TALIFIN NAZARI NA 20
Abin da Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna Ta Ce Zai Faru da Maƙiyan Allah
“Suka tattara sarakunan nan wuri ɗaya, a wurin da ake ce da shi Armageddon.”—R. YAR. 16:16.
WAƘA TA 150 Mu Bi Allah Don Mu Sami Ceto
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1. Mene ne Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna ta bayyana game da mutanen Allah?
LITTAFIN Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna ya nuna cewa Mulkin Allah ya riga ya soma sarauta a sama kuma an kori Shaiɗan daga sama. (R. Yar. 12:1-9) Wannan korar sa da aka yi ya sa aka sami zaman lafiya a sama amma a duniya kuma ya jawo mana matsaloli da yawa, domin Shaiɗan yana fushi da waɗanda suke bauta wa Jehobah da aminci a nan duniya kuma yana kai musu hari.—R. Yar. 12:12, 15, 17.
2. Me zai taimaka mana mu riƙe aminci ga Jehobah?
2 Me zai taimaka mana mu riƙe amincinmu duk da harin da Shaiɗan yake kawo mana? (R. Yar. 13:10) Wani abu da zai taimaka mana shi ne sanin abin da zai faru a nan gaba. Alal misali, a cikin littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna, manzo Yohanna ya kwatanta wasu daga cikin albarkun da za mu mora a nan gaba. Ɗaya daga cikin albarkun nan shi ne za a hallaka maƙiyan Allah. Yanzu bari mu tattauna ko su waye ne maƙiyan Allah, da kuma abin da zai faru da su.
AN YI AMFANI DA ALAMU AN BAYYANA MAƘIYAN ALLAH
3. Waɗanne alamu ne aka yi amfani da su a cikin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna?
3 A aya ta farko na Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna, mun karanta cewa bayanai da ke cikin littafin an nuna su ne ta alamu. (R. Yar. 1:1, New World Translation) An kwatanta maƙiyan Allah a alamance. A littafin an ambaci dabbobi dabam-dabam da suke wakiltar maƙiyan Allah. Alal misali, ya ce akwai “wata dabba tana fitowa daga cikin teku. Dabbar tana da ƙahoni goma, da kuma kawuna bakwai.” (R. Yar. 13:1) Biye da wannan kuma akwai wata dabba da “ta fito daga ƙasa.” Dabbar tana magana kamar dodon nan mai siffar maciji “har ma ta sa wuta ta sauko daga sama ta zuba a ƙasa.” (R. Yar. 13:11-13) Sa’an nan ya ambata dabba na uku wato “wata jar dabba” wadda wata karuwa take zaune a kai. Waɗannan dabbobi uku sun daɗe suna yaƙi da Jehobah da kuma Mulkinsa, don haka yana da muhimmanci mu san su.—R. Yar. 17:1, 3.
4-5. Ta yaya abin da aka rubuta a Daniyel 7:15-17 ya taimaka mana mu fahimci ma’anar alamun nan?
4 Muna bukatar mu san abin da dabbar da kuma karuwar suke wakilta. Hakan zai taimaka mana mu san ko su waye ne maƙiyan Allah. Littafi Mai Tsarki ne zai taimaka mana mu fahimci hakan. An riga an bayyana alamu da yawa da ke littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna a wasu littattafan da ke Littafi Mai Tsarki. Alal misali, annabi Daniyel ya yi mafarki, kuma a mafarkin ya ga ‘manyan dabbobi guda huɗu sun fito daga teku.’ (Dan. 7:1-3) Daniyel ya gaya mana abin da dabbobin suke wakilta. Manyan dabbobin suna wakiltar “sarakuna huɗu” ko kuma gwamnatoci. (Karanta Daniyel 7:15-17.) Wannan bayani ya taimaka mana mu fahimci cewa dabbobi da aka ambata a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna suna wakiltar gwamnatoci.
