TARIHI
Abin da Na Cim Ma a Hidima ta Cikakken Lokaci
Yin bimbini a kan shekaru 65 da na yi ina hidima ta cikakken lokaci ya tabbatar mini cewa na yi rayuwa mai ma’ana sosai. Hakan ba ya nufin cewa abubuwa suna yin tafiya sumul-sumul a kowane lokaci. (Zab. 34:12; 94:19) Amma dai, na yi rayuwa mai ma’ana da kuma albarka sosai!
NA SOMA hidima a Bethel da ke Brooklyn a ranar 7 ga Satumba, 1950. A lokacin, akwai ’yan’uwa maza da mata guda 355 masu shekaru tsakanin 19-80 daga ƙasashe dabam-dabam da suke hidima a Bethel. Da yawa cikinsu Kiristoci shafaffu ne.
YADDA NA SOMA BAUTA WA JEHOBAH
Mahaifiyana ce ta koya mini in riƙa bauta wa Allahnmu mai farin ciki. Ta soma bauta wa Jehobah sa’ad da nake ƙarami. Na yi baftisma a taron da’irar da aka yi a birnin Columbus, jihar Nebraska a Amirka a ranar 1 ga Yuli, 1939, sa’ad da nake ɗan shekara goma. Mu wajen ɗari mun taru a wani majami’a da muka yi haya don mu saurari jawabin da Ɗan’uwa Rutherford ya yi da aka ɗauka a faifai mai jigo “Fascism or Freedom” [“Baƙin Mulki ko ’Yanci”]. Sa’ad da muke kan sauraron jawabin, sai ’yan tawaye suka taru a wajen majami’ar. Bayan haka, sai suka shigo ciki da ƙarfi da yaji kuma suka kore mu daga garin. Mun sake taruwa a gonar wani ɗan’uwa da ke kusa da garin kuma muka ƙarasa sauraron jawabin. Wannan aukuwar ta sa ban taɓa manta kwanan watan da na yi baftisma ba!
Mahaifiyana ta yi ƙoƙari sosai don ta rene ni cikin gaskiya. Ko da yake mahaifina uba ne mai kirki, amma bai cika damun kansa da batun addini ba. Mahaifiyana tare da wasu Shaidu a Ikilisiyar Omaha ne suka ƙarfafa ni sosai.
NA CANJA MAƘASUDINA
Sa’ad da na kusan sauke karatu a makarantar sakandare, na soma tunani a kan abin da zan yi a rayuwa. A lokacin da muka samu dogon hutu daga makaranta, na yi hidimar majagaba na ɗan lokaci tare da tsara na.
An tura wasu ’yan’uwa biyu marasa aure masu suna John Chimiklis da Ted Jaracz da suka sauke karatu a aji na bakwai na Makarantar Gilead hidima a matsayin masu kula masu ziyara a yankinmu. Na yi mamaki cewa shekarunsu tsakanin 20 zuwa 23 ne. A lokacin ni ɗan shekara 18 ne kuma na kusan sauke karatu a makarantar sakandare. Na tuna ranar da Ɗan’uwa Chimiklis ya tambaye ni abin da nake so in yi da rayuwata. Sa’ad da na gaya masa, sai ya ce mini: “Hakika, ka soma hidima ta cikakken lokaci babu ɓata lokaci. Ba ka san abin da hakan zai sa ka cim ma ba.” Wannan shawarar da kuma misalin da suka kafa mini sun taimaka mini sosai. Bayan da na sauke karatu a makaranta, na soma hidimar majagaba a shekara ta 1948.
YADDA NA SOMA HIDIMA A BETHEL
A watan Yuli na shekara ta 1950, ni da iyayena mun halarci taron gunduma na ƙasashe a Filin Wasan Yankee a birnin New York. A wajen taron, na halarci taron ’yan’uwa da suke so su yi hidima a Bethel kuma na cika afilkeshan.
Ko da yake mahaifina bai hana ni yin hidimar majagaba da kuma zama a gidansa ba, amma ya ce in riƙa biyan kuɗin daƙin da nake zama da kuma abincin da nake ci. Saboda haka, wata rana a watan Agusta sa’ad da na fita neman aiki, na fara biya in duba ko ina da wasiƙa a cikin akwatin gidan waya. Sai na ga wasiƙar da aka aiko mini daga Brooklyn. Ɗan’uwa Nathan Knorr ne ya saka hannu a wasiƙar, kuma ya ce: “Mun karɓi afilkeshan da ka saka cewa kana so ka yi hidima a Bethel. Kuma na fahimci cewa kana so ka kasance a Bethel muddar ranka. Saboda haka, zan so ka zo Bethel da ke lamba 124 a unguwar Columbia Heights, a Brooklyn, birnin New York, a ranar 7 ga Satumba, 1950.”
Sa’ad da mahaifi na ya dawo daga aiki a ranar, na gaya masa cewa na samu aiki. Sai ya ce: “Da kyau, a ina ke nan?” Sai na ce masa, “A Bethel da ke Brooklyn kuma za a riƙa biya na dalla 10 a wata.” Hakan ya ɗan ba shi mamaki, amma ya ce mini idan abin da nake so ke nan, in yi shi da ƙwazo. Ba da daɗewa ba bayan wannan lokacin, mahaifina ya yi baftisma a taron gunduma da aka yi a Filin Wasan Yankee a shekara ta 1953!
