DARASI NA 42
Jonathan Mai Ƙarfin Hali da Aminci
Jonathan ne babba cikin yaran Sarki Saul kuma shi soja ne mai ƙarfin hali sosai. Dauda ya ce Jonathan ya fi gaggafa sauri kuma ya fi zaki ƙarfi. Wata rana, Jonathan ya ga wasu Filistiyawa a kan wani tudu. Sai ya gaya wa mai riƙe masa kayan yaƙi cewa: ‘Sai Jehobah ya nuna alama kafin za mu kai musu hari. Idan Filistiyawan sun ce mu zo, sai mu kai musu hari.’ Filistiyawan suka yi ihu suka ce: ‘Ku zo mu yi faɗa!’ Sai mazan biyu suka hau kan tudun kuma suka kashe sojoji guda 20.
Tun da Jonathan ne babba a cikin yaran Saul, shi ne ya kamata ya zama sarki bayan babansa. Amma Jonathan ya san cewa Jehobah ya zaɓi Dauda ya zama sarkin Isra’ila kuma bai yi kishin Dauda ba. Jonathan da Dauda sun zama abokai. Sun yi alkawari cewa za su taimaka wa juna. Har ma Jonathan ya ba Dauda rigarsa da doguwar wuƙarsa da bakansa da kuma ɗamararsa don ya nuna irin abokantakar da ke tsakaninsu.
Sa’ad da Dauda ya gudu don Saul yana nema ya kashe shi, Jonathan ya je wurinsa kuma ya ce masa: ‘Ka kasance da ƙarfin zuciya. Jehobah ya riga ya zaɓe ka ka zama sarki. Kuma babana ma ya san da hakan.’ Shin za ka so ka sami aboki kamar Jonathan?
Sau da yawa, Jonathan ya sadaukar da ransa don ya ceci abokinsa. Ya san cewa Sarki Saul yana so ya kashe Dauda. Don haka, ya gaya wa mahaifinsa cewa: ‘Za ka yi zunubi idan ka kashe Dauda domin bai yi wani laifi ba.’ Saul ya yi fushi da Jonathan sosai. Bayan wasu shekaru, sai aka kashe Saul da kuma Jonathan a yaƙi.
Bayan Jonathan ya mutu, sai Dauda ya nemi ɗan Jonathan mai suna Mephibosheth. Da Dauda ya same shi, sai ya ce wa Mephibosheth: ‘Mahaifinka abokina ne sosai. Don haka, zan kula da kai har ƙarshen ranka. Za ka zauna a fādata kuma ka ci abincin da nake ci.’ Hakika, Dauda bai taɓa manta da abokinsa Jonathan ba.
“Ku yi ƙaunar juna, kamar yadda ni na ƙaunace ku. Ba wanda yake da ƙauna wadda ta fi gaban wannan, wato mutum ya ba da ransa domin abokansa.”—Yohanna 15:12, 13