TALIFIN NAZARI NA 47
Kada Ka Bar Kome Ya Raba Ka da Jehobah
“Amma ni, na dogara gare ka, ya Yahweh, na ce, ‘Kai ne Allahna.’”—ZAB. 31:14.
WAƘA TA 122 Mu Tsaya Daram, Babu Tsoro!
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1. Ta yaya muka san cewa Jehobah yana so ya yi kusa da mu?
JEHOBAH ya gayyace mu mu yi kusa da shi. (Yak. 4:8) Yana so ya zama Allahnmu da Ubanmu da kuma Abokinmu. Yana amsa adduꞌoꞌinmu kuma yana taimaka mana a lokacin da muke fuskantar matsaloli. Yana kuma amfani da ƙungiyarsa ya koyar da mu, ya kuma kāre mu. Amma mene ne za mu yi don mu kusace Jehobah?
2. Ta yaya za mu kusace Jehobah?
2 Idan muna yin addu’a, muna kuma karanta Littafi Mai Tsarki da yin bimbini a kan sa, za mu iya kusace Jehobah. Hakan zai sa mu daɗa ƙaunar Jehobah da kuma yi masa godiya. Yana kuma motsa mu mu yi masa biyayya, kuma mu yi masa yabo don ya cancanci hakan. (R. Yar. 4:11) Yayin da muke daɗa sanin Jehobah, za mu daɗa yarda da shi da kuma ƙungiyar da ya tanadar mana don ta taimaka mana.
3. Ta yaya Iblis yake ƙoƙari ya raba mu da Jehobah, amma mene ne zai taimaka mana kada mu bar Allahnmu da kuma ƙungiyarsa? (Zabura 31:13, 14)
3 Iblis yana yin iya ƙoƙarinsa don ya raba mu da Jehobah, musamman a lokacin da muke fuskantar jarrabobi. Ta yaya yake yin hakan? Da sannu a hankali, yana yin ƙoƙari ya sa mu daina yarda da Jehobah da kuma ƙungiyarsa. Amma za mu iya yin nasara a kan Iblis. Idan bangaskiyarmu ga Jehobah tana da ƙarfi, kuma mun amince da shi sosai, ba za mu daina bauta wa Allahnmu ko mu bar ƙungiyarsa ba.—Karanta Zabura 31:13, 14.
4. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
4 A wannan talifin, za mu tattauna jarrabobi uku da za mu iya fuskanta daga waɗanda ba Shaidu ba, kuma kowannensu zai iya sa mu daina yarda da Jehobah da kuma ƙungiyarsa. Ta yaya ne waɗannan jarrabobin za su iya raba mu da Jehobah? Kuma mene ne za mu iya yi don mu kāre kanmu daga dabarun Shaiɗan?
IDAN MUNA FUSKANTAR MATSALOLI
5. Ta yaya wahaloli za su sa mu daina yarda da Jehobah da kuma ƙungiyarsa?
5 A wasu lokuta muna fuskantar matsaloli kamar hamayya daga iyali, ko kuma rashin aiki. Ta yaya waɗannan matsalolin za su iya raba mu da Jehobah ko kuma su sa mu daina yarda da ƙungiyarsa? Idan mun daɗe muna fama da matsaloli, za mu iya yin sanyin gwiwa da baƙin ciki. Shaiɗan zai iya amfani da irin waɗannan yanayoyin don ya sa mu ga kamar Jehobah ba ya ƙaunar mu. Shaiɗan yana so mu yi tunani cewa Jehobah ne da kuma ƙungiyarsa suke sa mu sha wahala. Wani abu makamancin hakan ya faru da Isra’ilawa a Masar. Da farko, sun yarda cewa Jehobah ne ya naɗa Musa da Haruna su cece su daga bauta. (Fit. 4:29-31) Amma daga baya, saꞌad da Firꞌauna ya daɗa tsananta musu, sun ɗora wa Musa da Haruna laifin abin da ke faruwa da su kuma sun ce musu: “Kun sa mana baƙin jini a wurin Firꞌauna da dattawansa. Abin da kuka yi yana kamar kun ɗauki takobi ne kun sa a hannunsu domin su kashe mu.” (Fit. 5:19-21) Sun ɗora wa amintattun bayin Allah laifi, kuma hakan abin baƙin ciki ne! Idan ka daɗe kana fuskantar matsaloli, ta yaya za ka ci gaba da yarda da Jehobah da kuma ƙungiyarsa?
