Karatun Littafi Mai Tsarki—Mai Amfani Kuma Mai Daɗi
“Ka yi . . . [karatunsa] dare da rana.”—JOSHUWA 1:8.
1. Menene amfanin karatu gabaki ɗayansa, musamman ma na Littafi Mai Tsarki?
KARATUN abubuwa masu kyau yana da amfani. Montesquieu ɗan falsafa na siyasar faransanci (Charles-Louis de Secondat) ya rubuta: “A gare ni, nazari shi ne babban maganin damuwar rayuwa. Babu wata damuwa da ta faɗo mini da karatu na sa’a guda bai kawar da ita ba.” Wannan gaskiya ne ƙwarai, game da karatun Littafi Mai Tsarki. Haka mai Zabura da aka hure ya ce: “Dokar Ubangiji cikakkiya ce, tana wartsakar da rai. Umarnan Ubangiji abin dogara ne, sukan ba da hikima ga wanda ba shi da ita. Ka’idodin Ubangiji daidai suke, waɗanda suke biyayya da su sun ji daɗi. Umarnan Ubangiji daidai suke, sukan ba da fahimi ga zuciya.”—Zabura 19:7, 8.
2. Me ya sa Jehovah ya adana Littafi Mai Tsarki a duk cikin shekaru, kuma menene yake son mutanensa su yi da shi?
2 Allah Jehovah mawallafin Littafi Mai Tsarki, ya adana shi a lokacin hamayya daga abokan gaba na addini da kuma waɗanda ba na addini ba. Tun da nufinsa ne “dukkan [irin-irin] mutane su sami ceto, su kuma kai ga sanin gaskiya,” ya ga cewa Kalmarsa ta samu ga dukan talikai. (1 Timoti 2:4) An kimanta cewa za a kai wajen misalin kashi 80 bisa ɗari na mazaunan duniya idan aka yi amfani da harsuna 100. Ana iya samun Littafi Mai Tsarki gabaki ɗayansa cikin harsuna 370, wasu sashen Nassosi kuma cikin harsuna 1,860. Jehovah yana son mutanensa su riƙa karatun Kalmarsa. Ya albarkaci bayinsa waɗanda suka mai da hankali bisa Kalmarsa, i, waɗanda suke karatunsa kullum.—Zabura 1:1, 2.
An Bukaci Dattawa Su Yi Karatun Littafi Mai Tsarki
3, 4. Menene Jehovah yake bukata daga wurin sarakunan Isra’ila, kuma saboda wane dalilai ne waɗannan bukatu ya shafi Kiristoci dattawa a yau?
3 Da yake magana game da lokacin da al’ummar Isra’ila za ta sami sarki bil adam, Jehovah ya ce: “Sa’ad da ya hau gadon sarautar, sai ya sa a rubuta masa dokoki daga cikin littafin dokoki wanda ke wurin Lawiyawan da ke firistoci. Kada ya rabu da littafin, amma ya riƙa karanta shi dukan kwanakinsa domin ya koyi tsoron Ubangiji Allahnsa ta wurin kiyaye dukan dokoki da umarnai, don kada zuciyarsa ta kumbura, har ya ga ya fi ’yan’uwansa, don kuma kada ya karkace daga bin umarni zuwa dama ko hagu.”—Maimaitawar Shari’a 17:18-20.
4 Ka lura da dalilai da suka sa Jehovah ya bukaci dukan sarakunan Isra’ila na gaba su karanta littafin da ke ɗauke da dokokin Allah kullum: (1) “domin ya koyi tsoron Ubangiji Allahnsa ta wurin kiyaye dukan dokoki da umarnai”; (2) “don kada zuciyarsa ta kumbura, har ya ga ya fi ’yan’uwansa”; (3) “don kuma kada ya karkace daga bin umarni zuwa dama ko hagu.” Kiristoci masu kula a yau ba sa bukatar su tsoraci Jehovah ne, su kiyaye dokokinsa, su guje wa ɗaukaka kansu bisa ’yan’uwansu, kuma guje kauce wa umarnan Jehovah? Babu shakka karatun Littafi Mai Tsarki kullum yana da muhimmanci a gare su kamar yadda yake ga sarakunan Isra’ila.
5. Menene Hukumar Mulki ta rubuta ba da daɗewa ba zuwa ga Kwamitocin Rassa game da karatun Littafi Mai Tsarki, kuma me ya sa dukan Kiristoci dattawa ya kamata su bi wannan gargaɗin?
