Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 4/1 p. 19
  • Yesu Ne Mika’ilu Sarkin Mala’iku?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yesu Ne Mika’ilu Sarkin Mala’iku?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Wanene Mika’ilu Shugaban Mala’iku?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Wane ne Mika’ilu, Shugaban Mala’iku?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 4/1 p. 19

Masu Karatu Sun Yi Tambaya . . .

Yesu Ne Mika’ilu Sarkin Mala’iku?

▪ A taƙaice, amsar ita ce e. Kiran mutum da suna fiye da guda sanannen abu ne a al’adu masu yawa. Yanayin iri ɗaya ne da sunayen mutane a lokacin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, an kira Yakubu uban iyali Isra’ila. (Farawa 35:10) A cikin rubutu na ainihi, an kira manzo Bitrus da sunaye biyar, Symeon, Siman, Bitrus, Kefas, da Siman Bitrus. (Matta 10:2; 16:16; Yohanna 1:42; Ayyukan Manzanni 15:7, 14) Yaya za mu iya tabbatar da cewa Mika’ilu wani suna ne na Yesu? Ka yi la’akari da waɗannan tabbaci daga Nassi.

Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da wurare biyar da aka ambata wannan halittar ruhu mai girma, Mika’ilu. Guda uku sun bayyana a littafin Daniyel. A littafin Daniyel 10:13, 21, mun karanta cewa Mika’ilu wanda aka kira “ɗaya daga cikin manyan sarakuna” da kuma “sarkinku,” ya ceci wani mala’ika da aka aika. Bayan haka, a Daniyel 12:1, mun koyi cewa a lokacin ƙarshe, “Michael [Mika’ilu] za ya tashi tsaye, shi babban jarumin nan mai-kāriyar ’ya’yan jama’arka.”

An sake ambata Mika’ilu a Ru’ya ta Yohanna 12:7 wadda ta kwatanta cewa ‘Mika’ilu da nasa mala’iku’ suna yin yaƙi mai muhimmanci da ya sa aka kori Shaiɗan Iblis da miyagun mala’ikunsa daga sama.

Ka lura cewa a kowanne cikin yanayin da aka ambata a sama, an nuna Mika’ilu a matsayin jarumin mala’ikan da ke yaƙi da kuma kāre mutanen Allah, har ma da kai hari ga Shaiɗan babban abokin gaban Jehobah.

Yahuda aya ta 9 ta kira Mika’ilu “shugaban mala’iku.” Ba a taɓa yin amfani da kalmomin nan “shugaban mala’iku” a matsayin jam’i ba a cikin Littafi Mai Tsarki. Wata aya guda kawai da aka sake ambata shugaban mala’iku ita ce 1 Tasalunikawa 4:16, inda Bulus yake kwatanta Yesu da aka ta da daga matattu, cewa: “Ubangiji [Yesu] da kansa za ya sauko daga sama, da kira mai-ƙarfi, da muryar sarkin mala’iku, da ƙafon Allah kuma.” Saboda haka a nan an kira Yesu Kristi sarkin mala’iku, ko shugaban mala’iku.

Bisa ga dukan waɗannan batutuwan, menene za mu kammala? Yesu Kristi shi ne Mika’ilu shugaban mala’iku. Sunayen nan biyu Mika’ilu (da ke nufin “Wanene Kamar Allah?”) da Yesu (da ke nufin “Jehobah Mai Ceto Ne”) sun mai da hankali ne ga matsayinsa na wanda ke kan gaba wajen goyon bayan ikon mallakar Allah. Filibiyawa 2:9 ta ce: “Allah kuma ya ba shi [Yesu da aka ɗaukaka] mafificiyar ɗaukaka, ya ba shi suna wanda ke bisa kowane suna.”

Yana da muhimmanci mu fahimci cewa haihuwar Yesu da aka yi a duniya ba ita ba ce farkon rayuwarsa. Kafin a haifi Yesu, wani mala’ika ya ziyarci Maryamu kuma ya gaya mata cewa za ta haifi ɗa ta hanyar ruhu mai tsarki kuma ta kira sunan ɗan Yesu. (Luka 1:31) A lokacin hidimarsa, Yesu yakan yi magana game da rayuwarsa kafin ya zama ɗan Adam.—Yohanna 3:13; 8:23, 58.

Saboda haka, Mika’ilu shugaban mala’iku shi ne Yesu kafin ya zo duniya. Bayan tashinsa daga matattu da kuma komawarsa sama, Yesu ya soma hidimarsa a matsayin Mika’ilu, shugaban mala’iku, “domin ɗaukaka Allah Uba.”—Filibiyawa 2:11, Littafi Mai Tsarki.

    Littattafan Hausa (1987-2025)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba