Yara da Matasa, Ku Kafa Maƙasudai a Bautarku
Ka “danƙa wa Yahweh ayyukanka, shirye-shiryenka kuwa za su kai ga nasara.”—K. MAG. 16:3.
1-3. (a) Wane ƙalubale ne yara da matasa suke fuskanta, kuma da me za a iya kwatanta wannan? (Ka duba hoton da ke shafi na 25.) (b) Mene ne zai taimaka wa yara da matasa a wannan yanayin?
A CE kana shirin yin tafiya zuwa wani gari mai nisa don ka halarci wani biki na musamman! Don ka kai wurin, kana bukatar ka shiga mota. Sa’ad da ka kai tashar motar, sai ka rikice domin akwai mutane da motoci da yawa. Amma, ka san ainihin wurin da za ka da kuma motar da za ka shiga! Hakika, ba za ka isa wurin da kake son ka je ba idan ka shiga motar da ke zuwa wani wuri dabam!
2 Rayuwa tana kamar yin tafiya kuma yara da matasa suna kamar mutanen da ke tashar mota. A wasu lokuta, suna da zaɓi da yawa da ya kamata su yi kuma hakan na iya rikitar da su. Amma, yin zaɓi zai yi wa matasa sauƙi idan suka zaɓa abin da za su yi tun suna ƙanana. Wane irin zaɓi ne ya kamata su yi?
3 Za a amsa tambayar nan a wannan talifin kuma za a ƙarfafa yara da matasa su mai da hankali ga faranta wa Jehobah rai. Hakan yana nufin cewa za su bi umurnin Jehobah a duk shawarwarin da za su tsai da a rayuwa. Wannan ya ƙunshi irin makaranta da aikin da za su yi da yin aure da haifan yara da dai sauransu. Ƙari ga haka, za su kafa maƙasudai da za su sa su kusaci Jehobah. Babu shakka, Jehobah zai albarkaci yara da matasa da suka mai da hankali ga bautarsu ga Jehobah.—Karanta Karin Magana 16:3.
ME YA SA KUKE BUKATAR KU KAFA MAƘASUDAI?
4. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
4 Yana da kyau ku kafa maƙasudai tun kuna ƙanana. Me ya sa? Za mu tattauna dalilai uku. Na farko da na biyu za su taimaka muku ku ga cewa kafa maƙasudai zai sa ku ƙarfafa dangantakarku da Jehobah. Na uku kuma zai nuna abin da ya sa yake da kyau ku kafa waɗannan maƙasudai tun kuna ƙanana.
5. Wane dalili mafi muhimmanci ne ya sa ya dace yara da matasa su kafa maƙasudai?
5 Dalili mafi muhimmanci da ya sa ya dace yara da matasa su kafa maƙasudai shi ne don su gode wa Jehobah don yadda yake ƙaunarsu da kuma abin da ya yi a madadinsu. Wani marubucin zabura ya ce: “Ya Yahweh, yana da kyau a yi maka godiya . . . Gama ya Yahweh, ka faranta mini rai da aikinka, na yi waƙar farin ciki don ayyukan hannuwanka.” (Zab. 92:1, 4) Ku yi tunanin duk abubuwan da Jehobah ya ba ku. Ya ba ku rai kuma ya sa ku kasance da bangaskiya. Ya ba ku Littafi Mai Tsarki da ikilisiya da kuma begen yin rayuwa har abada. Saboda haka, idan kuka kafa maƙasudai na bauta wa Jehobah, kuna nuna masa cewa kuna godiya don duk abubuwan da ya ba ku kuma hakan yana sa ku kusace shi.
6. (a) Ta yaya kafa maƙasudai yake shafan dangantakarmu da Jehobah? (b) Waɗanne maƙasudai ne za ku iya kafawa tun kuna ƙanana?
6 Dalili na biyu na kafa maƙasudai shi ne domin idan kuna ƙoƙari ku cim ma su, kuna yin aikin nagarta ga Jehobah kuma hakan zai sa ku kusace shi. Manzo Bulus ya ce: “Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai ƙyale ayyukanku da kuka yi ba, da ƙaunar da kuka nuna masa.” (Ibran. 6:10) Ya fi kyau ku kafa maƙasudai tun kuna ƙanana. Alal misali, wata mai suna Christine tana ’yar shekara goma sa’ad da ta tsai da shawara karanta tarihin Shaidu masu aminci da ke littattafanmu. Sa’ad da Toby yake ɗan shekara 12, ya kafa maƙasudin karance Littafi Mai Tsarki kafin ya yi baftisma. Maxim yana shekara 11 kuma ƙanwarsa Noemi ’yar shekara 10 ce sa’ad da suka yi baftisma. Dukansu sun kafa maƙasudin yin hidima a Bethel. Ƙari ga haka, don su cim ma wannan maƙasudin, sun manna fom na masu hidima a Bethel a bangon ɗakinsu. Kai kuma fa? Zai dace ka yi tunanin wasu maƙasudan da za ka kafa kuma ka yi ƙoƙari ka cim ma su!—Karanta Filibiyawa 1:10, 11.