6. Mene ne muka koya daga annabi Habakkuk game da yadda za mu iya jimre matsaloli? (Habakkuk 3:17-19)
6 Ka yi addu’a ga Jehobah da dukan zuciyarka kuma ka dogara gare shi don ya taimaka maka. Annabi Habakkuk ya fuskanci wahaloli. Akwai lokacin da ya yi shakka ko Jehobah ya damu da shi, don haka ya yi addu’a kuma ya gaya wa Jehobah yadda yake ji. Ya ce: “Har yaushe, ya Yahweh, zan yi ta kukan neman taimako, kai kuwa ka ƙi ji? . . . Halaka da tashin hankali suna gabana.” (Hab. 1:2, 3) Jehobah ya amsa adduꞌar bawansa mai aminci. (Hab. 2:2, 3) Bayan da Habakkuk ya yi tunani a kan yadda Jehobah ya ceci mutanensa a dā, sai ya sake yin da farin ciki. Ya kasance da tabbaci cewa Jehobah yana lura da shi kuma zai taimaka masa ya jimre duk wata matsala. (Karanta Habakkuk 3:17-19.) Wane darasi ne za mu iya koya? Idan kana fuskantar matsaloli, ka yi adduꞌa ga Jehobah kuma ka gaya masa yadda kake ji. Ka yi tunanin yadda Jehobah ya taimaka maka a dā. Idan ka yi haka, za ka daɗa dogara gare shi kuma za ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai ba ka ƙarfin jimrewa. Kuma idan ka ga yadda yake taimaka maka, za ka daɗa ba da gaskiya gare shi.
7. Wane raꞌayi ne ɗan’uwan Shirley ya yi ƙoƙari ya cusa mata, kuma me ya taimaka mata ta riƙe bangaskiyarta?
7 Ka ci gaba da yin abubuwan da ke sa ka kusace Jehobah. Abin da ya taimaki wata ꞌyarꞌuwa a Papua New Guinea mai suna Shirley ke nan, saꞌad da ta fuskanci matsaloli.b Iyalin Shirley talakawa ne kuma yana yi musu wuya su sami abinci. Wani danginta ya yi ƙoƙari ya sa ta yi shakkar cewa Jehobah yana tare da ita. Ya gaya mata cewa: “Kin ce ruhu mai tsarki yana taimaka miki, amma ina taimakon? Iyalinku talakawa ne har ila. Kina ɓata lokacinki kina waꞌazi.” Shirley ta ce: “Na tambayi kaina: ‘Shin Allah ya damu da mu da gaske kuwa?’ Sai na yi addu’a ga Jehobah nan da nan kuma na gaya masa abin da ke zuciyata. Na ci gaba da karanta Littafi Mai Tsarki da littattafanmu kuma ban daina waꞌazi da halartan taro ba.” Ba da daɗewa ba, ta gane cewa Jehobah yana lura da ita da iyalinta. Iyalinta ba sa kwana da yunwa kuma suna farin ciki. Shirley ta ce: “Na gane cewa Jehobah yana amsa adduꞌoꞌina.” (1 Tim. 6:6-8) Idan kai ma ka ci gaba da yin abubuwan da za su sa ka kusace Jehobah, ba za ka bar wahaloli ko shakka su raba ka da Jehobah ba.
IDAN ANA TSANANTA WA ꞌYANꞌUWA DA KE JA-GORANCI A ƘUNGIYAR JEHOBAH
8. Mene ne zai iya faruwa da ꞌyanꞌuwa da ke ja-goranci a ƙungiyar Jehobah?
8 Ta wurin yin amfani da kafofin yaɗa labarai da shafuffukan sada zumunta, magabtanmu sukan yaɗa ƙarya game da ꞌyanꞌuwa da ke ja-goranci a ƙungiyar Jehobah. (Zab. 31:13) An kama wasu ꞌyanꞌuwa kuma an zarge su da aikata laifi. ꞌYanꞌuwa a ƙarni na farko sun fuskanci irin wannan yanayin a lokacin da aka kama manzo Bulus kuma an zarge shi da aikata laifi. Me suka yi?
9. Mene ne wasu Kiristoci suka yi a lokacin da manzo Bulus yake kurkuku?
9 Wasu ꞌyanꞌuwa a ƙarni na farko sun daina goyon bayan manzo Bulus a lokacin da aka saka shi a kurkuku a Roma. (2 Tim. 1:8, 15) Me ya sa? Shin suna jin kunyar manzo Bulus ne domin mutane suna yi masa kallon mai aikata laifi? (2 Tim. 2:8, 9) Ko kuma suna jin tsoro don kada su ma a tsananta musu ne? Ko da wane dalili ne ya sa suka yi hakan, ka yi tunanin yadda Bulus ya ji da yake ya jimre matsaloli da yawa kuma ya sa ransa a haɗari domin su. (A. M. 20:18-21; 2 Kor. 1:8) Kada mu zama kamar mutanen da suka ƙi su taimaka ma Bulus a lokacin da yake bukatar taimakon su! Me ya kamata mu tuna idan ana tsananta wa ꞌyanꞌuwa da ke ja-goranci?
10. Mene ne ya kamata mu tuna idan ana tsananta ma ꞌyanꞌuwan da ke ja-goranci?
10 Ka tuna dalilin da ya sa ake tsananta mana da kuma wanda yake sa a tsananta mana. Timoti na biyu sura 3:12 ta ce: “Duk wanda yake so ya yi rayuwa irin hali na Allah a cikin Almasihu Yesu zai sha tsanani.” Don haka, kada mu yi mamaki cewa masu ja-goranci ne Shaiɗan ya fi kai wa hari. Burinsa shi ne ya sa ꞌyanꞌuwan nan su daina kasancewa da aminci kuma ya tsoratar da mu.—1 Bit. 5:8.
11. Mene ne muka koya daga misalin Onesiforus? (2 Timoti 1:16-18)
11 Ka ci gaba da taimaka ma ꞌyanꞌuwan da ke ja-goranci kuma kada ka guje su. (Karanta 2 Timoti 1:16-18.) Wani Kirista a ƙarni na farko mai suna Onesiforus bai yi abin da sauran ꞌyanꞌuwan suka yi a lokacin da aka sa Bulus a kurkuku ba. “Bai ji kunya wai [Bulus] ɗan kurkuku ba ne.” A maimakon haka, Onesiforus ya nemi Bulus kuma da ya same shi, ya yi iya ƙoƙarinsa ya taimaka wa Bulus. Ta yin hakan, Onesiforus ya sa ransa a cikin haɗari. Wane darasi ne za mu koya daga hakan? Bai kamata mu bar tsoron mutum ya hana mu taimaka ma ꞌyanꞌuwanmu da ake tsananta musu ba. A maimakon haka, ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu mu kāre su kuma mu tallafa musu. (K. Mag. 17:17) Suna bukatar mu nuna musu ƙauna da kuma goyon baya.
12. Mene ne muka koya daga ꞌyanꞌuwanmu maza da mata da ke Rasha?
12 Ka yi tunanin yadda ꞌyanꞌuwanmu maza da mata da ke Rasha suke taimaka wa ꞌyanꞌuwansu masu bi da ke kurkuku. Idan ana yi ma wasunsu shariꞌa, ꞌyanꞌuwansu maza da mata da yawa sukan je kotun don su ƙarfafa su. Wane darasi ne za mu iya koya daga hakan? Idan aka yi ƙarya a kan ꞌyanꞌuwanmu da ke ja-goranci ko aka kama su ko kuma ana tsananta musu, kada ku ji tsoro. Ku yi adduꞌa a madadin su, ku lura da iyalansu kuma ku nemi wasu hanyoyi da za ku iya taimaka musu.—A. M. 12:5; 2 Kor. 1:10, 11.
IDAN ANA MANA BAꞌA
13. Ta yaya baꞌa za ta iya sa mu daina yarda da Jehobah da kuma ƙungiyarsa?
13 Danginmu da ba Shaidu ba, ko abokan aikinmu ko abokan makarantarmu za su iya yi mana baꞌa don muna waꞌazi ko kuma don muna bin dokokin Jehobah. (1 Bit. 4:4) Suna iya cewa: “Ina jin daɗin tarayya da kai, amma addininku yana da tsattsaurar raꞌayi kuma tsohon yayi ne.” Wasu za su iya sūkar mu don yadda muke bi da waɗanda aka yi musu yankan zumunci, kuma su ce: “Ai ku ba kwa ƙaunar mutane.” Maganganu kamar haka za su iya sa mu yi shakkar ko dokokin Jehobah daidai ne, kuma mu tambayi kanmu: ‘Jehobah yana so in yi abin da ya fi ƙarfina ne? Ƙungiyarsa tana hana mu sakewa ne?’ Idan kana fuskantar irin wannan yanayin, ta yaya za ka ci gaba da bin Jehobah da kuma ƙungiyarsa?
14. Mene ne ya kamata mu yi idan mutane suka yi mana baꞌa domin muna bin ƙaꞌidodin Jehobah? (Zabura 119:50-52)
14 Ka ƙudura cewa za ka ci gaba da yin abin da Jehobah yake so. Ayuba mutum ne da ya ci gaba da bin dokokin Jehobah duk da cewa an yi masa baꞌa. Ɗaya daga cikin abokan Ayuba ya yi ƙoƙari ya sa Ayuba ya ɗauka cewa Jehobah bai damu da amincinsa. (Ayu. 4:17, 18; 22:3) Amma Ayuba ya ƙi ya yarda da ƙarairayin. Ya san cewa ƙa’idodin da Jehobah ya kafa game da abu mai kyau da marar kyau daidai ne kuma ya ƙudura cewa zai ci gaba da bin su. Bai yarda kowa ya hana shi riƙe amincinsa ba. (Ayu. 27:5, 6, New World Translation) Wane darasi ne za mu koya daga hakan? Kada ka yarda baꞌa da ake yi maka ya sa ka yi shakkar ƙaꞌidodin Jehobah. Ka yi tunanin abubuwan da suka faru a rayuwarka. Babu shakka sau da yawa ka ga cewa bin ƙa’idodin Jehobah ya amfane ka. Ka ƙudura cewa za ka ci gaba da bin ƙungiyar da ke bin ƙa’idodin Jehobah. Idan ka yi hakan, babu irin baꞌa da za ta sa ka daina bauta wa Jehobah.—Karanta Zabura 119:50-52.
15. Mene ne ya sa aka yi wa Brizit baꞌa?
15 Ka yi laꞌakari da misalin wata ꞌyarꞌuwa a Indiya mai suna Brizit. Iyalinta sun yi mata baꞌa domin addininta. Ba da daɗewa ba bayan an yi mata baftisma a 1997, maigidanta da ba Mashaidi ba ya rasa aikinsa. Don haka, ya yanke shawara cewa shi da Brizit da yaransu su koma zama da iyayensa a wani birni. Amma ba waɗannan ne iyakacin ƙalubalen da Brizit ta fuskanta ba. Da yake mijinta ba ya aiki, ta bukaci ta yi aiki na cikakken lokaci don ta taimaka ma iyalinsu. Ƙari ga haka, ikilisiya mafi kusa da su tana da nisan kilomita 350. Abin baƙin ciki kuma shi ne, iyalin mijinta sun yi hamayya da ita don addininta. Yanayin ya daɗa tsanani har ya sa Brizit da iyalinta sun sake ƙaura. Ba zato ba tsammani, sai mijinta ya rasu. Daga baya, ɗaya daga cikin ꞌyarsu mai shekara 12 ta mutu don ciwon kansa. Bugu da ƙari, iyalin Brizit sun ɗora mata laifi don abubuwan da suka faru. Sun ce da ba ta zama ɗaya daga cikin Shaidun Jehobah ba, da waɗannan abubuwan ba su faru ba. Duk da haka, ta ci gaba da riƙe amincinta ga Jehobah da kuma ƙungiyarsa.
