Shawara Mai Kyau Game Da Kasancewa Marar Aure Da Kuma Mai Aure
“Wannan na ke faɗi . . . domin zuwa abin da ya dace, domin ku yi hidimar Ubangiji ba da raba hankali ba.”—1 KOR. 7:35.
1, 2. Me ya sa ya kamata mutum ya bincika gargaɗin Littafi Mai Tsarki game da kasancewa marar aure da mai aure?
YIN cuɗanya da kishiyar jinsi yana yawan jawo farin ciki da takaici da ɓacin rai da kuma alhini. Muna bukatar ja-gorar Allah domin mu bi da waɗannan matsalolin. Akwai dalilai masu yawa da suka sa muke bukatar ja-gorarsa. Alal misali, wasu Kiristoci da suke farin ciki da ba su yi aure ba suna iya ganin cewa iyalinsu da kuma abokansu suna matsa musu su yi aure. Wasu za su so su yi aure amma ba su samu wanda ko wadda ta dace ba. Wasu suna bukatar ja-gora don shirya hakkinsu a matsayin miji ko mata. Kuma Kiristoci marasa aure da ma’aurata suna fuskantar gwajin yin lalata.
2 Ban da yadda wannan batun ya shafi farin cikinmu, ya kuma shafi dangantakarmu da Jehobah Allah. A sura ta 7 ta wasiƙa ta farko da Bulus ya rubuta wa Korintiyawa, ya ba da gargaɗi game da kasancewa marar aure da kuma mai aure. Maƙasudinsa shi ne ya motsa waɗanda suka karanta wasiƙarsa “zuwa abin da ya dace, domin [su] yi hidimar Ubangiji ba da raba hankali ba.” (1 Kor. 7:35) Yayin da kuke yin la’akari da gargaɗinsa a kan waɗannan muhimman batutuwa, ku yi ƙoƙarin ganin yanayinku, ko ku marasa aure ne ko ma’aurata, a matsayin yanayi na bauta wa Jehobah sosai.
Shawara Mai Muhimmanci da Kowane Mutum Yake Yi
3, 4. (a) Ta yaya matsaloli sukan taso a wasu lokatai idan mutane sun cika damuwa game da wani aboki ko ɗan iyalinsu da bai yi aure ba? (b) Yaya gargaɗin Bulus zai taimaka wa mutum ya kasance da ra’ayin da ya dace game da aure?
3 Kamar yadda Yahudawa na ƙarni na farko suke yi, al’adu da yawa a yau suna ɗaukan aure a matsayin abu mai ban sha’awa sosai. Idan wani saurayi ko budurwa sun kai wasu shekaru kuma ba su yi aure ba, abokai da iyalai za su iya so su ba su shawara. Suna iya ce musu su sa ƙwazo wajen neman aboki ko abokiyar aure. Suna iya gaya musu wasu abubuwa game da wani ko wata da za su iya aura. Suna ma iya yin wayo don su sa namijin da ta macen su haɗu a wani wuri. Hakan yana jawo kunya da ɓata dangataka tsakanin abokai da kuma ɓacin rai.
4 Bulus bai taɓa tilasta wa mutane su yi aure ba ko kuma kada su yi aure. (1 Kor. 7:7) Ya gamsu da bauta wa Jehobah ba tare da mata ba, amma ya daraja damar da wasu suke da shi na jin daɗin aure. Kiristoci ɗai-ɗai ma a yau suna da ’yancin zaɓan su yi aure ko kada su yi aure. Kada kowa ya tilasta musu su yi aure.
Yadda Marasa Aure Za Su Yi Nasara
5, 6. Me ya sa Bulus ya ƙarfafa Kiristoci su kasance marasa aure?
5 Wani fitaccen abu a kalamin Bulus ga Korintiyawa shi ne ra’ayinsa mai kyau game da rashin aure. (Karanta 1 Korintiyawa 7:8.) Ko da yake Bulus bai yi aure ba, bai ɗaukaka kansa fiye da waɗanda suka yi aure ba, kamar yadda limaman Kiristendam da ba su yi aure ba suke yi. Maimakon hakan, manzon ya nanata fa’idoji masu yawa da masu shelar bishara da yawa da ba su yi aure ba suke morewa. Mene ne waɗannan fa’idojin?