5 Yanzu bari mu tattauna wasu daga cikin alamun da aka ambata a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna. Yayin da muke hakan, za mu ga yadda Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu fahimci ma’anarsu. Za mu soma da tattauna dabbobin da aka ambata. Da farko, za mu ga abin da suke wakilta. Sa’an nan za mu ga abin da ya faru da dabbobin. A ƙarshe, za mu ga yadda hakan ya shafe mu.
AN BAYYANA KO SU WAYE NE MAƘIYAN ALLAH
6. Mene ne dabba mai kawuna bakwai da aka ambata a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 13:1-4 take wakilta?
6 Mene ne wannan dabbar mai kawuna bakwai take wakilta? (Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 13:1-4.) Mun ga cewa dabbar tana kama da damisa, amma ƙafafunta na kama da na beyar, sa’an nan bakinta kuma kamar na zaki kuma tana da ƙahoni goma. Kamanin wannan dabbar yana kama da dabbobi huɗu da aka ambata a Daniyel sura 7. Amma a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna, dabba ɗaya ce take da kamanin duka dabbobin nan. Wannan dabbar ba ta wakiltar gwamnati ɗaya kawai. An ce tana mulki ne “a kan kowace zuriya, da kabila, da yare, da al’umma.” Don haka, ta fi gwamnatin ƙasa guda kawai. (R. Yar. 13:7) Za mu iya cewa wannan dabbar tana wakiltar dukan gwamnatocin da suke yin iko bisa ’yan Adam daga zamanin dā har zuwa yau.b—M. Wa. 8:9, Littafi Mai Tsarki.
7. Mene ne kowanne cikin kawuna na dabbar nan take wakilta?
7 Mene ne kowane ɗayan kawunan nan yake wakilta? Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna sura 17 ta taimaka mana mu san amsar, domin ta kwatanta siffar dabbar da aka ambata a sura 13. A Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 17:10 mun karanta cewa: “Kawuna bakwai ɗin nan kuma su ne sarakunan nan bakwai, waɗanda biyar daga cikinsu sun faɗi, ɗaya yana nan, ɗayan bai zo ba tukuna. Sa’ad da ya zo kuwa dole ne ya yi mulki na ɗan ƙaramin lokaci kawai.” A cikin dukan gwamnatocin da Shaiɗan ya yi amfani da su an kwatanta bakwai da “kawuna” domin sun kasance da iko sosai. Waɗannan su ne gwamnatocin da suka yi mulki a kan dukan duniya kuma mulkinsu ya shafi bayin Allah. A lokacin da manzo Yohanna yake raye, guda biyar daga cikin gwamnatocin nan sun riga sun yi mulki, gwamnatocin su ne: Masar, Assuriya, Babila, Midiya da Farisa da kuma Girka. Gwamnati na shida wato Roma tana mulki a lokacin da Yohanna ya ga ru’uyar. Wace gwamnati ce za ta zama ta bakwai da za ta yi mulki bisa dukan duniya?
8. Wace gwamnati ce kai na bakwai na dabbar yake wakilta?
8 Kamar yadda za mu gani, annabce-annabcen da ke littafin Daniyel za su taimaka mana mu san ko wane ne wannan kai na bakwai na dabbar nan wanda shi ne na ƙarshe. Wace gwamnati ce take mulki tun lokacin da “ranar Ubangiji” ta soma? (R. Yar. 1:10) Gwamnatin haɗin kai ta Birtaniya da Amirka ne. Don haka, za mu iya cewa ita ce kai na ƙarshe na dabbar nan da aka ambata a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 13:1-4.
