Fansa “Cikakkiyar Kyauta” Ce Daga Jehobah
‘Kowace kyakkyawar baiwa da kowace cikakkiyar kyauta daga . . . wurin Uban ne.’—YAƘ. 1:17.
1. Waɗanne albarka muka samu saboda fansa?
HADAYAR fansa da Yesu ya yi ya sa mutane za su sami albarka sosai, kuma hakan zai sa dukan ‘ya’yan Adamu masu adalci su zama ‘ya’yan Allah. Ƙari ga haka, fansar ta ba mu zarafin yin rayuwa har abada. Ban da sa ‘yan Adam su kasance da bege a nan gaba, mutuwar da Yesu ya yi ta sa mun san gaskiya game da wasu batutuwa masu muhimmanci.—Ibran. 1:8, 9.
2. (a) Waɗanne batutuwa masu muhimmanci ne aka ambata a addu’ar da Yesu ya koya wa almajiransa? (Ka duba hoton da ke shafin nan.) (b) Me za mu bincika a wannan talifin?
2 Shekaru biyu kafin Yesu ya ba da ransa fansa, ya koya wa almajiransa yadda za su yi addu’a. Ya ce: ‘Ubanmu wanda ke cikin sama, a tsarkake sunanka. Mulkinka shi zo. Abin da kake so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda ake yinsa cikin sama.’ (Mat. 6:9, 10) Bari mu tattauna yadda fansar take da alaƙa da tsarkake sunan Allah da Mulkin Allah da kuma cika nufinsa don mu nuna godiyarmu.
“A TSARKAKE SUNANKA”
3. Mene ne sunan Jehobah yake wakilta, kuma ta yaya Shaiɗan ya ɓata wannan suna mai tsarki?
3 A addu’ar da Yesu ya koya wa almajiransa, tsarkake sunan Allah ne abu na farko da ya ambata. Sunan Jehobah yana wakiltar shi da kansa da martabarsa da ikonsa da kuma adalcinsa. A wani wuri kuma Yesu ya kira shi “Uba mai-tsarki.” (Yoh. 17:11) Da yake Jehobah mai tsarki ne, duk ƙa’idodi da dokoki da ya bayar suna da tsarki. Duk da haka, Shaiɗan ya yi ƙarya a gonar Adnin cewa bai kamata Jehobah ya kafa wa ‘yan Adam dokoki ba. Wannan ƙaryar da Shaiɗan ya yi ne ya ɓata sunan Jehobah mai tsarki.—Far. 3:1-5.
4. Ta yaya Yesu ya tsarkake sunan Allah?
4 Yesu yana son sunan Jehobah sosai. (Yoh. 17:25, 26) Shi ya sa ya tsarkake sunan Allah ba kamar Shaiɗan da ya ɓata sunan ba. (Karanta Zabura 40:8-10.) Yesu ya nuna cewa ya dace Jehobah ya kafa mana dokoki ta rayuwar da ya yi a duniya da kuma koyarwarsa. Duk da irin wahalar da Shaiɗan ya sa Yesu ya sha a kan gungumen azaba, Yesu ya kasance da aminci ga Allah. Hakan ya nuna cewa zai yiwu kamiltaccen mutum ya bi dokokin Allah.
5. Ta yaya za mu tsarkake sunan Allah?
5 Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar sunan Jehobah? Ta wurin halinmu. Jehobah yana son mu zama masu tsarki. (Karanta 1 Bitrus 1:15, 16.) Wannan yana nufin cewa za mu bauta wa Jehobah kuma mu riƙa yi masa biyayya da dukan zuciyarmu. Ko da ana tsananta mana, ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu mu riƙa bin ƙa’idodin Jehobah da dokokinsa. Muna sa a ɗaukaka sunan Jehobah ta wurin kasancewa da halaye masu kyau. (Mat. 5:14-16) Idan muka kasance da halaye masu kyau, muna nuna cewa dokokin Jehobah suna da amfani kuma Shaiɗan maƙaryaci ne. Kuma a lokacin da muka yi kuskure, ya kamata mu tuba da gaske kuma mu daina ayyukan da suke ɓata sunan Jehobah.—Zab. 79:9.