6 Ya fi kasance wa Kirista marar aure da sauƙi ya karɓi wani hakki a hidimar Jehobah wanda mai aure ba zai iya yi ba. Bulus ya karɓi hakki na musamman a matsayin “manzon Al’ummai.” (Rom. 11:13) A littafin Ayyukan Manzanni sura ta 13 zuwa 20, muna iya karanta game da yadda Bulus ya yi tafiya tare da wasu masu wa’azi a ƙasashen waje don yin wa’azi a sababbin yankuna, kuma sun kafa sababbin ikilisiyoyi. Bulus ya jimre da wahaloli da yawa da yawancinmu ba mu taɓa fuskanta ba. (2 Kor. 11:23-27, 32, 33) Amma Bulus ya yarda ya jimre da dukan waɗannan mawuyacin yanayi sa’ad da yake almajirtarwa, kuma hakan ya sa shi farin ciki matuƙa. (1 Tas. 1:2-7, 9; 2:19) Shin, da zai yiwu ya cim ma dukan waɗannan abubuwan da a ce yana da aure ko kuma iyali? Da ƙyar.
7. Ka ba da misalin wasu Shaidun da ba su yi aure ba waɗanda suka yi amfani da yanayinsu don faɗaɗa al’amuran Mulki.
7 Kiristoci da yawa da ba su yi aure ba suna amfani da yanayinsu yanzu don cim ma abubuwa da yawa a hidimar Mulki. Sara da Limbania, wasu majagaba marasa aure a ƙasar Bolivia, sun ƙaura zuwa wani ƙauyen da aka yi shekaru ba a yi wa’azi ba. Shin, rashin wutar lantarki zai zama musu matsala ne? Sun bayyana: “Babu rediyo da talabijin a ƙauyen, saboda haka, babu abin da yake janye hankalin mutane daga karatu.” Wasu mazauna ƙauyen sun nuna wa majagaban wasu tsofaffin littattafan Shaidun Jehobah da an riga an daina bugawa da daɗewa da suke karantawa. Da yake kusan kowa ya saurare su, ya kasance musu da wuya su yi wa kowa wa’azi a yankin. Wata tsohuwa ta gaya musu: “Babu shakka, ƙarshe ya yi kusa sosai, da yake Shaidun Jehobah sun isa wurinmu.” Ba da daɗewa ba, wasu daga ƙauyen suka soma halartar tarurrukan ikilisiya.
8, 9. (a) Me ya sa Bulus ya ce yana da kyau mutum ya bauta wa Jehobah a matsayin marar aure? (b) Mene ne wasu amfani na bauta wa Jehobah a matsayin marar aure?
8 Hakika, Kiristoci ma’aurata ma suna samun sakamako mai kyau sa’ad da suke wa’azi a yankuna da ba a son saƙonmu. Amma wasu ayyukan da majagaba da ba su yi aure ba suke yi zai kasance wa ma’aurata ko waɗanda suke da yara wuya. Sa’ad da Bulus ya rubuta wasiƙarsa ga ikilisiyoyi, ya san cewa akwai sauran aiki a yin wa’azin bishara. Yana son kowa ya yi farin ciki kamar shi. Saboda haka, ya yi magana sosai game da bauta wa Jehobah a matsayin marar aure.
9 Wata majagaba da ba ta yi aure ba a Amirka ta rubuta: “Wasu mutane sun gaskata cewa waɗanda ba su yi aure ba ba za su iya farin ciki ba. Amma na ga cewa dangantaka ta kud da kud da Jehobah ne ke sa mutum farin ciki matuƙa. Ko da yake rashin aure sadaukarwa ne, ta gaskata cewa idan mutum ya yi amfani da yanayinsa sosai, hakan zai iya kasance baiwa mai kyau.” Game da yin farin ciki, ta rubuta: “Rashin aure ba ya sa mutum baƙin ciki, amma yana kawo farin ciki sosai. Na san cewa da waɗanda ba su yi aure ba da kuma ma’aurata za su iya more tagomashin Jehobah.” A yau, tana hidima da farin ciki a ƙasar da akwai bukata na masu shelar Mulki sosai. Idan ba ka yi aure ba, shin za ka iya yin amfani da ’yancin da kake da shi don daɗa saka hannu sosai a wajen koya wa mutane gaskiya? Idan za ka iya, kasance marar aure zai iya zama kamar baiwa mai tamani daga wurin Jehobah.
Marasa Aure da Suke Son Su Yi Aure
10, 11. Ta yaya Jehobah yake taimaka wa waɗanda suke son su yi aure amma ba su samu aboki ko abokiyar auren da ta dace ba tukun?
10 Bayin Jehobah da yawa da suka jima ba su yi aure ba, suna iya yanki shawarar yin aure. Domin sun san cewa suna bukatar ja-gora, ya kamata su roƙi Jehobah ya taimaka musu su samu aboki ko abokiyar aure da ta dace da za su aura.—Karanta 1 Korintiyawa 7:36.
11 Idan kana son ka auri wata wadda take bauta wa Jehobah da dukan zuciyarta, ka ci gaba da yin addu’a ga Jehobah game da muradinka. (Filib. 4:6, 7) Ko da shekaru nawa ne za ka yi kafin ka yi aure, kada ka karaya. Jehobah ya san abin da kake bukata, kuma idan ka dogara gare shi, zai taimaka maka ka jimre da yanayinka.—Ibran. 13:6.