9. Mene ne dabba mai “ƙahoni biyu kamar na ɗan rago” take wakilta?
9 An ci gaba da yi mana bayani a sura 13 inda aka ce wannan kai na bakwai, wato mulkin Birtaniya da kuma Amirka yana yin abubuwa kamar dabba mai “ƙahoni biyu kamar na ɗan rago, [wadda] ta kuma yi magana kamar dodon nan mai siffar maciji.” Dabbar “ta yi manyan alamun ban mamaki, har ma ta sa wuta ta sauko daga sama ta zuba a ƙasa a idon kowa.” (R. Yar. 13:11-15) Sura 16 da 19 sun kwatanta wannan dabbar a matsayin “annabin nan na ƙarya.” (R. Yar. 16:13; 19:20) Daniyel ma ya faɗi wani abu makamancin hakan, kuma ya ce gwamnatin Birtaniya da kuma Amirka za su “kawo halakarwa mai ban tsoro.” (Dan. 8:19, 23, 24) Abin da ya faru ke nan a lokacin Yaƙin Duniya na 2, sa’ad da ’yan kimiyyar Amirka da Birtaniya suka haɗa hannu suka ƙirƙiro bam na nukiliya guda biyu da suka jefa wa Jafan. Hakan ne ya kawo ƙarshen yaƙin. Ta wajen ƙera wannan bam, gwamnatin Birtaniya da Amirka “ta sa wuta ta sauko daga sama ta zuba a ƙasa.”
10. Mene ne siffar dabbar take wakilta? (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 13:14, 15; 17:3, 8, 11)
10 Bayan haka, sai aka ambata wata dabba kuma mai kama da dabba mai kawuna bakwai, amma bambancin wannan shi ne cewa dabbar tana da jar kala. An kira ta “siffar ta dabba” kuma an bayyana ta a matsayin sarki na “takwas.”c (Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 13:14, 15; 17:3, 8, 11.) Littafin ya ce wannan “sarkin” ya fito, sai ya daina wanzuwa, daga baya kuma sai ya sake fitowa. Wannan kwatancin ya dace da Majalisar Ɗinkin Duniya sosai wadda take kan gaba wajen goyon bayan gwamnatocin duniya! Da farko ta fito a matsayin tsohuwar Majalisar Ɗinkin Duniya. Sa’an nan a lokacin Yaƙin Duniya na 2 ta daina wanzuwa. Daga baya kuma ta sake fitowa a matsayin Majalisar ɗinkin Duniyar kamar yadda muka san ta a yau.
11. Mene ne dabbobin nan za su yi, kuma me ya sa bai kamata mu ji tsoron su ba?
11 Ta wajen yaɗa farfaganda, waɗannan gwamnatocin suna ƙarfafa mutane su yi adawa da Jehobah da kuma mutanensa. A alamance, za su tattara “dukan sarakunan duniya” zuwa yaƙin Armageddon, wanda shi ne “babbar Ranar nan ta Allah Mai Iko Duka.” (R. Yar. 16:13, 14, 16) Amma bai kamata mu ji tsoron kome ba. Allahnmu mai iko, Jehobah, zai ɗauki mataki nan da nan don ya ceci dukan waɗanda suke goyon bayan mulkinsa.—Ezek. 38:21-23.
12. Mene ne zai faru da dukan dabbobin nan?
12 Me zai faru da dukan dabbobin nan? Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 19:20 ta ce: “Sai aka kama dabbar tare da wannan annabin ƙarya wanda ya yi alamun ban mamaki a gaban dabbar. Ta wurin waɗannan alamun ban mamakin ne ya ruɗe waɗanda suke da lambar wannan dabba, da kuma waɗanda suka yi wa siffarta sujada. Aka kama wannan dabba tare da annabin nan na ƙarya aka jefa su da rai cikin tafkin wuta mai ƙuna da farar wuta mai wari.” Hakan yana nufin cewa za a hallaka su a lokacin da suke mulki kuma ba za su sake tasowa ba.
