Tsoron Allah Hikima Ne!
“Tsoron Ubangiji mafarin hikima ne.”—MISALAI 9:10.
1. Me ya sa mutane da yawa suke ganin cewa tsoron Allah yana da wuyan fahimta?
A DĀ idan aka ce mutum mai tsoron Allah ne, ana yabonsa ne. A yau kuwa, mutane da yawa suna ganin cewa idan aka ce da mutum mai tsoron Allah, tsohon yayi ne kuma batu ne mai wuyan fahimta. Za su iya tambaya, “Idan Allah ƙauna ne, me ya sa zan ji tsoronsa?” A ganinsu, tsoro abu ne da bai dace ba da ke sa mutum baƙin ciki. Duk da haka, tsoron Allah na gaske yana da ma’ana mai zurfi, kuma kamar yadda za mu gani, tsoron Allah ba motsin zuciya ba ne kawai.
2, 3. Menene tsoron Allah da gaske ya ƙunsa?
2 A cikin Littafi Mai Tsarki, tsoron Allah abu ne mai kyau. (Ishaya 11:3) Ana girmama Allah ne da kuma yi masa biyayya sosai, tare da muradi mai ƙarfi da kuma tsoron baƙanta masa rai. (Zabura 115:11) Ya haɗa da amincewa da kuma manne wa ɗabi’a ta Allah da kuma muradin yin abin da Allah ya ce yana da kyau ko kuma marar kyau. Wani bincike da aka yi ya nuna cewa irin wannan tsoron shi ne “kasancewa da halin da ya dace wurin Allah, wanda yake sa a nuna hali mai kyau da kuma guje wa kowane irin mugunta.” Kalmar Allah ta gaya mana daidai da ta ce: “Tsoron Ubangiji mafarin hikima ne.”—Misalai 9:10.
3 Hakika, tsoron Allah ya ƙunshi ayyukan mutane masu yawa. An haɗa shi da hikima, tare da farin ciki, salama, ni’ima, tsawon rai, bege, gaskatawa, da kuma aminci. (Zabura 2:11; Misalai 1:7; 10:27; 14:26; 22:4; 23:17, 18 Ayukan Manzanni 9:31) Tsoro yana da nasaba da bangaskiya da kuma ƙauna. Hakika, wannan ya ƙunshi dangantakarmu da Allah da kuma ’yan’uwanmu. (Kubawar Shari’a 10:12 Ayuba 6:14 Ibraniyawa 11:7) Tsoron Allah ya haɗa da cikkaken tabbaci cewa Ubanmu na samaniya yana lura da mu kuma a shirye yake ya gafarta mana zunubanmu. (Zabura 130:4) Miyagu waɗanda suka ƙi tuba ne kaɗai ya kamata su yi fargaba.a—Ibraniyawa 10:26-31.
Ka Koyi Jin Tsoron Jehobah
4. Menene zai iya taimakonmu mu “ji tsoron” Jehobah?
4 Tun da yake tsoron Allah na da muhimmanci a wurin tsai da shawara mai kyau da kuma samun albarkar Allah, ta yaya za mu ‘koyi jin tsoron Jehobah’ ta hanyar da ta dace? (Kubawar Shari’a 17:19) An rubuta misalan maza da mata da suka ji tsoron Allah a cikin Nassosi “domin koyarwarmu.” (Romawa 15:4) Don mu fahimci abin da ake nufi da tsoron Allah, bari mu tattauna a kan rayuwar Sarki Dauda na Isra’ila ta dā.