12. Idan wani ya ce ki aure shi, me ya kamata ki yi la’akari a kai sosai kafin ki yarda?
12 Mene ne za ki yi idan wani wanda ba shi da ruhaniya sosai ko kuma ba Mashaidi ba ne ya ce yana son ya aure ki? Kuma wataƙila kina son ki yi aure. Idan hakan ya faru da ke, ki tuna cewa baƙin cikin da mutum zai samu don zaɓar aboki ko abokiyar auren da bai dace ba ya fi kaɗaitawar da wanda bai yi aure ba zai ji. Kuma zaɓin da ka yi yanzu zai shafi rayuwarka baki ɗaya. (1 Kor. 7:27) Kada ki auri mutum domin kina jin cewa wannan ne kaɗai zarafin da kike da shi na yin aure. Za ki iya yin da-na-sani daga baya.—Karanta 1 Korintiyawa 7:39.
Yin Shirin Aure
13-15. Waɗanne abubuwa da za su iya jawo matsala tsakanin ma’aurata a nan gaba ne ya kamata su tattauna kafin su yi aure?
13 Bulus ya ce ya kamata mutum ya bauta wa Jehobah a matsayin marar aure, amma bai ji cewa ya fi waɗanda suka yi aure daraja ba. Maimakon hakan, hurarren gargaɗinsa yana taimaka wa ma’aurata su fahimci abin da zai faru bayan sun yi aure kuma su zauna a auren.
14 Wasu ma’aurata suna bukatar su daidaita ra’ayinsu game da abin da zai faru a aurensu a nan gaba. Sa’ad da mutane biyu suke zawarci, za su iya ganin cewa ƙaunarsu ta musamman ce. Za su iya ji cewa su kaɗai ne suke jin hakan. Sukan soma aurensu da wannan ra’ayin kuma suna gaskata cewa ba za su taɓa yin baƙin ciki a aurensu ba. Amma irin wannan ra’ayin bai dace ba. Gaskiya ne cewa lokacin soyayya yana iya kawo farin ciki. Amma hakan ba zai iya yin maganin matsaloli da wahalar da dukan ma’aurata suke fuskanta ba.—Karanta 1 Korintiyawa 7:28.a
15 Ango da amarya suna yin mamaki sa’ad da aboki ko abokiyar aurensu na da ra’ayi dabam da nasu. Su biyu suna iya kasancewa da ra’ayi dabam-dabam game da kashe kuɗi da kuma yin nishaɗi, inda za su zauna da kuma lokacin da za su riƙa ziyarar surukansu. Kuma kowannensu yana da halin da ɗayan ba zai so ba. Sa’ad da mutane biyu suke zawarci, za su iya ji cewa ba sa bukatar tattauna abubuwa masu muhimmanci. Amma idan ba su tattauna waɗannan abubuwan ba, za su iya sake tasowa a nan gaba sa’ad da suka yi aure. Ya fi dacewa ma’aurata su tattauna waɗannan abubuwan kafin su yi aure.
16. Me ya sa ya kamata ma’aurata su tsai da shawara a kan yadda za su fuskanci ƙalubale na rayuwar aure?
16 Idan ma’aurata suna son su yi nasara da kuma farin ciki, wajibi ne su kasance da ra’ayi ɗaya game da yadda za su bi da hakkokinsu. Ya kamata su tsai da shawara yadda za su yi renon yaransu da kuma yadda za su kula da iyayensu tsofaffi. Kowacce iyali tana da nata matsaloli, amma bai kamata su ƙyale waɗannan ya raɓa su ba. Idan sun yi biyayya ga gargaɗin Littafi Mai Tsarki, za su magance matsaloli da yawa, su jimre waɗanda suke fuskanta kuma su ci gaba da yin farin ciki tare.—1 Kor. 7:10, 11.
17. Me ya sa ma’aurata suke “tattalin abin da ke na duniya”?
17 Bulus ya ƙara bayyana rayuwar aure a 1 Korintiyawa 7:32-34. (Karanta.) Ma’aurata suna “tattalin abin da ke na duniya,” kamar su abinci da sutura da wurin kwana da wasu batutuwa da ba na ruhaniya ba. Me ya sa hakan? Sa’ad da ɗan’uwa bai yi aure ba tukun, wataƙila yana fita hidima sosai. Amma yanzu da ya zama maigida, ya ga cewa wajibi ne ya yi amfani da wasu cikin lokacinsa da kuzarinsa don ya kula da matarsa kuma ya faranta mata rai. Hakan ma yake da mata ga mijinta. Jehobah ya fahimci wannan bukatar. Ya san cewa mata da miji suna bukatar su sadaukar da wasu lokaci da kuzari da suke amfani da su a hidimar Jehobah sa’ad da ba su yi aure ba tukun.