13. Wace matsala ce gwamnatocin duniyar nan suke jawo wa Kiristoci?
13 Ta yaya abubuwan nan suka shafe mu? A matsayinmu na Kiristoci, wajibi ne mu riƙe amincinmu ga Allah da kuma Mulkinsa. (Yoh. 18:36) Abin da zai taimaka mana mu yi hakan shi ne mu guji saka hannu a siyasa gabaki ɗaya. Amma hakan bai da sauƙi domin gwamnatocin duniya suna so mu goyi bayansu ta wajen abin da muke faɗa da kuma yi. Waɗanda suka yarda suka goyi bayan dabbar za su sami lambar dabbar. (R. Yar. 13:16, 17) Amma duk wanda ya sami wannan lambar zai rasa amincewar Jehobah kuma ba zai sami rai na har abada ba. (R. Yar. 14:9, 10; 20:4) Saboda haka, yana da muhimmanci sosai mu guji saka hannu a batun siyasa ko da gwamnatocin duniya sun matsa mana mu yi hakan!
A ƘARSHE, KARUWAR ZA TA SHA KUNYA
14. Wane abin ban mamaki ne kuma manzo Yohanna ya gani? (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 17:3-5)
14 Manzo Yohanna ya ce “mamaki ya kama” shi ƙwarai domin wani abu da ya gani. Me ke nan? Ya ga wata mace zaune a kan dabbobin nan masu ban tsoro. (R. Yar. 17:1, 2, 6) Matar ita ce “babbar karuwa” da ake kira “Babila Mai Girma” ko kuma Babila Babba. Tana lalata da “sarakunan duniya.”—Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 17:3-5.
15-16. Mene ne Babila Babba take wakilta kuma ta yaya muka san hakan?
15 Wace ce Babila Babba? Wannan macen ba tsarin siyasa na duniya ba ce domin an ce tana lalata da sarakunan duniya. (R. Yar. 18:9) Da yake an ce tana zaune a kan dabbar nan hakan ya nuna cewa tana ƙoƙari ta yi iko da sarakunan duniya. Ƙari ga haka, ba ta wakiltar waɗanda suke ƙarƙashin tsarin kasuwancin duniyar Shaiɗan masu haɗama, domin Littafi Mai Tsarki ya kira su “ ’yan kasuwa.”—R. Yar. 18:11, 15, 16.
16 A cikin Littafi Mai Tsarki, akan yi amfani da kalmar nan “karuwa” idan ana maganar waɗanda suke da’awar cewa suna bauta wa Allah amma suna bautar gumaka ko kuma suna abokantaka da duniyar nan. (1 Tar. 5:25; Yak. 4:4, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Amma waɗanda suke bauta wa Jehobah da aminci Littafi Mai Tsarki ya kira su “masu zaman tsabta” ko kuma masu “tsarki.” (2 Kor. 11:2; R. Yar. 14:4) Babila ta dā ƙasa ce mai ɗaukaka bauta ta ƙarya sosai. Don haka, Babila Babba tana wakiltar dukan ire-iren addinan ƙarya da akwai a yau. Hakika ita ce daular addinin ƙarya.—R. Yar. 17:5, 18; ka duba talifin nan “Mece ce Babila Babba?” a jw.org.
17. Me zai faru da Babila Babba?
17 Me zai faru da Babila Babba? Ga amsar da Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 17:16, 17 suka bayar, sun ce: “Ƙahoni goma da ka gani, su da dabbar za su ƙi ganin wannan karuwa. Za su ƙwace kome da take da shi su kuma bar ta tsirara, za su cinye naman jikinta, su kuma ƙone ta da wuta. Gama Allah ya nufe su su aikata nufinsa.” Hakika Jehobah zai sa ƙasashe su yi amfani da jar dabbar nan wato Majalisar Ɗinkin Duniya, su kai wa dukan addinan ƙarya hari kuma ta hallaka ta gabaki ɗaya.—R. Yar. 18:21-24.
18. Me za mu yi don mu tabbata cewa babu ruwanmu da Babila Babba?
18 Ta yaya abubuwan nan suka shafe mu? Dole ne mu bi “addinin da Allah Uba ya tabbatar mai tsarki kuma mai gaskiya” ne. (Yak. 1:27) Kada mu bi koyarwar ƙarya da bukukuwan masu bautar gumaka da halin lalata da kuma sihiri da Babila Babba take ɗaukakawa! Kuma za mu ci gaba da yi wa mutane gargaɗi su “fito . . . daga cikinta” don kada su saka hannu cikin zunubanta.—R. Yar. 18:4.