7, 8. (a) Ta yaya kafa maƙasudai yake sa tsai da shawara ya yi sauƙi? (b) Me ya sa wata matashiya ta ƙi zuwa makarantar jami’a?
7 Dalili na uku na kafa maƙasudai shi ne domin zai taimaka muku sa’ad da kuke tsai da shawarwari. Matasa za su tsai da shawara game da irin makaranta ko aikin da za su yi, da kuma wasu batutuwa. Tsai da shawarwari yana kamar zaɓan hanyar da za ka bi sa’ad da ka isa wata mararraba. Muddin ka san hanyar da za ka bi, zaɓan hanyar da ta dace ba zai yi maka wuya ba. Hakazalika, tsai da shawarwari zai yi maka sauƙi idan ka riga ka kafa maƙasudai a rayuwa. Littafin Karin Magana 21:5 ya ce: “Shirye-shirye na mai ƙwazo lallai sukan kai ga yalwata.” Hakika, za ku yi nasara idan kuka kafa maƙasudai masu kyau tun kuna ƙanana. Abin da ya faru ke nan da wata mai suna Damaris sa’ad da take bukatar ta tsai da wata shawara mai muhimmanci a lokacin da take matashiya.
8 Damaris ta ci jarrabawa sa’ad da ta gama makarantar sakandare. Kuma ta sami sukolashif na zuwa makarantar jami’a da zai sa ta zama lauya, amma ta zaɓa ta riƙa yin aiki na ɗan lokaci. Me ya sa? Ta ce: “Na tsai da shawara tun ina ƙarama cewa zan yi hidimar majagaba. Hakan yana nufin cewa zan riƙa aiki na ɗan lokaci. Da a ce na je jami’a da zan sami aikin da za a riƙa biya na albashi mai tsoka. Amma da samun aiki na ɗan lokaci zai yi mini wuya.” Yanzu Damaris ta yi shekara 20 tana hidimar majagaba. Shin tana ganin ta kafa maƙasudi mai kyau kuma ta tsai da shawarar da ta dace? Ta ce: “A wurin da nake aiki, ina tarayya da lauyoyi da yawa. Da a ce na je jami’a da irin aikin da zan riƙa yi ke nan. Amma, da yawa a cikinsu ba sa jin daɗin aikinsu. Shawarar zama majagaba da na tsai da yana sa ni farin ciki sosai a hidimata ga Jehobah.”
9. Me ya sa yara da matasa suka cancanci a yaba musu sosai?
9 Yara da matasa da yawa a ikilisiyoyi da ke faɗin duniya sun cancanci mu yaba musu sosai. Suna mai da hankali ga bautarsu ga Jehobah da kuma kafa maƙasudai. Irin waɗannan yara da matasa suna jin daɗin rayuwarsu kuma suna bin umurnin Jehobah a duk abubuwan da suke yi. Hakan ya ƙunshi makaranta da aiki da kuma iyali. Sulemanu ya ce: Ka “dogara ga Yahweh da dukan zuciyarka . . . A dukan hanyoyin rayuwarka ka girmama shi, shi kuwa zai daidaita hanyoyinka.” (K. Mag. 3:5, 6) Jehobah yana ƙaunar yara da matasa sosai. Suna da tamani a gare shi kuma zai kāre su, ya yi musu ja-goranci kuma ya albarkace su.
KU YI SHIRI DON KU YI WA’AZI DA KYAU
10. (a) Me ya sa ya kamata yin wa’azi ya fi muhimmanci a gare mu? (b) Ta yaya za mu yi wa’azi da kyau?
10 Yara ko matasa da suka mai da hankali ga faranta wa Jehobah rai za su so su gaya wa mutane game da shi. Yesu Kristi ya ce, “dole ne a yi wa dukan al’ummai shelar labarin nan mai daɗi.” (Mar. 13:10) Ya kamata mu sa yin wa’azi a kan gaba domin yana da muhimmanci sosai. Shin zai yiwu ku kafa maƙasudin yin wa’azi a kai a kai? Za ku iya soma hidimar majagaba? Idan ba ka jin daɗin yin wa’azi kuma fa? Ta yaya za ka yi wa’azi da kyau? Abubuwa biyu za su taimaka maka: Ka yi shiri da kyau kuma kada ka ƙi gaya wa mutane abin da ka yi imani da shi. Idan ka yi hakan, za ka soma jin daɗin yin wa’azi sosai.
