DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | EZEKIYEL 1-5
Ezekiyel Ya Yi Shelar Saƙon Allah da Farin Ciki
Jehobah ya ba Ezekiyel takarda a wahayi kuma ya ce ya ci takardar. Mene ne ma’anar wahayin?
2:9–3:2
Ya kamata Ezekiyel ya fahimci Kalmar Allah sosai. Yin bimbini a kan kalmomin da ke cikin littafin zai sosa zuciyarsa kuma zai motsa shi ya yi magana
3:3
Takardar da Ezekiyel ya ci tana da zaƙi domin ya kasance da ra’ayi mai kyau game da aikinsa