuna wa ’yan’uwanta masu bi misali mai kyau na kasancewa da bangaskiya da gaba gaɗi. A jana’izarta, mutane da yawa sun motsu sosai sa’ad da suka sadu da Diojany kuma suka ji ta ce: “Alejandra da iyalinta misali ne mai kyau a gare ni. Na ƙudura aniyar bauta wa Jehobah kuma in yi baftisma ba da daɗewa ba. Ina sha’awar ganin Alejandra a cikin Aljanna a nan gaba!”
Hakika, wasiƙa ƙaramar aba ce. Amma tana kawo sakamako mai kyau na dindindin!