6. Ko da yake mu ajizai ne, me ya sa Jehobah yake ganinmu a matsayin masu adalci?
6 Jehobah yana gafarta ma waɗanda suke ba da gaskiya gare shi ta wurin fansar da Yesu ya bayar. Jehobah yana amincewa da waɗanda suke so su bauta masa kuma yana ɗaukansu a matsayin bayinsa. Ƙari ga haka, yana ɗaukan shafaffun Kiristoci a matsayin ‘ya’yansa, “waɗansu tumaki” kuma a matsayin abokansa. (Yoh. 10:16; Rom. 5:1, 2; Yaƙ. 2:21-25) A yanzu ma, fansar tana taimaka mana mu kasance da adalci a gaban Allah kuma mu riƙa tsarkake sunansa.
“MULKINKA SHI ZO”
7. Wane albarka ne za a samu sa’ad da Mulkin Allah ya soma sarauta?
7 Abu na biyu da Yesu ya roƙa a addu’arsa shi ne: “Mulkinka shi zo.” Ta yaya fansa take da alaƙa da Mulkin Allah? Fansar ta taimaka wajen tattara mutane 144,000 da za su yi sarauta a matsayin sarakuna da firistoci da Yesu a sama. (R. Yoh. 5:9, 10; 14:1) Yesu da abokan sarautarsa za su albarkaci mutane masu adalci na tsawon shekara dubu a Mulkin. Za a mai da duniya ta zama aljanna kuma mutane masu aminci za su zama kamiltattu. Kuma a wannan lokacin ne mala’iku da bayin Allah da ke duniya za su zama iyali ɗaya. (R. Yoh. 5:13; 20:6) Yesu zai tattake kan macijin kuma ya kawar da duk matsalolin da Shaiɗan ya jawo.—Far. 3:15.
8. (a) Ta yaya Yesu ya taimaka wa almajiransa su san muhimmancin Mulkin Allah? (b) Ta yaya muke tallafa wa Mulkin a yau?
8 Nan da nan bayan Yesu ya yi baftisma, ya taimaka wa almajiransa su san muhimmancin Mulkin Allah. Yesu ya yi “bishara ta mulkin Allah” a duk wuraren da ya je. (Luk. 4:43) Kafin Yesu ya koma sama, ya gaya wa almajiransa su riƙa yin bishara har “iyakan duniya.” (A. M. 1:6-8) Wa’azin da muke yi yana ba mutane zarafin koyan abubuwa game da fansa kuma su kasance cikin waɗanda za su sami albarka da Mulkin Allah zai kawo. A yau, muna tallafa wa Mulkin Allah ta wurin taimaka wa shafaffu da suka rage a yin wa’azi a duk faɗin duniya.—Mat. 24:14; 25:40.
“ABIN DA KAKE SO, A YI SHI”
9. Me ya sa muke da tabbaci cewa Jehobah zai cika nufinsa ga mutane?
9 Abu na uku da Yesu ya roƙa a addu’arsa shi ne: “Abin da kake so, a yi shi.” Me yake nufi sa’ad da ya yi furucin nan? Da yake Jehobah shi ne mahalicci, idan ya ce wani abu zai faru, kamar abun ya riga ya faru ne. (Isha. 55:11) Tawayen da Shaiɗan ya yi ba zai hana Allah ya cika nufinsa ga ‘yan Adam ba. Tun farko, Jehobah ya so Adamu da Hauwa’u su haifi kamiltattun yara da za su mamaye duniya. (Far. 1:28) Da a ce Adamu da Hauwa’u ba su haifi yara ba, da nufin Jehobah cewa mutane su mamaye duniya bai cika ba. Shi ya sa bayan da Adamu da Hauwa’u suka yi zunubi, Jehobah ya bar su su haifi yara. Ta wurin fansa, Allah ya ba mutanen da suka ba da gaskiya a gare shi zarafin zama kamiltattu kuma su yi rayuwa har abada. Jehobah yana ƙaunar mutane kuma yana son waɗanda suke masa biyayya su yi irin rayuwar da yake so mutane su yi.