5. Ta yaya ne kiwon tumaki ya koya wa Dauda jin tsoron Jehobah?
5 Jehobah ya ƙi Saul, sarki na farko a Isra’ila, saboda yana jin tsoron mutanensa kuma ba shi da tsoron Allah. (1 Samuila 15:24-26) Akasarin haka, rayuwar Dauda da kuma dangantakarsa da Jehobah sun nuna cewa shi mutum ne mai tsoron Allah. A lokacin da yake yaro, Dauda yakan tafi kiwon tumakin mahaifinsa ko da yaushe. (1 Samuila 16:11) Kiwon da Dauda yake yi har cikin dare ne ya taimake shi ya fahimci tsoron Allah. Ko da yake ya fahimci kaɗan ne kawai daga cikin girman sararin samaniya, Dauda ya fahimci amsar da ta dace, wato Allah ne ya cancanci biyayyarmu da kuma girmamawa. “Sa’anda ina lura da sammanka, aikin yatsotsinka, wata kuma da taurari waɗanda ka sanya,” sai ya ce, “Wane abu ne mutum, da ka ke tuna da shi? Ɗan adam kuma da ka ke ziyartarsa?”—Zabura 8:3, 4.
6. Yaya ne Dauda ya ji sa’ad da ya fahimci girman Jehobah?
6 Hakika, sa’ad da Dauda ya kwatanta karancinsa da girman sararin samaniya, hakan ya burge shi. Maimakon ya ba shi tsoro, wannan sanin ya motsa shi ya yabi Jehobah kuma ya ce: “Sammai suna bayyanawar ɗaukakar Allah; sararin sama kuma yana nuna aikin hannuwansa.” (Zabura 19:1) Yadda Dauda ya ɗaukaka Allah ya sa shi ya kusanci Jehobah kuma ya sa Dauda yana son ya koya kuma ya bi kamiltacciyar hanyarsa. Ka yi tunanin yadda Dauda ya ji sa’ad da ya yi waƙa ga Jehobah: “Mai-girma ne kai, mai-aikata al’ajabai: kai kaɗai ne Allah. Ya Ubangiji, ka koya mini tafarkinka; ni kuwa in yi tafiya cikin gaskiyarka: ka daidaita zuciyata ta ji tsoron sunanka.”—Zabura 86:10, 11.
7. Ta yaya ne tsoron Allah ya taimaki Dauda ya yi faɗa da Goliyat?
7 Sa’ad da Filistiyawa suka kai wa Isra’ila hari, Goliyat mai tsawon kusan mita uku, ya tsokani Isra’ilawa yana cewa: ‘Ku zaɓi mutum na wajenku shi gangaro wurina! Idan ya ci nasara, za mu zama bayinku.’ (1 Samuila 17:4-10) Saul da dukan sojojinsa sun ji tsoro, amma ban da Dauda. Dauda ya sani cewa komin ƙarfin mutum, Jehobah ne ya kamata a ji tsoronsa, ba mutum ba. Dauda ya cewa Goliyat: “Na zo wurinka cikin sunan Ubangiji mai runduna,. . . dukan taron jama’an nan kuma su sani Ubangiji yana ceto ba da takobi da māshi ba: gama yaƙi na Ubangiji ne.” Da majajjawarsa da dutse ɗaya, tare da taimakon Jehobah ne Dauda ya kashe Goliyat.—1 Samuila 17:45-47.
8. Menene misalan Littafi Mai Tsarki suka koya mana game da masu tsoron Allah?
8 Mai yiwuwa muna fuskantar tangarɗa mai tsanani ko abokan gaba kamar waɗanda Dauda ya fuskanta. Me ya kamata mu yi? Da tsoron Allah za mu iya samun nasara kamar yadda Dauda da kuma waɗansu amintattu a dā suka yi. Tsoron Allah zai sha kan tsoron mutum. Nehemiya bawan Allah mai aminci ya umurci ’yan’uwansa Isra’ilawa, waɗanda suke cikin matsi daga hannun ’yan hamayya: “Kada ku ji tsoronsu, ku tuna da Ubangiji, wanda shi ke mai-girma, mai-ban razana.” (Nehemiah 4:14) Da taimakon Jehobah, Dauda da Nehemiya da kuma waɗansu amintattun bayin Allah sun yi nasara ta wurin cika aikin da Allah ya ba su. Da tsoron Allah, za mu iya yin nasara.
