Ka Ci Gaba da Ƙarfafa Dangantakarka da Jehobah!
“Ku yi tafiya bisa ga Ruhu.”—GAL. 5:16.
1, 2. Mene ne wani ɗan’uwa ya lura kuma wane mataki ne ya ɗauka?
WANI mai suna Robert ya yi baftisma sa’ad da yake yaro, amma bai ɗauki bautarsa ga Jehobah da muhimmanci ba. Ya ce: “Ban taɓa yin wani laifi ba, amma da’awar bauta wa Allah kawai nake yi. Idan ka gan ni, za ka ɗauka cewa ni mai ibada ne sosai, don ina halartan dukan taro kuma a wasu watanni ina yin hidimar majagaba na ɗan lokaci. Duk da haka, da akwai abin da ba na yi a rayuwata.”
2 Sai bayan Robert ya yi aure ne ya san matsalarsa. Shi da matarsa sukan yi wasan wasa ƙwaƙwalwa daga Littafi Mai Tsarki. Da yake matarsa mai ibada ce sosai, takan ba da amsoshin daidai. Amma Robert ba ya ba da amsar daidai. Ya ce: “Nakan ji kamar ban san kome ba. Sai na soma tunani, ‘Idan zan cika hakkina na yin shugabanci a iyali, ina bukatar in ɗau mataki.’ ” Wane mataki ne Robert ya ɗauka? Ya ce: “Na yi nazarin Littafi Mai Tsarki sosai, har sai da na soma fahimtar Littafi Mai Tsarki da kyau. Hakan ya sa na zama mai hikima kuma na ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah.”
3. (a) Wane darasi ne za mu iya koya daga abin da ya faru da Robert? (b) Waɗanne tambayoyi masu muhimmanci ne za mu tattauna?
3 Za mu iya koyan darasi mai kyau daga abin da ya faru da Robert. Wataƙila mun san Littafi Mai Tsarki sosai, ko kuma muna halartan taro sosai. Yin abubuwan nan kaɗai ba za su sa mu kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah ba. Wataƙila mun riga mu ƙarfafa dangantakarmu da Allah, amma idan muka sake bincika kanmu za mu lura cewa har yanzu muna bukatar mu ci gaba da kyautata dangantakar. (Filib. 3:16) Don mu ci gaba da ƙarfafa dangantakarmu da Allah, za mu tattauna tambayoyi uku masu muhimmanci a wannan talifin: (1) Ta yaya za mu san ko dangantakarmu da Jehobah tana da ƙarfi sosai? (2) Me za mu yi don mu ƙarfafa dangantakarmu da Allah? (3) Kuma ta yaya hakan yake taimaka mana a rayuwa?
MU BINCIKA KANMU
4. Don su waye ne aka rubuta umurnin da ke Afisawa 4:23, 24?
4 A lokacin da muka soma bauta wa Allah, mun yi canje-canje sosai a rayuwarmu. Kuma ya kamata mu ci gaba da yin hakan bayan baftisma. Shi ya sa aka umurce mu mu ci gaba da ‘sabonta kuma cikin ruhun azancinmu.’ (Afis. 4:23, 24) Da yake mu ajizai ne, muna bukatar mu ci gaba da yin canje-canje a rayuwarmu. Waɗanda suka daɗe suna bauta wa Jehobah ma suna bukatar su ci gaba da kyautata dangantakarsu da shi.—Filib. 3:12, 13.
5. Waɗanne tambayoyi ne za su taimaka mana mu bincika kanmu?
5 Don mu ci gaba da ƙarfafa dangantakarmu da Allah muna bukatar mu bincika kanmu sosai. Ko mu matasa ne ko kuma tsofaffi, kowannenmu zai iya tambayar kansa: ‘Shin na lura cewa na daɗa ƙarfafa dangantakata da Allah? Ina tunani kamar Kristi ne? Halina da kuma abubuwan da nake yi a taro suna nuna cewa ni mai ibada ne sosai? Mene ne abubuwan da nake hira a kansu suke nunawa game da ni? Mene ne yadda nake nazari da irin tufafin da nake sakawa suke nunawa? Ƙari ga haka, yaya nake ji idan aka ba ni shawara? Mene ne zan yi idan na fuskanci gwaji? Na manyanta kuwa?’ (Afis. 4:13) Yin tunanin amsoshin tambayoyin nan zai taimaka mana mu san ko mu masu ibada ne sosai.