5 Kiristoci dattawa a yau suna da ayyuka da yawa, da ya sa karatun Littafi Mai Tsarki kullum ya zama wani kaluɓale. Alal misali, waɗanda suke cikin Hukumar Mulki na Shaidun Jehovah da kuma waɗanda suke cikin Kwamitin Rassa a dukan duniya mutane ne da suke shagala cikin aiki ƙwarai. Duk da haka, wasiƙa ta baya bayan nan daga wajen Hukumar Mulki zuwa ga dukan Kwamitocin Rassa ta nanata bukatar karatun Littafi Mai Tsarki kullum da kuma tsarin nazari mai kyau. Wannan, wasiƙar ta ce, zai ƙara ƙaunarmu ga Jehovah da kuma gaskiya, kuma zai “taimaka mana mu kiyaye bangaskiyarmu, farin cikinmu, da kuma jurewarmu har zuwa ƙarshe mafi kyau.” Dukan dattawan iklisiyoyi na Shaidun Jehovah suna da irin wannan bukatar. Karatun Nassosi kullum zai taimaka musu su “arzuta.” (Joshuwa 1:7, 8) Don su musamman, karatun Littafi Mai Tsarki “mai amfani ne kuma wajen koyarwa, da tsawatarwa, da gyaran hali, da kuma tarbiyyar aikin adalci.”—2 Timoti 3:16.
Wajibi ga Matasa da Tsofaffi
6. Me ya sa Joshuwa ya karanta dukan kalmomin dokar Jehovah da babbar murya a gaban taron ƙabilun Isra’ila da kuma baƙi da suke zaune tare da su?
6 A lokatan dā, mutane ba su da Nassosi a wurinsu, saboda haka karatun Littafi Mai Tsarki ana yi ne a gaban taron jama’a. Bayan Jehovah ya ba Joshuwa nasara bisa birnin Ai, sai ya tara ƙabilun Isra’ila a gaban Dutsen Ebal da kuma Dutsen Gerizim. Sai, tarihin ya ce: “Ya karanta dukan zantattukan shari’a, da na albarka da na la’ana, bisa ga dukan abin da aka rubuta cikin Attaura. Babu wata kalmar da Musa ya umarta, da Joshuwa bai karanta a gaban dukan taron Isra’ilawa ba, tare da mata da ƙanana, da baƙin da ke zaune tare da su.” (Joshuwa 8:34, 35) Yara da manya, ɗan ƙasa da baƙo, an bukace su su kafa a zukatarsu da kuma tunaninsu irin ɗabi’un da za su kawo albarkar Jehovah da kuma abin da zai kawo la’anarsa. Karatun Littafi Mai Tsarki a kai a kai babu shakka zai taimaka mana a yin wannan.
7, 8. (a) Su waye suke kama da “baƙi,” kuma me ya sa ya kamata su riƙa karatun Littafi Mai Tsarki kullum? (b) Ta wace hanya ce yara “ƙanana” da suke tsakanin mutanen Jehovah za su iya koyi da Yesu?
7 A yau, miliyoyin Shaidun Jehovah suna kama da waɗannan “baƙi” a azanci na ruhaniya. A dā, suna rayuwa bisa mizanan duniya, amma sun sake rayukansu. (Afisawa 4:22-24; Kolosiyawa 3:7, 8) Suna bukatar su riƙa tuna wa kansu mizanan Jehovah na nagarta da mugunta kullum. (Amos 5:14, 15) Karatun Littafi Mai Tsarki kullum zai taimaka musu su yi wannan.—Ibraniyawa 4:12; Yakubu 1:25.
8 Da akwai yara “ƙanana” da yawa a tsakanin mutanen Jehovah waɗanda iyayensu suka koya musu mizanan Jehovah, amma waɗanda suke bukatar su huɗubantar da kansu game da adalcin nufinsa. (Romawa 12:1, 2) Ta yaya za su yi wannan? A Isra’ila, firist da kuma dattawa an umarce su: “Sai ku karanta musu waɗannan dokoki su ji da kunnuwansu. Ku tara dukan jama’a wuri ɗaya, mata da maza, da yara, da baƙin da ke zaune tare da ku a garuruwanku domin su ji, su koyi tsoron Ubangiji Allahnku, su kuma lura su aikata dukan dokokin nan, domin ’ya’yansu, waɗanda ba su sani ba, su ji, su koyi tsoron Ubangiji Allahnku.” (Maimaitawar Shari’a 31:11-13) A ƙarƙashin Dokar, Yesu ɗan shekara 12 kawai ya nuna yana so ya fahimci dokokin Ubansa. (Luka 2:41-49) Daga baya, ta zama al’adarsa ya saurari karatu kuma ya yi karatun Nassosi a majami’a. (Luka 4:16; Ayyukan Manzanni 15:21) Ya kamata yara su yi ƙoƙari su yi koyi da Yesu wajen karatun Littafi Mai Tsarki kullum kuma su riƙa halartan taro inda ake karatun Littafi Mai Tsarki kuma ake nazarinsa.
