Zuwa Ga Masu Karatu
MUNA farin cikin sanar da ku cewa farawa daga wannan mujallar, za a yi wasu canje-canje a Hasumiyar Tsaro. Kafin mu yi bayani game da canje-canjen bari mu faɗi abubuwa da za su kasance kamar yadda suke a dā.
Sunan wannan mujallar, Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah, bai canja ba. Saboda haka, Hasumiyar Tsaro za ta ci gaba da girmama Jehobah, Allah na gaskiya kuma ta yi wa masu karatunta ta’aziyya da bisharar Mulki. Talifofi da suke shafuffuka na 5 zuwa 9 na wannan fitowar za su tattauna ma’anar Mulkin da kuma lokacin da zai zo. Ƙari ga haka, Hasumiyar Tsaron za ta ci gaba da ƙarfafa bangaskiya ga Yesu Kristi, ta yaɗa gaskiya ta Littafi Mai Tsarki, kuma ta bayyana ma’anar abubuwan da suke faruwa a duniya kamar yadda annabce-annabce na Littafi Mai Tsarki suka nuna, kamar yadda ta yi na shekaru masu yawa.
To, menene kuma sabo? Bari mu yi bayani game da wasu abubuwan ban sha’awa da za su kasance a cikin fitowa ta 1 ga wata.a
Talifofi masu sa tunani za su riƙa fitowa kowane wata. Talifi mai jigo “Ka San?” zai ba da cikakken bayani game da ma’anar wasu zaɓaɓɓun labarai daga Littafi Mai Tsarki. Talifin nan “Ka Kusaci Allah” zai nanata abin da za mu koya game da Jehobah daga wasu takamammun ayoyin Littafi Mai Tsarki. Talifin nan “Masu Karatu Sun Yi Tambaya” zai ba da amsoshi ga tambayoyi da aka yi game da Littafi Mai Tsarki. Alal misali, mutane da yawa suna tambaya, “Mulkin Allah a zuciyarmu take da gaske?” Za ka sami amsa a shafi na 13.
An tsara wasu talifofi domin iyalai su amfana. Talifin nan “Yadda Iyali Za ta Sami Farin Ciki,” zai fito sau huɗu a shekara, zai yi bayani a kan irin matsalolin da iyalai suke fuskanta kuma ya nuna yadda mizanan Littafi Mai Tsarki za su taimaka wajen magance su. “Ku Koyar da ’ya’yanku,” talifi ne da zai bayyana domin iyaye su karanta da ’ya’yansu. Za a riƙa musanya da wannan talifin “Domin Matasanmu,” wanda zai gabatar da yadda matasa za su yi nazarin Littafi Mai Tsarki.
Wasu talifofi kuma za su bayyana sau huɗu a shekara. “Ku Yi Koyi da Bangaskiyarsu” zai ƙarfafa mu mu bi misalin mutanen dā. Alal misali a shafi na 18 zuwa 21 na wannan fitowar, za ka karanta tarihi mai ban sha’awa na Iliya da kuma yadda za mu yi koyi da bangaskiyarsa. Wani talifi kuma “Wasiƙa daga . . . ” zai ba da rahoto daga masu wa’azi a ƙasashen waje da kuma wasu ɓangarorin duniya dabam dabam. “Abin da Muka Koya Daga Yesu” zai gabatar da abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa a sauƙaƙe.
Muna da tabbaci cewa Hasumiyar Tsaro za ta ci gaba da kayatar da masu karanta ta a ko’ina waɗanda suke daraja Littafi Mai Tsarki kuma suke so su san abin da yake koyarwa. Muna fatan cewa wannan mujallar za ta taimaka wajen gamsar da bukatarka ta gaskiyar Littafi Mai Tsarki.
MASU BUGAWA
[Hasiya]
a Yanzu za a riƙa buga Hasumiyar Tsaro iri biyu. Wannan fitowar mai kwanan wata, 1 ga wata za a buga ne domin dukan jama’a. Fitowa mai kwanan wata, 15 ga wata za ta kasance na nazari ce wadda Shaidun Jehobah za su yi amfani da ita a taronsu na ikilisiya, wanda jama’a suna iya halarta.