6. Mene ne zai taimaka mana mu san ko muna da dangantaka mai kyau da Allah?
6 A wasu lokuta muna bukatar taimakon wasu don mu san ko muna da dangantaka mai kyau da Allah. Manzo Bulus ya ce mutumin da ba shi da dangantaka da Allah, ba ya sanin cewa abin da yake yi yana ɓata wa Allah rai. Amma mutum mai dangantaka mai kyau da Allah ya san ra’ayinsa a kan wasu batutuwa. Kuma ya san cewa bin sha’awoyin banza yana ɓata wa Jehobah rai. (1 Kor. 2:14-16; 3:1-3) Da yake dattawa a ikilisiya suna tunani kamar Kristi, suna saurin lura cewa dangantakar mutum da Allah ya soma tsami. Muna bin shawararsu idan suka lura da hakan kuma suka gaya mana? Ta yin hakan, za mu nuna cewa muna son mu ƙarfafa dangantakarmu da Allah.—M. Wa. 7:5, 9.
KA KASANCE DA DANGANTAKA MAI KYAU DA ALLAH
7. Me ya sa sanin Littafi Mai Tsarki kaɗai ba zai sa mu ƙulla dangantaka mai kyau da Allah ba?
7 Sanin Littafi Mai Tsarki ba ya nufin cewa mutum yana da dangantaka mai kyau da Allah. Sarki Sulemanu ya san Jehobah sosai, har ma an saka littattafan da ya rubuta cikin Littafi Mai Tsarki. Amma daga baya dangantakarsa da Jehobah ta yi tsami, har ya kasa riƙe amincinsa. (1 Sar. 4:29, 30; 11:4-6) Ban da sanin Littafi Mai Tsarki, mene ne muke bukatar mu yi? Muna bukatar mu ci gaba da ƙarfafa dangantakarmu da Allah. (Kol. 2:6, 7) Ta yaya za mu yi hakan?
8, 9. (a) Mene ne zai taimaka mana mu kasance da bangaskiya sosai? (b) Me muke so mu cim ma sa’ad da muke nazari? (Ka duba hoton da ke shafi na 23.)
8 A ƙarni na farko, Bulus ya ƙarfafa Kiristoci su yi ‘ƙoƙari su manyanta.’ (Ibran. 6:1, NW ) Ta yaya za mu bi shawarar Bulus a yau? Hanya ɗaya ita ce ta yin nazarin littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah.” Yin nazarin wannan littafin zai taimaka maka ka san yadda za ka bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a rayuwarka. Idan kuma ka riga ka kammala nazarinsa, akwai wasu littattafan da za ka iya yin nazarinsu don ka zama mai bangaskiya sosai. (Kol. 1:23) Ƙari ga haka, kana bukatar ka yi tunani sosai a kan abin da ka yi nazarinsa kuma ka yi addu’a ga Jehobah ya taimaka maka ka riƙa yin abin da ka koya.
9 Sa’ad da muke nazari da kuma bimbini, burinmu shi ne mu koyi abubuwan da za su taimaka mana mu riƙa yi wa Jehobah biyayya. (Zab. 40:8; 119:97) Ƙari ga haka, za mu koyi guje wa abubuwan da za su iya sa mu kasa ƙulla dangantaka mai kyau da shi.—Tit. 2:11, 12.
10. Mene ne matasa za su yi don su ƙarfafa dangantakarsu da Allah?
10 Idan kai matashi ne, ka kafa maƙasudai a hidimar Jehobah? A duk lokacin da wani ɗan’uwa da ke hidima a Bethel ya halarci taron da’ira, yakan tattauna da matasan da suke son su yi baftisma kafin a soma taron. Yakan tambaye su maƙasudansu. Da yawa suna ba da amsar da ta nuna sun tsara yadda za su bauta wa Jehobah. Wasu sun kafa maƙasudin soma yin hidima ta cikakken lokaci ko kuma su ƙaura zuwa inda ake da bukata. Wasu matasan kuma ba su san yadda za su amsa wannan tambayar ba. Shin hakan yana nufin cewa ba sa son su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah ne? Ka tambayi kanka: ‘Ina bauta wa Jehobah ne don iyayena suna son in yi hakan? Ko kuma ni ne na tsai da shawarar ƙulla dangantaka mai kyau da Allah?’ Hakika, ya kamata dukanmu mu ci gaba da ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah ba matasa kaɗai ba. Yin hakan zai sa mu kasance da bangaskiya sosai.—M. Wa. 12:1, 13.