Karatun Littafi Mai Tsarki —Abu ne da Ya fi Muhimmanci
9. (a) Me ya sa ya kamata mu riƙa zaɓen abin da za mu karanta? (b) Menene wanda ya kafa wannan jaridar ya ce game da littattafai na nazarin Littafi Mai Tsarki?
9 Sarki mai hikima Sulemanu ya rubuta: “Ka yi hankali, . . . gama wallafa littattafai ba shi da iyaka, yawan karatu kuma gajiyar da kai ne!” (Mai Hadishi 12:12) Za a iya ƙarawa da cewa karatun littattafai da yawa da ake wallafawa a yau ba gajiyar da kai ba ne kawai amma kuma haɗari ne ga zuciya. Saboda haka, yana da kyau a riƙa zaɓe. Ƙari ga karatun littattafan nazarin Littafi Mai Tsarki, muna bukatar mu karanta Littafi Mai Tsarkin kansa. Wanda ya kafa buga wannan jaridar ya rubuta zuwa ga masu karatunta: “Kada ku manta cewa Littafi Mai Tsarki shi ne Mizaninmu ko yaya taimako da Allah ya ba mu, ‘taimako’ ne ba masauyin Littafi Mai Tsarki ba ne.”a Saboda haka, yayin da ba ma banza da littattafai masu tushe daga Littafi Mai Tsarki, muna bukatar karatun Littafi Mai Tsarki kansa.
10. Ta yaya “amintaccen bawan nan mai hikima” ya nanata muhimmancin karatun Littafi Mai Tsarki?
10 Saboda wannan bukata, shekaru da yawa yanzu “amintaccen bawan nan mai hikima” ya tsara karatun Littafi Mai Tsarki ya zama sashen tsarin ayyukan Makarantar Hidima ta Allah a kowacce iklisiya. (Matiyu 24:45) Wannan tsarin karatun Littafi Mai Tsarki na yanzu zai kammala Littafi Mai Tsarki a cikin shekara bakwai. Wannan tsari zai amfani kowa, amma musamman sababbi waɗanda ba su taɓa karanta Littafi Mai Tsarki gaba ɗayansa ba. Waɗanda suka yi Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Watchtower ta Gilead domin masu zuwa wa’azi a ƙasashen waje da kuma Makarantar Koyar da Masu Hidima har da sababbi cikin iyalin Bethel ana bukatar su karanta Littafi Mai Tsarki gaba ɗayansa cikin shekara guda. Kowane irin tsari ka bi, kai kaɗai ko kuma a cikin iyali, cika wannan yana bukatar ba wa karatun Littafi Mai Tsarki muhimmanci.
Menene Halinka na Karatu Ya Nuna?
11. Ta yaya kuma me ya sa za mu ci daga maganar Jehovah kowace rana?
11 Idan bin tsarin da ka yi na karatun Littafi Mai Tsarki yana yi maka wuya, zai dace ka tambayi kanka: ‘Yaya karatuna ko kuma kallon telibijin zai shafi karatuna na Kalmar Jehovah?’ Ka tuna da abin da Musa ya rubuta—kuma da Yesu ya maimaita—“ba da gurasa kaɗai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace maganar da ke fitowa daga wurin Allah.” (Matiyu 4:4; Maimaitawar Shari’a 8:3) Kamar yadda muke bukatar mu ci burodi ko kuma abinci kowace ranar rayuwanmu domin mu rayu, hakanan muke bukatar tunanin Jehovah kowace rana domin mu kiyaye ruhaniyarmu. Za mu iya samun tunanin Jehovah kowace rana ta wurin karatun Nassosi.
12, 13. (a) Ta yaya manzo Bitrus ya misalta marmari da ya kamata mu yi na Kalmar Allah? (b) Ta yaya Bulus ya yi amfani da nono a hanyar da ta bambanta da na Bitrus?
12 Idan muka ƙaunaci Littafi Mai Tsarki, ‘ba mu karɓe ta kamar maganar mutum ce ba, sai dai ainihin yadda take, wato Maganar Allah,’ za mu matso kusa da shi kamar yadda jariri yake marmarin nonon uwarsa. (1 Tasalonikawa 2:13) Manzo Bitrus ya gwada wannan, ya rubuta: “Kamar jariri sabon haihuwa, ku yi marmarin shan madara marar gami mai ruhu, domin ku girma da shi, har ya kai ku ga samun ceto, in dai har kun ɗanɗana alherin Ubangiji.” (1 Bitrus 2:2, 3) Idan mun ɗanɗana da gaske, cewa, ‘Ubangiji mai alheri’ ne, za mu yi marmarin karatun Littafi Mai Tsarki.
13 Ya kamata a lura cewa Bitrus a wannan ayar ya yi amfani da madara ta hanya da ta bambanta da ta Manzo Bulus. Ga jariri sabon haihuwa, nono yana ɗauke da dukan abin gina jiki da yake bukata. Misalin Bitrus ya nuna cewa Kalmar Allah tana ɗauke da dukan abin da muke bukata don mu yi girma da shi, ‘har ya kai mu ga samun ceto.’ Bulus kuma, ya yi amfani da nono ya ba da misalin irin cin abinci da bai dace ba da wasu da suka kira kansu manya a ruhaniya suke yi. A wasiƙarsa zuwa ga Kiristoci Ibraniyawa, Bulus ya rubuta: “Ko da ya ke kamar yanzu kam, ai, ya kamata ku zama masu koyarwa, duk da haka, ashe, ba ku wuce wani ya sāke koya muku jigajigan farko na Maganar Allah ba, har ya zamana sai an ba ku nono, ba abinci mai tauri ba. Ai, duk wanda yake nono ne abincinsa, bai ƙware da maganar adalci ba, kamar jariri yake. Amma abinci mai tauri, ai, na manya ne, wato waɗanda hankalinsu ya horu yau da kullum, su rarrabe nagarta da mugunta.” (Ibraniyawa 5:12-14) Mai da hankali ga karatun Littafi Mai Tsarki zai hora hankalinmu kuma ya ta da marmarin abubuwa na ruhaniya.
Yadda Za a Karanta Littafi Mai Tsarki
14, 15. (a) Wace gata ce Mawallafin Littafi Mai Tsarki ya ba mu? (b) Ta yaya za mu amfana daga hikima wajen Allah? (Ka ba da misalai.)
14 Karatun Littafi Mai Tsarki mafi amfani yana farawa ba da karatu ba, amma da addu’a. Addu’a gata ce babba. Kamar kana so ka fara karatun wani littafi ne game da wani abu babba, ka kira mawallafin ya taimake ka ka fahimci abubuwan da ka ke so ka karanta. Wannan zai kawo amfani mai yawa! Mawallafin Littafi Mai Tsarki Jehovah ya ba ka wannan gatar. Wani daga cikin hukumar mulki na ƙarni na farko ya rubuta wannan zuwa ga ’yan’uwansa: “In waninku ya rasa hikima, sai ya roƙi Allah, mai ba kowa hannu sake, ba tare da gori ba, sai kuma a ba shi. Amma fa sai ya roƙa da bangaskiya, ba tare da shakka ba.” (Yakubu 1:5, 6) Hukumar Mulki ta zamani tana ariritarmu mu yi karatun Littafi Mai Tsarki tare da addu’a.
15 Hikima yin amfani ne da kyau da ilimi yadda ya dace. Saboda haka, kafin ka buɗe Littafi Mai Tsarki naka, ka roƙi Jehovah ya taimake ka ka fahimci darussa daga karatunka da suke bukatar ka yi amfani da su a rayuwarka. Ka haɗa sababbin abubuwa da ka koya da abubuwa da ka riga ka sani. Ka saka su cikin “sahihiyar maganar” da ka fahimta. (2 Timoti 1:13) Ka yi waswasi a kan rayuwar bayin Jehovah na dā, ka kuma tambayi kanka da yaya za ka yi a irin wannan yanayin.—Farawa 39:7-9; Daniyel 3:3-6, 16-18; Ayyukan Manzanni 4:18-20.