10. Ta yaya mutanen da suka mutu za su amfana daga fansar?
10 Biliyoyin mutanen da suka mutu ba tare da sun sami zarafin sanin Jehobah da bauta masa kuma fa? Fansar za ta sa a ta da su kuma Jehobah zai ba su damar koya game da shi kuma su sami rai na har abada. (A. M. 24:15) Jehobah ba ya son mutane su mutu amma su ci gaba da rayuwa. Da yake shi ne Mai ba da rai, zai zama Uba ga dukan waɗanda aka ta da daga mutuwa. (Zab. 36:9) Shi ya sa Yesu ya ce mu riƙa addu’a cewa: ‘Ubanmu wanda ke cikin sama.’ (Mat. 6:9) Jehobah ya ba Yesu ikon ta da matattu. (Yoh. 6:40, 44) Yesu ya ce: “Ni ne tashin matattu, ni ne rai.”—Yoh. 11:25.
11. Mene ne Allah zai yi wa “taro mai girma”?
11 Jehobah ba ya nuna karimci ga mutane kalilan kawai. Yesu ya ce: ‘Gama iyakar wanda za ya aika nufin Allah, shi ne ɗan’uwana, da ‘yar’uwata, da uwata.’ (Mar. 3:35) Nufin Allah ne mutane da yawa daga “taro mai girma” waɗanda suka fito daga al’ummai da al’adu da kuma harsuna su bauta masa. Waɗanda suka ba da gaskiya ga fansar da Yesu ya yi kuma suna yin nufin Allah ne za su iya ce: “Ceto ga Allahnmu ne wanda ya zauna bisa kursiyin, ga Ɗan ragon kuma.”—R. Yoh. 7:9, 10.
12. Ta yaya addu’ar da Yesu ya yi ta nuna nufin Allah ga mutane masu adalci?
12 Addu’ar da Yesu ya koyar ta nuna nufin Jehobah ga mutane masu adalci. Don haka, muna son mu yi iya ƙoƙarinmu don mu tsarkake sunan Jehobah. (Isha. 8:13) Sunan Yesu yana nufin “Jehobah Mai-ceto Ne.” Kuma ceton da muka samu ta wurin fansar yana ɗaukaka sunan Jehobah. Mulkin Allah ne zai sa mutane su sami albarkar da fansar ta tanadar. Babu shakka, addu’ar Yesu ta tabbatar mana cewa babu abin da zai hana Allah ya cika nufinsa.—Zab. 135:6; Isha. 46:9, 10.
KA NUNA WA JEHOBAH KANA GODIYA DON FANSA
13. Mene ne baftismar da muke yi take nufi?
13 Hanya ta musamman da za mu nuna cewa muna godiya don tanadin fansa da Jehobah ya yi mana ita ce ta wurin yin alkawarin bauta wa Jehobah da kuma yin baftisma. Baftismar da muke yi tana nuna cewa mu “na Ubangiji” ne. (Rom. 14:8) Ban da haka ma, hakan yana nuna cewa muna roƙon Allah ya ba mu zuciyar kirki. (1 Bit. 3:21) Jehobah yana amsa addu’ar nan ta wurin yin amfani da jinin da Yesu ya yi amfani da shi don ya fanshe mu kuma mu kasance da tsabta. Muna da tabbaci cewa zai cika dukan alkawarin da ya yi mana.—Rom. 8:32.
14. Me ya sa aka umurce mu mu riƙa ƙaunar maƙwabtanmu?
14 Ta wace hanya ce kuma za mu iya nuna godiya don fansa? Da yake Jehobah yana nuna ƙauna a duk sha’anin da yake yi da mutane, ya kamata dukan bayinsa su riƙa nuna ƙauna. (1 Yoh. 4:8-11) Muna nuna cewa mu ‘ ’ya’yan Ubanmu wanda ke cikin sama’ ne idan muna ƙaunar juna. (Mat. 5:43-48) Dokoki biyu da suka fi muhimmanci su ne mu yi ƙaunar Jehobah da kuma maƙwabtanmu. (Mat. 22:37-40) Hanya ɗaya da muke nuna wannan ƙaunar ita ce ta bin umurnin da aka ba mu cewa mu yi wa’azin Mulkin Allah. Muna nuna ɗaukakar Allah idan muna ƙaunar mutane. Babu shakka, ƙaunar Allah tana “cika a cikinmu” sa’ad da muka yi biyayya da umurnin nan cewa mu riƙa nuna ƙauna musamman ma ga ‘yan’uwanmu.—1 Yoh. 4:12, 20.
FANSA TANA SA MU SAMI ALBARKA DAGA JEHOBAH
15. (a) Wane albarka muke samuwa daga Jehobah yanzu? (b) Wane albarka za mu samu a nan gaba?
15 An gafarta mana zunubanmu, don mun ba da gaskiya ga fansa. Kalmar Allah ta tabbatar mana cewa za a iya “shafe” zunubanmu. (Karanta Ayyukan Manzanni 3:19-21.) Kamar yadda muka tattauna ɗazu, Jehobah ya sa shafaffu sun zama ‘ya’yansa ta wurin fansa. (Rom. 8:15-17) Ya kawo “waɗansu tumaki” zuwa cikin iyalinsa. Bayan mun zama kamiltattu kuma mun tsira daga ƙunci mai girma, za mu zama ‘ya’yan Allah da ke duniya. (Rom. 8:20, 21; R. Yoh. 20:7-9) Jehobah yana son ‘ya’yansa sosai kuma albarkar da fansar za ta kawo babu iyaka. (Ibran. 9:12) Kyautar fansa da Allah ya ba mu za ta dawwama, babu wanda zai iya ƙwacewa daga wurinmu.
16. Ta yaya fansar ta ‘yantar da mu?
16 Babu abin da Shaiɗan zai iya yi don ya hana mutanen da suka ba da gaskiya kasancewa cikin iyalin Allah. Yesu ya zo duniya kuma ya mutu ‘sau ɗaya’ kawai. Don haka, an fanshe mu har abada. (Ibran. 9:24-26) Hakan ya sa an share mana zunubin da muka gāda daga Adamu. Muna nuna godiya saboda fansar Yesu don mun sami ‘yanci daga duniyar nan da Shaiɗan yake iko da ita. Ban da haka ma, ba ma tsoron matattu kuma.—Ibran. 2:14, 15.
17. Ta yaya ka amfana daga ƙaunar da Jehobah yake yi maka?
17 Mun tabbata cewa Allah zai cika alkawarin da ya yi mana. Kamar yadda tsarin halittun da Allah ya yi ba sa canjawa, Jehobah ba zai taɓa karya alkawarinsa ba. (Mal. 3:6) Ban da rai da Allah ya ba mu, ya ba mu wata kyauta kuma. Yana ƙaunarmu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mun sani, mun kuma gaskata ƙaunar da Allah ke yi mana. Allah shi ne ƙauna.” (1 Yoh. 4:16, Littafi Mai Tsarki) Duniya za ta zama aljanna kuma kowane mutum a duniya zai riƙa nuna ƙauna. Bari dukanmu da mala’iku da ke sama mu ce: “Albarka, da ɗaukaka, da hikima, da godiya, da daraja, da iko, da ƙarfi, ga Allahnmu har zuwa zamanun zamanai. Amin.”—R. Yoh. 7:12.