11. Mene ne za mu yi don mu ƙarfafa dangantakarmu da Allah? (a) Wane misali a Littafi Mai Tsarki ne za mu yi koyi da shi?
11 Idan mun lura cewa muna bukatar mu gyara rayuwarmu, ya kamata mu soma hakan ba tare da ɓata lokaci ba. Domin hakan yana da muhimmanci sosai a rayuwa. (Rom. 8:6-8) Amma hakan ba ya nufin cewa mu zama kamilai. Jehobah zai iya taimaka mana da ruhu mai tsarki. Duk da haka, muna bukata mu saka ƙwazo sosai. A lokacin da wani memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu mai suna John Barr yake bayyana Luka 13:24 ya ce, “Mutane da yawa ba sa saka ƙwazo don su ƙarfafa dangantakarsu.” Muna bukatar mu zama kamar Yakubu da ya yi kokawa da mala’ika har sai da ya sami albarka. (Far. 32:26-28) Ko da yake za mu iya jin daɗin karanta Littafi Mai Tsarki, bai kamata mu ɗauke shi kamar jarida ba. Muna bukatar mu bincika shi sosai don mu koyi abubuwan da za su taimaka mana.
12, 13. (a) Me zai taimaka mana mu bi shawarar da ke Romawa 15:5? (b) Ta yaya misalin Bitrus da shawararsa za su iya taimaka mana? (c) Me za ka yi don ka zama mai ibada sosai? (Ka duba akwatin nan “Yadda Za Ka Ƙarfafa Dangantakarka da Allah.”)
12 Idan muka saka ƙwazo don mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah, ruhu mai tsarki zai taimaka mana mu canja tunaninmu. Kuma a hankali, za mu soma yin tunani kamar Yesu. (Rom. 15:5) Ƙari ga haka, zai taimaka mana mu kawar da sha’awoyin banza, kuma mu kasance da halayen da za su faranta wa Allah rai. (Gal. 5:16, 22, 23) Idan muka lura cewa mun fi mai da hankali ga abin duniya ko kuma sha’awoyinmu, kada mu bar hakan ya sa mu yi sanyin gwiwa. Amma mu ci gaba da roƙon Jehobah ya taimaka mana da ruhu mai tsarki don mu mai da hankali ga yin abin da ya dace. (Luk. 11:13) Akwai lokuta da yawa da manzo Bitrus bai yi tunani kamar Kristi ba. (Mat. 16:22, 23; Luk. 22:34, 54-62; Gal. 2:11-14) Amma hakan bai sa shi sanyin gwiwa ba, kuma Jehobah ya taimaka masa. A hankali Bitrus ya soma tunani kamar Kristi. Mu ma za mu iya yin hakan.
13 Bitrus ya ambata wasu halaye masu kyau da za su iya taimaka mana. (Karanta 2 Bitrus 1:5-8.) Muna bukatar mu ci gaba da “ƙara ba da ƙoƙari” don mu kasance da halaye kamar su kamewa da jimrewa da kuma ƙauna. Hakan zai taimaka mana mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah. Ban da haka, a kowace rana muna bukatar mu tambayi kanmu: ‘Wane hali nake bukatar in kasance da shi yau don in ci gaba da ƙarfafa dangantakata da Allah?’
KA RIƘA BIN ƘA’IDODIN ALLAH KULLUM
14. Ta yaya kasancewa da dangantaka mai kyau da Allah zai shafi rayuwarka?
14 Yin tunani kamar Kristi zai shafi halinmu a makaranta da kuma wurin aiki. Za a ga hakan a yadda muke magana da kuma irin shawarwarin da muke yankewa. Waɗannan abubuwan za su nuna ko mu mabiyan Yesu ne. Da yake muna da dangantaka mai kyau da Jehobah, ba ma son kome ya ɓata dangantakar. Idan muka fuskanci gwaji, ƙaunarmu ga Jehobah za ta sa mu yi tsayin dāka. Ban da haka ma, sa’ad da muke son mu yanke shawara, za mu yi tunani sosai a kan tambayoyin nan: ‘Wace ƙa’idar Littafi Mai Tsarki ce za ta taimaka mini in tsai da shawara mai kyau? Mene ne Kristi zai yi a irin wannan yanayin? Wace shawara ce za ta sa Jehobah farin ciki?’ Ya kamata mu koyar da kanmu mu riƙa tunani hakan. Bari mu tattauna wasu yanayin da ya kamata mu yi tunani sosai a kansu. A kowannensu, za mu ga ƙa’idar Littafi Mai Tsarki da za ta taimaka mana mu tsai da shawarar da ta dace.