11, 12. (a) Mene ne yara ko matasa za su yi don su yi wa’azi da kyau? (b) Ta yaya wani matashi ya yi wa’azi da kyau a makaranta?
11 Za ku iya soma da shirya amsar da za ku ba abokan makarantarku. Alal misali, tambayar nan, “Kana Ganin Allah Ya Damu da Wahalar da Muke Sha?” Dandalin jw.org yana ɗauke da talifofin da za su taimaka wa matasa su amsa wannan tambayar. Ka duba KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI > MATASA > UMURNI DON NAZARI > MECECE KOYARWA TA GASKIYA GAME DA ALLAH? (SASHE NA 1). A wurin za ka ga wani umurni don nazari mai jigo “Allah Ya Damu da Wahalar da Muke Sha Kuwa?” Wannan umurni don nazari zai taimake ku sa’ad da kuke shirya amsar da za ku bayar. Yana ɗauke da nassosin da suka bayyana abin da kuka yi imani da shi. Alal misali, Yaƙub 1:13, Farawa 6:5, 6 da kuma 1 Yohanna 4:8. Ta wurin yin amfani da wannan umurni don nazari, za ku shirya amsoshinku.—Karanta 1 Bitrus 3:15.
12 Ku gaya wa abokan makarantarku cewa za su iya shiga dandalin jw.org da kansu. Abin da Luca ya yi ke nan. Akwai wata rana da ake tattaunawa game da addinai dabam-dabam a ajinsu, kuma Luca ya ga cewa littafi da suke amfani da shi ya faɗi abubuwan da ba daidai ba game da Shaidun Jehobah. Ko da yake Luca ya ji tsoro, ya nemi izini daga malaminsa don ya gyara wasu kurakurai da ke littafin, kuma malamin ya yarda. Sai Luca ya bayyana abin da ya yi imani da shi kuma ya nuna wa dukan ajin dandalinmu. Sai malamin ya gaya wa dukan ’yan ajin su kalli bidiyon zanen allo mai jigo Ka Bugi Azzalumi Ba Tare da Damtse Ba. Luca ya yi farin ciki sosai domin ya yi wa’azi a makaranta.
13. Me ya sa bai kamata mu yi sanyin gwiwa ba sa’ad da muke fuskantar matsaloli ba?
13 Kada ku yi sanyin gwiwa sa’ad da kuka fuskanci matsaloli, amma ku ci gaba da ƙoƙari don ku cim ma maƙasudanku. (2 Tim. 4:2) Abin da Katharina ta yi ke nan. Sa’ad da take ’yar shekara 17, ta kafa maƙasudin yi wa dukan abokan aikinta wa’azi. Wani cikinsu ya zage ta sau da yawa, amma hakan bai hana ta ci gaba da wa’azi ba. Halinta ya burge wani abokin aikinta mai suna Hans. A sakamako, sai ya soma karanta littattafanmu da yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Daga baya, sai ya yi baftisma. Amma Katharina ba ta sani ba domin ta riga ta ƙaura daga wurin. Wata rana da Katharina ta halarci taro a Majami’ar Mulki da iyalinta, ta yi mamaki sosai sa’ad da aka gabatar da Hans a matsayin baƙo mai jawabi! Hakan ya faru bayan shekara 13 da ta ƙaura. Ta yi farin ciki cewa ta ci gaba da yi wa abokan aikinta wa’azi duk da ƙalubalen da ta fuskanta!
KADA KU BAR KOME YA RABA HANKALINKU
14, 15. (a) Me ya kamata ku tuna sa’ad da kuke fuskantar matsi? (b) Ta yaya yara da matasa za su guji yin abin da tsararsu suke so?
14 A wannan talifin, an ƙarfafa ku ku mai da hankali ga faranta wa Jehobah rai da kuma kafa maƙasudai. Hakan yana nufin cewa ya kamata ku mai da hankali ga bautarku ga Jehobah. Amma, tsaranku da yawa suna son shaƙatawa kawai. Kuma wataƙila za su gayyace ku ku bi su yin hakan. Nan ba da daɗewa ba, za ku bukaci ku nuna cewa yana da muhimmanci ku cim ma maƙasudanku. Kada ku bar tsararku su sa ku manta da maƙasudan da kuka kafa. Babu shakka, idan kuna tashar mota da aka ambata a farko wannan talifin, ba za ku shiga motar da ke zuwa wurin da ba ku sani ba domin kun ga fasinjojin da ke ciki suna shaƙatawa.