HUKUNCIN DA ZA A YI WA BABBAN MAƘIYIN ALLAH
19. Wane ne “jan dodo mai siffar maciji”?
19 Littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna ya kuma yi magana a kan “wani jan dodo mai siffar maciji.” (R. Yar. 12:3) Wannan dodon ya yi faɗa da Yesu da kuma mala’ikunsa. (R. Yar. 12:7-9) Yana kai wa mutanen Allah hari, kuma yana ba da iko ga gwamnatocin ’yan Adam. (R. Yar. 12:17; 13:4) To wane ne dodon? Dodon shi ne “mai siffar maciji . . . na tun dā, wanda shi ne Mugun nan, ko kuma Shaiɗan.” (R. Yar. 12:9; 20:2) Shi ne yake iko a kan dukan sauran maƙiyan Jehobah.
20. Mene ne zai faru da dodo mai siffar macijin?
20 Me zai faru da dodon? Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 20:1-3 sun bayyana cewa wani mala’ika ya kama Shaiɗan kuma ya sa shi a cikin wani rami mai zurfi da ke kamar kurkuku. Sa’ad da yake cikin kurkukun, Shaiɗan ba zai “ƙara ruɗin al’ummai ba sai bayan shekaru dubun nan sun wuce.” A ƙarshe, za a hallaka Shaiɗan da aljanunsa kuma Littafi Mai Tsarki ya kwatanta hakan sa’ad da ya ce an jefa su cikin “tafkin wuta mai ƙuna da farar wuta mai wari.” (R. Yar. 20:10) Ka yi tunanin yadda duniya za ta kasance babu Shaiɗan da aljanunsa. Kowa zai ji daɗi sosai!
21. Me ya sa zai dace mu yi farin ciki don abubuwan da muka karanta a littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna?
21 Sanin ma’anar alamu da ke littafin Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna yana da ban ƙarfafa sosai! Mun gane ko su waye ne maƙiyan Allah kuma mun ga abin da zai faru da su. Hakika ‘mai albarka ne mutumin da yake karanta wannan kalmomin annabci, da waɗanda suke jin wannan kalmomin annabci’! (R. Yar. 1:3) Amma bayan an kawar da gwamnatocin ’yan Adam, wane albarka ne masu aminci za su mora? Za mu tattauna hakan a talifi na ƙarshe na wannan jerin talifofi.
WAƘA TA 23 Jehobah Ya Soma Sarautarsa
a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna ta yi amfani da alamu don ta bayyana mana ko su waye ne maƙiyan Allah. Littafin Daniyel ya taimake mu mu fahimci ko mene ne ma’anar waɗannan alamun. A wannan talifin, za mu tattauna alaƙar da ke tsakanin annabce-annabcen da ke littafin Daniyel da kuma waɗanda ke Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna. Ta hakan, za mu san ko su waye ne maƙiyan Allah. Sa’an nan za mu ga abin da zai faru da su.
b Wani abu kuma da ya nuna cewa wannan dabba mai kawuna bakwai tana wakiltar dukan gwamnatocin da suka fara mulki daga zamanin dā har zuwa yau shi ne cewa tana da “ƙahoni goma.” A Littafi Mai Tsarki, ana yawan yin amfani da lambar nan goma don a nuna cikakken abu.
c Wannan dabbar ba ta da hular sarki a kan ƙahoninta kamar yadda dabba ta farko take da su. (R. Yar. 13:1) Dalilin shi ne, daga cikin sarakuna “bakwai ɗin nan . . . ta fito” kuma su ne suke ba ta iko.—Ka duba talifin nan “Mene ne Jar Dabba da Aka Ambata a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna Sura 17 Take Wakilta?” a dandalin jw.org.