18. Waɗanne gyare-gyare game da wasanni ne wasu za su bukaci su yi bayan sun yi aure?
18 Amma ga ƙarin darasin da za mu iya koya. Idan ma’aurata za su yi amfani da wasu lokaci da kuzarin da suke amfani da su a hidimar Allah don su kula da kansu, zai dace ma su rage lokacin da suke shaƙatawa sa’ad da ba su yi aure ba. Idan miji ya ci gaba da yin wasanni sosai tare da abokansa kamar a dā, yaya hakan zai shafi matarsa? Ko kuma yaya miji zai ji idan matarsa ta ci gaba da ɓata lokaci sosai tare da ƙawayenta? Mijin ko matar za ta iya jin ta kaɗaita ko ba ta farin ciki kuma ba a ƙaunarta. Za a guji wannan idan ma’aurata sun yi iya ƙoƙarinsu don su ƙarfafa dangantakarsu.—Afis. 5:31.
Jehobah Yana Bukatar Mu Kasance da Tsabta na Ɗabi’a
19, 20. (a) Me ya sa ma’aurata suke bukatar su kāre kansu daga lalata? (b) Wace matsala ce za ta iya faruwa idan ma’aurata suka rabu da kansu na dogon lokaci?
19 Bayin Jehobah sun ƙudurta su kasance da tsabta na ɗabi’a. Wasu sun yanki shawara su yi aure don su guji yin lalata. Amma aure ba ya kāre mutum baki ɗaya daga lalata. A zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, ganuwa tana kāre mutum idan bai fita daga ciki ba. Idan mutum ya fita daga ƙofar sa’ad da ɓarayi da ’yan tawaye suke yawo, za su iya yi masa fashi ko su kashe shi. Hakazalika, ma’aurata suna samun kāriya daga lalata idan suka yi biyayya ga dokar da Jehobah ya kafa game da aure.
20 Bulus ya bayyana wannan dangantaka a 1 Korintiyawa 7:2-5. Ya kamata mata ta yi jama’i da mijinta kaɗai, kuma ya kasance hakan da mijin. Kowannensu yana bukata ya biya ibadar aure, da yake hakan hakkin maigida da uwargida ne. Amma dai, wasu mata ko miji suna kasancewa su kaɗai na dogon lokaci, suna zuwa hutu su kaɗai saboda aikinsu, kuma da hakan ba sa yin ibadar aure. Ka yi la’akari da matsalar da za ta iya tasowa idan saboda “rashin daurewarku,” kuka faɗa cikin tarkon shaiɗan, kuma kuka yi zina. Jehobah yana yi wa magidanta da suke wa iyalinsu tanadi ba tare da sa aurensu cikin haɗari ba albarka.—Zab. 37:25.
Amfanin Bin Shawarar Littafi Mai Tsarki
21. (a) Me ya sa tsai da shawara game kasance marar aure da kuma yin aure yake da wuya? (b) Me ya sa gargaɗin da ke 1 Korintiyawa sura ta 7 yake da amfani?
21 Tsai da shawara game da kasance marasa aure da kuma yin aure yana da wuya sosai. Dukanmu ajizai ne, kuma wannan ne yake jawo matsaloli tsakanin mutane. Ko da Jehobah yana yi wa mutanensa albarka, amma suna iya yin baƙin ciki saboda abin da ke faruwa a rayuwa a wasu lokatai. Idan ka bi umurnin da ke 1 Korintiyawa sura ta 7, za ka iya rage waɗannan matsalolin. Za ka iya faranta wa Jehobah rai, ko ka yi aure ko a’a. (Karanta 1 Korintiyawa 7:37, 38.) Samun amincewar Jehobah ita ce abu mafi kyau da za mu iya cim ma. Za mu iya samun amincewarsa yanzu kuma a nan gaba za mu more rayuwa har abada a aljanna. A lokacin, maza da mata ba za su riƙa samun matsalolin da suke da shi a yau ba.
[Hasiya]
a Ka duba littafin nan Asirin Farinciki na Iyali, babi na 2, sakin layi na 16-19.
Mece ce Amsarka?
• Me ya sa bai kamata a matsa wa wani ya yi aure ba?
• Ta yaya za ka iya yin amfani da lokacinka sosai a matsayinka na bawan Jehobah da bai yi aure ba?
• Ta yaya waɗanda suke zawarci za su iya yin shiri don matsalolin da za su iya tasowa a aure?
• Me ya sa ya kamata ma’aurata su kāre kansu daga lalata?
[Hotona a shafi na 14]
Kiristoci marasa aure da suke saka hannu sosai a hidima suna farin ciki
[Hoto a shafi na 16]
Waɗanne gyare-gyare ne wasu za su bukaci su yi bayan sun yi aure?