15, 16. Ka ba da misalin yadda yin tunani kamar Yesu zai taimaka mana sa’ad da muke tsai da shawarar (a) zaɓan wanda za mu aura. (b) zaɓan abokai.
15 Zaɓan wanda za mu aura. Ƙa’idar tana littafin 2 Korintiyawa 6:14, 15. (Karanta.) Bulus ya nuna bambancin da ke tsakanin mutum mai dangantaka mai kyau da Allah da kuma wanda ba shi da dangantaka mai kyau da Allah. Ra’ayinsu a kan wasu al’amura ya bambanta. Ta yaya wannan ƙa’idar za ta taimaka mana sa’ad da muke son mu zaɓa wanda za mu aura?
16 Zaɓan abokai. Ƙa’idar tana littafin 1 Korintiyawa 15:33. (Karanta.) Mutum mai dangantaka mai kyau da Allah ba zai yi abokantaka da mutane da za su sa shi yin abin da bai dace ba. Wace tambaya ce za ta taimaka maka ka bi wannan ƙa’idar? Alal misali, ta yaya hakan ya shafi dandalin zumunta na Intane? Kuma wane mataki za ka ɗauka idan waɗanda ba ka sani ba suka gayyace ka yin wasa da su a intane?
17-19. Ta yaya ƙulla dangantaka mai kyau da Allah za ta taimaka maka (a) ka ƙi biɗan abubuwa marasa amfani? (b) ka kafa maƙasudai a rayuwarka? (c) ka sasanta saɓani da wasu?
17 Ayyukan da za su ɓata dangantakarmu da Allah. Bulus ya yi wa Kiristoci gargaɗi a Ibraniyawa 6:1. (Karanta.) Mene ne “matattun ayyuka” da muke bukatar mu guje musu? Sun ƙunshi ayyukan da ba za su sa mu ƙarfafa dangantakarmu da Allah ba. Wannan ƙa’idar za ta taimaka mana mu amsa tambayoyin nan: ‘Yin wannan abun zai amfane ni kuwa? Zai dace in yi wannan sana’ar? Me ya sa bai kamata in shiga wata ƙungiyar da take son canja yanayin duniya ba?’
18 Maƙasudanmu. Abin da Yesu ya faɗa sa’ad da yake Huɗuba a kan Dutse zai taimaka mana mu kafa maƙasudai masu kyau. (Mat. 6:33) Mutum da ya ƙulla dangantaka mai kyau da Allah yana sa al’amuran Mulkin Allah a kan gaba. Wannan ƙa’idar za ta taimaka mana mu amsa tambayoyin nan: ‘Shin ya kamata in kafa maƙasudin zuwa jami’a? Zai dace in yi wannan aikin?’
19 Saɓani. Ta yaya shawarar Bulus ga ikilisiyar da ke Roma za ta taimaka mana idan mun sami saɓani da wasu? (Rom. 12:18) Da yake mu mabiyan Kristi ne, muna yin iya ƙoƙarinmu don mu yi ‘zaman lafiya da dukan mutane.’ Amma idan muka sami saɓani da wasu, mene ne za mu yi? Yana mana wuya ne mu sasanta, ko kuwa an san mu da son zaman lafiya?—Yaƙ. 3:18.
20. Me ya sa kake son ka ci gaba da ƙarfafa dangantakarka da Jehobah?
20 Babu shakka, misalan nan sun nuna mana cewa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki yana da kyau. Domin zai taimaka mana mu tsai shawarwarin da za su nuna cewa muna da dangantaka mai kyau da Allah. Idan muka mai da hankali ga yin abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarmu da Allah, za mu riƙa farin ciki kuma mu sami gamsuwa. Robert wanda aka ba da labarinsa ɗazu, ya ce: “Ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah ya taimaka mini. Yanzu na zama miji da mahaifin kirki. Ban da haka, ina da wadar zuci kuma ina farin ciki.” Za mu sami irin wannan albarkar, idan muka ɗauki dangantakarmu da Allah da muhimmanci fiye da kome. Hakan zai sa mu yi farin ciki yanzu kuma a nan gaba mu sami “hakikanin rai.”—1 Tim. 6:19.