Fuskantar Matsaloli da Tsoron Allah
9. A wane irin yanayi ne Dauda ya nuna cewa yana tsoron Allah?
9 Bayan da Dauda ya kashe Goliath, Jehobah ya ba shi ƙarin nasarori. Saboda haka, da farko Saul mai kishi ya yi dabarar yadda zai kashe Dauda, a ƙarshe kuma ya kawo sojoji don su kashe shi. Ko da yake Jehobah ya tabbatar wa Dauda cewa zai zama sarki, Dauda ya gudu na shekaru kuma yana faɗa, sa’annan yana jiran ranar da Jehobah zai mai da shi sarki. Da haka, Dauda ya nuna cewa yana tsoron Allah na gaskiya.—1 Samuila 18:9, 11, 17; 24:2.
10. Ta yaya ne Dauda ya nuna cewa yana da tsoron Allah sa’ad da yake fuskantar matsala?
10 A wani lokaci, Dauda ya nemi mafaka a wajen Achish sarkin Filistiya a birnin Gath, garinsu Goliyat. (1 Samuila 21:10-15) Bayin sarkin suka ce Dauda maƙiyin ƙasarsu ne. Menene Dauda ya yi sa’ad da yake cikin wannan mummunar yanayi? Ya buɗe wa Jehobah zuciyarsa a cikin addu’a. (Zabura 56:1-4, 11-13) Ko da yake ya yi kamar ya haukace don ya samu ya gudu, Dauda ya sani cewa Jehobah ne ya cece shi saboda ƙoƙarinsa. Yadda Dauda ya dogara ga Jehobah da zuciya ɗaya ya nuna cewa da gaske Dauda mutum ne mai tsoron Allah.—Zabura 34:4-6, 9-11.
11. Ta yaya za mu nuna tsoron Allah idan muka fuskanci gwaji, kamar yadda Dauda ya yi?
11 Kamar Dauda, za mu iya nuna cewa muna tsoron Allah ta yadda muke dogara ga alkawarinsa na taimaka mana mu jimre wa matsalolin da muke fuskanta. Dauda ya ce: “Ka danƙa ma Ubangiji tafarkinka; ka dogara gareshi, shi kuma za ya tabbatar da shi.” (Zabura 37:5) Wannan ba ya nufin cewa mu miƙa wa Jehobah matsalolinmu ba tare da ƙoƙarin yin abin da za mu iya yi ba, sai dai mu jira Jehobah ya taimake mu. Dauda bai yi addu’a Allah ya taimake shi ba ba tare da ɗaukan mataki ba. Ya yi amfani da ƙarfi da kuma ilimin da Jehobah ya ba shi ya warware matsalolin da yake fuskanta. Duk da haka, Dauda ya sani cewa ƙoƙarin mutum kaɗai ba zai iya ba shi nasara ba. Irin wannan ra’ayin ne ya kamata mu kasance da shi. Bayan mun yi iyakan ƙoƙarinmu, sai mu bar ma Jehobah sauran. Da gaske, ba abin da za mu yi sai dai mu dogara ga Jehobah. Yanzu ne ya kamata kowannenmu ya nuna yana da tsoron Allah. Za mu samu ƙarfafa daga furcin Dauda da ya fito daga zuciyarsa: “Asirin Ubangiji ga masu-tsoronsa ya ke.”—Zabura 25:14.
12. Me ya sa ya kamata mu ɗauki addu’o’inmu da muhimmanci, kuma wane irin hali ne ya kamata mu guje wa?
12 Saboda haka, ya kamata mu ɗauki addu’a da dangantakarmu da Allah abu mai muhimmanci. Idan muka yi addu’a ga Jehobah, dole ne mu “bada gaskiya akwai shi, kuma shi mai-sākawa ne ga waɗanda ke biɗarsa.” (Ibraniyawa 11:6; Yaƙub 1:5-8) Idan kuma ya taimake mu, sai mu “zama masu godiya,” kamar yadda manzo Bulus ya umurce mu. (Kolossiyawa 3:15, 17) Kada mu zama kamar waɗanda wani shafaffen Kirista ya kwatanta haka: “Sun ɗauki Allah kamar wani mai raba abinci ne a sama,” in ji shi. “Idan suna bukatar wani abu, suna son su same shi nan da nan. Kuma idan har sun samu abin da suke so, sai su mance da shi.” Irin wannan halin ba ya nuna tsoron Allah.