An kira Ɗan’uwa Alfred Nussrallah da muke hidimar majagaba tare ma zuwa Bethel, kuma mun je wurin tare. Daga baya ya auri Joan kuma su biyu sun je makarantar Gilead, bayan sun sauke karatu, sai aka tura su hidima a ƙasar Lebanon, bayan haka, suka koma yin hidimar mai kula mai ziyara a ƙasar Amirka.
AYYUKAN DA NA YI A BETHEL
Aikin da na fara yi a Bethel shi ne a wurin da ake saka bayan littattafai kuma an ba ni aikin ɗinkin littattafai. Littafi na farko da na yi aiki a kai shi ne What Has Religion Done for Mankind? Bayan na yi aiki na wajen wata takwas a wurin, sai aka tura ni Sashen Kula da Hidima kuma a nan na yi aiki tare da Ɗan’uwa Thomas J. Sullivan. Na ji daɗin yin aiki tare da shi kuma na amfana daga hikima da kuma basirarsa da ya samu don ya yi hidima ta shekaru da yawa a ƙungiyar Jehobah.
Bayan na yi hidima kusan shekaru uku a Sashen Kula da Hidima, sai Ɗan’uwa Max Larson ya gaya mini cewa Ɗan’uwa Knorr yana son gani na. Sai na soma tunani ko na yi wani laifi ne. Hankalina ya kwanta sa’ad da Ɗan’uwa Knorr ya tambaye ni ko ina shirin barin Bethel a nan gaba. Yana neman wani da zai yi aiki na ɗan lokaci a ofishinsa kuma yana so ya ga ko zan iya yin aikin. Na gaya masa cewa ba na shirin barin Bethel. A sakamako, na more gatan yin aiki a ofishinsa har shekara 20.
Ina yawan cewa ba zan taɓa iya biyan kuɗin ilimin da na samu domin na yi aiki tare da Ɗan’uwa Sullivan da Knorr tare da wasu a Bethel, kamar su Milton Henschel da Klaus Jensen da Max Larson da Hugo Riemer da kuma Grant Suiter ba.a
’Yan’uwan da na yi aiki tare da suna tsara aikin da suke yi a hidimar Jehobah daidai wa daida. Ɗan’uwa Knorr ba ya gajiya kuma yana so ya ga ana samun ci gaba a hidimar Mulki. Waɗanda suka yi aiki tare da shi sun ga cewa shi ɗan’uwa ne mai fara’a. Ko da ra’ayinmu sun bambanta a wasu yanayi, muna tattauna abubuwa cikin natsuwa.
Akwai wani lokaci da Ɗan’uwa Knorr ya yi mini magana game da mai da hankali ga ayyukan da ake gani ƙanana ne. Alal misali, ya gaya mini cewa sa’ad da yake kula da sashen maɗaba’a, Ɗan’uwa Rutherford ya kira shi a waya ya ce: “Ɗan’uwa Knorr, sa’ad da ka zo maɗaba’a a lokacin cikin abincin rana, don Allah ka kawo mini magogin fensir. Ina bukatarsu a kan teburina.” Ɗan’uwa Knorr ya ce ya fara zuwa ya karɓo abin kuma ya saka shi cikin aljihunsa. Da rana, sai ya kai abin ofishin Ɗan’uwa Rutherford. Sai Ɗan’uwa Knorr ya gaya mini: “Ina so in riƙa tarar da fensir da aka feƙe a kan teburina kowace safiya.” Na ci gaba da yin hakan cikin shekaru da yawa.
Ɗan’uwa Knorr yana yawan nanata amfanin ƙasa kunne sosai sa’ad da ake gaya mana mu yi wani aiki. Akwai wani lokaci da ya gaya mini na yi wani abu, amma ban saurara sosai ba. A sakamako, na jawo masa matsala sosai. Hakan bai sa ni farin ciki ba, sai na rubuta masa wasiƙa cewa ya gafarce ni kuma zan so a canja mini wajen aiki. Washegari, Ɗan’uwa Knorr ya zo ofishina ya ce, “Robert, na ga wasiƙarka. Ka yi kuskure, na yi maka gyara kuma na tabbata cewa za ka daɗa mai da hankali a nan gaba. Yanzu bari mu koma bakin aiki.” Na yi farin ciki sosai don kirkin da ya yi mini.