15 Saboda haka, da akwai abubuwa da dama da za ku yi don kada tsararku su rinjaye ku. Alal misali, ku guji yanayin da zai sa ku faɗa cikin matsala. (K. Mag. 22:3) Kuma ku riƙa tuna da mugun sakamakon yin abubuwan da ba su dace ba. (Gal. 6:7) Ƙari ga haka, ku riƙa bin shawara mai kyau. Ku saurari shawarwarin iyayenku da kuma ’yan’uwa da suka manyanta a ikilisiya.—Karanta 1 Bitrus 5:5, 6.
16. Ka ba da labarin da ya nuna amfanin zama mai tawali’u.
16 Wani mai suna Christoph mai tawali’u ne, kuma hakan ya taimaka masa ya bi shawara mai kyau. Ba da daɗewa ba bayan ya yi baftisma, sai ya soma zuwa wurin motsa jiki a kai a kai. Wasu matasa a wurin suka soma ƙarfafa shi ya shiga kulob ɗinsu na yin wasanni. Sai ya je ya nemi shawara daga wani dattijo. Dattijon ya gaya masa ya yi tunanin wasu haɗarurruka da ke tattare da yin hakan, musamman ma don wasan ya ƙunshi yin gasa. Duk da haka, Christoph ya shiga kulob ɗin. Amma da shigewar lokaci, ya ga cewa ana mugunta a wasan kuma yana da haɗari sosai. Ya je ya nemi shawara daga dattawa da yawa kuma suka ba shi shawara daga Littafi Mai Tsarki. Sai ya ce, “Jehobah ya turo mutane da suka ba ni shawara mai kyau, kuma na saurare su, ko da ban bi shawararsu nan da nan ba.” Kana bin shawara mai kyau kuwa?
17, 18. (a) Mene ne Jehobah yake son yara da matasa a yau su yi? (b) Me zai taimaka muku don kada ku yi da-na-sani? Ka ba da misali.
17 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya saurayi, ji daɗin kuruciyarka, bar zuciyarka ta yi farin ciki a kwanakin zama matashinka.” (M. Wa. 11:9) Hakika, Jehobah yana son ku yi farin ciki sa’ad da kuke matasa. A wannan talifin, kun koya cewa wani abu da zai sa ku farin ciki shi ne mai da hankali ga kafa maƙasudai da kuma bin shawarar Jehobah a dukan shirye-shiryenku. Idan kuka soma hakan tun da wuri, Jehobah zai yi muku ja-goranci, zai kāre ku kuma zai albarkace ku. Ku yi tunanin dukan shawarwari masu kyau da yake ba ku kuma ku bi wannan shawarar da ta ce: “Ka tuna da Mahaliccinka a kwanakin kuruciyarka.”—M. Wa. 12:1.
18 Yara suna saurin girma kuma su zama manya. Abin baƙin ciki, da yawa a cikinsu suna yin da-na-sani don sun kafa maƙasudan da ba su dace ba ko kuma ba su kafa maƙasudi ba. Amma, yara da matasan da suka kafa maƙasudai a hidimar Jehobah za su ci gaba da farin ciki har sa’ad da suka tsufa. Abin da ya faru da wata mai suna Mirjana ke nan, wadda ta ƙware sosai a wasanni sa’ad da take matashiya. An gaya mata ta yi wasan Olimfik, amma ta zaɓi ta soma hidimar majagaba na kullum. Yanzu bayan shekara 30, tana hidimar majagaba da mijinta. Ta ce: “Mutanen da suka yi suna, kuma suna da ɗaukaka da iko da kuma arziki ba sa farin ciki da gaske. Amma maƙasudai da suka fi kyau su ne bauta wa Allah da kuma taimaka wa mutane su san shi.”
19. Mene ne amfanin kafa maƙasudai tun muna ƙanana?
19 Yara da matasa da suke cikin ikilisiya sun cancanci a yaba musu sosai domin duk da matsalolin da suke fuskanta, sun mai da hankali ga bautarsu ga Jehobah. Matasa suna yin hakan ta wajen kafa maƙasudai da kuma sa yin wa’azi a kan gaba a rayuwarsu. Ƙari ga haka, ba sa barin kome a wannan duniyar ya raba hankalinsu. Matasa suna da tabbaci cewa Allah yana lura da ayyukansu kuma ’yan’uwa suna ƙaunar su da kuma tallafa musu. Saboda haka, ku dogara ga Jehobah a dukan shirye-shiryenku kuma za ku yi nasara.