Sa’ad da Aka Daina Jin Tsoron Allah
13. A wane lokaci ne Dauda ya nuna cewa bai daraja Dokar Allah ba?
13 Yadda Jehobah ya taimaki Dauda sa’ad da yake cikin wahala ya ƙarfafa shi kuma hakan ya sa ya ci gaba da dogara ga Allah. (Zabura 31:22-24) Duk da haka, sau uku, Dauda ya daina jin tsoron Allah, wanda hakan ya kai ga mugun sakamako. Na farkon ya ƙunshi shirin da ya yi na ɗaukan akwatin alkawari na Jehobah zuwa Urushalima a kan keken shanu maimakon a kafaɗar Lawiyawa, kamar yadda dokar Allah ta ce. Sa’ad da Uzza, wanda yake korar keken shanun ya miƙa hannunsa ya gyara akwatin alkawarin, nan take ya mutu domin “karambaninsa.” Hakika, Uzzah ya yi zunubi mai tsanani, duk da haka, laifin Dauda ne domin bai bi dokar Allah ba, wanda hakan ya jawo irin wannan mummunar sakamako. Tsoron Allah yana nufin yin abubuwa daidai kamar yadda aka shirya.—2 Samuila 6:2-9; Litafin Lissafi 4:15; 7:9.
14. Menene kiɗaya Isra’ilawa da Dauda ya yi, ya jawo?
14 Daga baya, Shaiɗan ya zuga Dauda ya ƙirga dukan maza da za su iya fita yaƙi na Isra’ila. (1 Labarbaru 21:1) Da haka, Dauda ya nuna cewa ya daina jin tsoron Allah, abin da ya yi ya jawo mutuwar Isra’ilawa 70,000. Ko da yake Dauda ya tuba, amma shi da waɗanda suke tare da shi sun sha wahala sosai.—2 Samuila 24:1-16.
15. Menene ya sa Dauda ya faɗa cikin zunubin lalata?
15 Dauda ya nuna cewa ya daina jin tsoron Allah sa’ad da ya yi zina da Beth-sheba, matan Uriya. Dauda ya sani cewa yin zina ko kuma yin sha’awar matar wani ba shi da kyau. (Fitowa 20:14, 17) Matsalar ta soma ne sa’ad da Dauda ya hangi Bath-sheba tana wanka. Da tsoron Allah ya kamata ya motsa Dauda ya kawar da idanunsa da tunaninsa daga wurin Bath-sheba. Maimakon haka, Dauda ya ci gaba da ‘duban mace’ har sha’awarta ya fi ƙarfin tsoronsa ga Allah. (Matta 5:28; 2 Samuila 11:1-4) Dauda ya mance cewa yana sha’ani da Jehobah a dukan abubuwan da yake yi a rayuwansa.—Zabura 139:1-7.
16. Wane sakamako ne Dauda ya shaida saboda zunubinsa?
16 Zina da Dauda ya yi da Bath-sheba ya kai ga samun ɗa. Bayan haka, Jehobah ya aiki annabinsa Natan ya fallasa zunubin Dauda. Bayan ya dawo cikin hayyacinsa, Dauda ya fahimci muhimmancin tsoron Allah sa’annan ya tuba. Ya roƙi Jehobah kada ya yashe shi ko kuma ya ɗauke ruhunsa mai tsarki daga gare shi. (Zabura 51:7, 11) Jehobah ya gafarta wa Dauda kuma ya rage nauyin hukuncinsa, amma bai kawar da duka sakamakon abin da ya yi ba. Ɗan Dauda ya mutu, tun daga nan baƙin ciki da kuma masifa suka faɗa kan iyalinsa. Hakika, wannan sakamako ne na daina jin tsoron Allah!—2 Samuila 12:10-14; 13:10-14; 15:14.