BURIN YIN AURE
Bayan na yi hidima ta shekara takwas a Bethel, na so na ci gaba hidimata amma hakan ya canja. A lokacin taron ƙasashe da aka yi a Filin Wasan Yankee da na Polo a shekara ta 1958, na haɗu da wata mai suna Lorraine Brookes, wadda na taɓa haɗuwa da ita a shekara ta 1955 sa’ad da take hidimar majagaba a birnin Montreal, a ƙasar Kanada. Lorraine Brookes tana son hidima ta cikakken lokaci sosai kuma tana a shirye ta je duk inda aka tura ta kuma hakan ya burge ni sosai. Maƙasudinta shi ne ta halarci Makarantar Gilead. Sa’ad da take ’yar shekara 22, an gayyace ta zuwa aji na 27 na makarantar a shekara ta 1956. Bayan sun sauke karatu, an tura ta hidima a ƙasar Brazil. Ni da ita mun sake soma abokantaka a shekara ta 1958 kuma ta yarda ta aure ni. Mun shirya cewa za mu yi aure a shekara ta 1959 kuma idan zai yiwu za mu ci gaba da hidima a ƙasar waje tare.
Sa’ad da na gaya wa Ɗan’uwa Knorr shirin da muka yi, sai ya shawarce ni cewa in jira sai bayan shekara uku sai na yi aure kuma na ci gaba da hidima a Bethel da ke Brooklyn. A lokacin, kafin mutum ya yi aure kuma ya ci gaba da hidima a Bethel, sai ɗaya cikinsu ya yi hidima a Bethel shekara goma ko sama da hakan, ɗayan kuma shekara uku. Saboda haka, Lorraine ta yarda ta yi hidima shekara biyu a Bethel da ke ƙasar Brazil kuma shekara ɗaya a Brooklyn kafin mu yi aure.
A cikin shekara biyu da muke fita zance, muna tattaunawa ta wasiƙa. Yin waya yana da tsada sosai kuma babu i-mail a lokacin. Sa’ad da muka yi aure a ranar 16 ga Satumba, 1961, Ɗan’uwa Knorr ne ya ba da jawabin auren. A gaskiya, shekarun da muka jira sun yi yawa sosai. Amma yanzu idan muka tuna cewa mun yi shekaru hamsin da aure, hakan yana sa mu farin ciki da gamsuwa kuma mun yarda cewa kwalliya ta biya kuɗin sabulu!
GATA A ƘUNGIYAR JEHOBAH
A shekara ta 1964, na samu gatan ziyartar wasu ƙasashe a matsayin dattijo mai ziyartar ofisoshin reshe. A lokacin, mata ba sa bin mazajensu wannan ziyarar. An yi wani gyara a shekara ta 1977, kuma an ce mata su riƙa zuwa wannan ziyarar da mazansu. A shekarar, ni da matata mun je ziyara tare da Ɗan’uwa Grant da matarsa Edith Suiter a ofisoshin reshe da ke ƙasar Jamus da Austria da Girka da Cyprus da Turkiya da kuma Isra’ila. Na ziyarci adadin ƙasashe 70 a faɗin duniya.
A wani ziyarar da muka yi a ƙasar Brazil a shekara ta 1980, mun je birnin Belém inda matata ta taɓa hidima. Mun kuma ziyarci ’yan’uwa a birnin Manaus. Sa’ad da muke ba da jawabi a wani filin wasa, mun ga wasu rukunin mutane da ba sa yin gaisuwa irin ta al’ada na ƙasar. A ƙasar, mata suna gaisuwa ta wajen yin sumba a kumatu kuma maza suna shan hannu. Me ya sa waɗannan mutanen suka ware kansu?
’Yan’uwanmu ne daga rukunin kutare da suke yankin Amazon. Sun ware kansu don kada wasu su kamu da cutar. Amma, sun ratsa zuciyarmu sosai kuma ba za mu taɓa manta da farin ciki da suka yi ba! Hakan ya tabbatar da abin da Jehobah ya ce: “Bayina za su yi rairawa domin murna a zuci.”—Isha. 65:14.
RAYUWA MAI MA’ANA DA KUMA ALBARKA
Ni da matata Lorraine muna yawan yin tunani a kan fiye da shekaru sittin da muka yi muna hidima ga Jehobah. Muna matuƙar farin ciki domin yadda muka yarda Jehobah ya ja-gorance mu ta ƙungiyarsa. Ko da yake ba na iya tafiye-tafiye zuwa ƙasashe dabam-dabam kamar a dā, amma ina taimaka wa Kwamiti Mai Kula da kuma Kwamitin Hidima na Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah. Ina godiya sosai domin na samu gatan saka hannu wajen tallafa wa ’yan’uwa a dukan duniya a wannan hanyar. Muna mamakin ganin yadda matasa maza da mata suke hidima ta cikakken lokaci kuma suna kasancewa da irin halin Ishaya wanda ya ce: “Ga ni; ka aike ni.” (Isha. 6:8) Waɗannan mutanen suna furta kalmomin mai kula mai ziyara wanda ya taɓa ce mini: “Ka soma hidima ta cikakken lokaci babu ɓata lokaci. Ba ka san abin da hakan zai sa ka cim ma ba.”
a Idan kana so ka karanta labaran waɗannan ’yan’uwan, ka duba waɗannan talifofin Hasumiyar Tsaro: Thomas J. Sullivan (15 ga Agusta, 1965); Klaus Jensen (15 ga Oktoba, 1969); Max Larson (1 ga Satumba, 1989); Hugo Riemer (15 ga Satumba, 1964); da kuma Grant Suiter (1 ga Satumba, 1983).