16. Waɗanne shawara aka bayar domin su taimake mu mu sa karatunmu na Littafi Mai Tsarki ya zama mai amfani?
16 Kada ka yi karatu domin kawai ka karanta inda aka ce a karanta. Ka yi a hankali. Ka mai da hankali ga abin da ka ke karantawa. Idan wani abu a ciki ya kwashi hankalinka, ka duba inda aka tura ka ka gani idan Littafi Mai Tsarki da ka ke da shi yana da wannan. Idan ba ka fahimci abin ba har ila, ka rubuta domin ka ƙara bincike daga baya. Yayin da ka ke karatu, ka saka lamba a kan ayar da ka ke so musamman ka tuna, ko kuma ka kofa. Za ka iya ƙara naka rubutu da kuma wasu ayoyi da za ka duba a hasiyar. Ayoyin da ka ke ji za ka so ka yi amfani da su wata rana a aikinka na wa’azi da koyarwa, ka kula da muhimmin kalma ka duba cikin fihirisa na Littafi Mai Tsarki da yake bayan Littafi Mai Tsarki.b
Ka Mai da Karatun Littafi Mai Tsarki Abin Farin Ciki
17. Me ya sa za mu yi farin ciki wajen karanta Littafi Mai Tsarki?
17 Mai zabura ya yi maganar mutum mai farin ciki wanda “yana jin daɗin karanta shari’ar Allah, yana ta nazarinta dare da rana.” (Zabura 1:2) Karatunmu na Littafi Mai Tsarki bai kamata ya zama abin dole ba amma abin da muke yi da farin ciki. Hanya ɗaya da za mu mai da shi abin murna ita ce fahimtar tamanin abubuwa da muke koya. Sarki mai hikima Sulemanu ya rubuta: “Mai farin ciki ne mutumin da ya zama mai hikima . . . Hikima takan sa ka ji daɗin zama, ta kuma bi da kai lafiya a zamanka. Masu farin ciki ne waɗanda suka sami hikima, hikima za ta ba su rai kamar yadda itace yakan ba da ’ya’ya.” (Karin Magana 3:13, 17, 18) Ƙoƙari da ake bukata a sami hikima da gaske kwalliya ce da za ta biya kuɗin sabulu, domin takan kai ga zaman lafiya, salama, farin ciki, a ƙarshe kuma rai.
18. Menene ya wajaba ƙari ga karatun Littafi Mai Tsarki, kuma menene za mu bincika a cikin talifi na gaba?
18 Hakika, karatun Littafi Mai Tsarki yana da amfani kuma yana da daɗi. Amma wannan ya isa ne? Waɗanda suke cocin Kiristendam suna karatun Littafi Mai Tsarki ƙarnuka da yawa da suka shige yanzu, “kullum suna koyo, amma kullum sai su kasa kaiwa ga sanin gaskiya.” (2 Timoti 3:7) Domin karatun Littafi Mai Tsarki ya zama mai amfani, dole ne mu yi shi da zuciyar amfani da ilimin da muka samu a rayuwarmu da kuma amfani da shi a aikinmu na wa’azi da kuma koyarwa. (Matiyu 24:14; 28:19, 20) Wannan yana bukatar ƙoƙari da kuma tsarin nazari mai kyau, wanda zai zama da daɗi da kuma lada, kamar yadda za mu gani a talifi da yake gaba.
[Hasiya]
a Duba Jehovah’s Witnesses—Proclaimers of God’s Kingdom, wanda Watchtower Bible and Tract Society of New York, Inc., suka buga, shafi na 241.
b Duba Hasumiyar Tsaro, fitar 1 ga Mayu, 1995 shafuffuka na 28-29, “Shawawarai don ƙara darajar karatunka na Littafi Mai-Tsarki.”
Tambayoyin Maimaitawa
• Wane gargaɗi ne da aka ba wa sarakunan Isra’ila ya shafi masu kula a yau, kuma me ya sa?
• Su waye ne a yau suke kama da “baƙi” da kuma yara “ƙanana,” kuma me ya sa suke bukatar su yi karatun Littafi Mai Tsarki kullum?
• A wace hanya ce mai amfani “amintaccen bawan nan mai hikima” ya taimake mu mu yi karatun Littafi Mai Tsarki kullum?
• Ta yaya za mu iya samun amfani na gaske da kuma farin ciki daga karatun Littafi Mai Tsarki?
[Hoto a shafi na 17]
Dattawa, musamman suna bukatar karatun Littafi Mai Tsarki kullum
[Hoto a shafi na 18]
Al’adar Yesu ne ya yi karatun Littafi Mai Tsarki a majami’a