17. Ka yi bayanin sakamakon da ayyukan lalata ke jawowa?
17 A yau, ƙin jin tsoron Allah a batutuwan ɗabi’a zai iya jawo sakamako mai tsanani. Ka yi tunanin baƙin cikin wata matar aure ƙarama sa’ad da ta gane cewa maigidanta Kirista ba shi da aminci a gare ta sa’ad da ya tafi ƙasashen waje. Cike da baƙin ciki, ta fashe da kuka. Yaushe ne za ta kuma amince da maigidanta har ta daraja shi? Za a iya kauce wa irin wannan mummunar sakamako idan aka ji tsoron Allah da gaske.—1 Korinthiyawa 6:18.
Tsoron Allah Zai Hana mu Yin Zunubi
18. Menene manufar Shaiɗan kuma ta yaya yake tafiyar da ayyukansa?
18 Shaiɗan yana taɓarɓare tamanin tarbiyya a duniya, musamman yana so ya lalata Kiristoci na gaskiya. Don ya aikata nufinsa, yana amfani da zuciyarmu da kuma hankalinmu ta wurin azancinmu, musamman idanunmu da kunnenmu. (Afisawa 4:17-19) Yaya za ka yi idan ka gamu ba zato ba tsammani da hotunan lalata, kalami, ko kuma mutane?
19. Ta yaya ne tsoron Allah ya taimaki wani Kirista ya guje wa gwaji?
19 Ka yi la’akari da misalin André,b wani dattijo Kirista, uba ne kuma likita ne a ƙasan Turai. Sa’ad da André yake aikin dare a asibiti, kullum abokan aikinsa mata sai su ajiye masa ’yar takarda mai zanen zuciya, a matashinsa, suna gayyartansa ya yi lalata da su. André bai yarda da gayyartarsu ba. Bugu da ƙari, don ya cire kansa daga irin wannan mummunar mahalli, sai ya nemi aiki a wani wuri. Tsoron Allah hikima ce kuma yakan kai ga albarka, saboda a yau André yana hidima na ɗan lokaci a ofishin reshe na Shaidun Jehobah da ke ƙasarsu.
20, 21. (a) Ta yaya ne tsoron Allah ya taimake mu mu guji yin zunubi? (b) Menene za a tattauna a talifi na gaba?
20 Idan kana tunani marasa kyau a zuciyarka hakan na iya jawo wani irin tunani da zai sa ka yi watsi da dangantakarka da Jehobah ga wani abin da ba ka da iko a kai. (Yaƙub 1:14, 15) Akasarin haka, idan muka ji tsoron Jehobah, za mu kauce wa mutane, wurare, ayyuka, da kuma nishaɗi da za su rage ɗabi’armu. (Misalai 22:3) Kowane irin kunya ko kuma sadaukar da kai da hakan ya ƙunsa kaɗan ne, idan aka gwada da rasa tagomashin Allah. (Matta 5:29, 30) Babu shakka, tsoron Allah ya ƙunshi kauce wa duk wani abin da zai sa mu yi lalata da gangan, ko kuma kallon hotunan tsiraru, maimakon haka mu kawar da idanunmu daga “duban abin banza.” Idan muka yi haka, za mu iya dogara ga Jehobah ya ‘rayar da mu cikin tafarkunsa’ kuma ya ba mu abin da muke bukata.—Zabura 84:11; 119:37.
21 Hakika, tsoron Allah ta gaskiya a koyaushe hikima ce. Kuma shi ne tushen farin ciki na gaskiya. (Zabura 34:9) Za a bayyana wannan a talifi na gaba.
[Hasiya]
a Dubi talifin nan “The Bible’s Viewpoint: How Can You Fear a God of Love?” da ke cikin Awake, fitar 8 ga Janairu, 1998, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
b An sake sunan.
Za Ka Iya Ba da Bayani?
• Wane halin Kirista ne tsoro yake ɗauke da shi?
• Ta yaya ne tsoron Allah ya fi ta mutum?
• Ta yaya za mu nuna cewa mun fahimci abin da addu’a ke ɗauke da shi?
• Ta yaya tsoron Allah zai kiyaye mu daga zunubi?
[Hoto a shafi na 19]
Dauda ya koyi tsoron Allah sa’ad da ya lura da ayyukan Jehobah
[Hotuna a shafi na 20]
Menene za ka yi sa’ad da ka fuskanci gwaji ba zato ba tsammani?