16. Wace albarka ce Brizit ta samu don ta ci gaba da kasancewa tare da Jehobah da kuma ƙungiyarsa?
16 Da yake wurin da Brizit take zama ya yi nisa da ikilisiyar, wani mai kula da daꞌira ya ƙarfafa ta ta riƙa waꞌazi a yankinta kuma ta riƙa halartan taro a gidanta. Da farko ta ɗauka cewa hakan zai yi mata wuya sosai. Amma ta bi shawarar da ɗanꞌuwan ya ba ta. Ta soma wa’azi ga mutane, ta yi ta yin taro a gidanta, kuma ta yi ibada ta iyali tare da yaranta a kai a kai. Wane sakamako ne ta samu? Brizit ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane da yawa kuma da yawa daga cikin ɗalibanta sun yi baftisma. A shekara ta 2005, ta soma hidimar majagaba. Ta sami albarka domin amincinta ga Jehobah da kuma ƙungiyarsa. Yaranta suna bauta ma Jehobah da aminci kuma akwai ikilisiyoyi guda biyu a yankin yanzu! Brizit tana da tabbaci cewa Jehobah ne ya ba ta ƙarfi don ta jimre wa matsalolinta da kuma baꞌa da ta fuskanta a iyalinta.
KA CI GABA DA RIƘE AMINCINKA GA JEHOBAH DA KUMA ƘUNGIYARSA
17. Mene ne ya kamata mu ƙudura niyyar yi?
17 Shaiɗan yana so mu ɗauka cewa Jehobah ba zai taimaka mana ba idan muna fuskantar matsaloli, kuma kasancewa a ƙungiyarsa zai sa rayuwa ta daɗa yi mana wuya. Shaiɗan yana so mu ji tsoro idan an yi ƙarya a kan ꞌyanꞌuwa da ke ja-goranci ko ana tsananta musu ko idan an sa su a cikin kurkuku. Kuma ta wurin sa a yi mana baꞌa, yana ƙoƙarin sa mu daina yarda da Jehobah da kuma ƙungiyarsa. Amma mun san mugayen dabarunsa ƙwarai kuma ba zai iya ruɗe mu ba. (2 Kor. 2:11) Ka ƙudura cewa za ka ƙi ƙarairayin Shaiɗan kuma za ka riƙe amincinka ga Jehobah da kuma ƙungiyarsa. Ka tuna cewa Jehobah ba zai taɓa yashe ka ba. (Zab. 28:7) Don haka, kada ka bar kome ya raba ka da Jehobah!—Rom. 8:35-39.
18. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?
18 A wannan talifin, mun tattauna ƙalubalen da za mu iya fuskanta daga waɗanda ba Shaidu ba. Amma ƙalubale da suka taso daga cikin ikilisiya ma za su iya gwada amincinmu ga Jehobah da kuma ƙungiyarsa. Ta yaya za mu ci nasara a kan irin waɗannan ƙalubalen? Za mu tattauna wannan a talifi na gaba.
WAƘA TA 118 Ka “Ƙara Mana Bangaskiya”
a Kafin mu iya riƙe aminci a wannan lokacin, dole ne mu ci gaba da dogara ga Jehobah da kuma ƙungiyarsa. Iblis yana yin iya ƙoƙarinsa domin ya yi amfani da jarrabobi ya hana mu dogara ga Jehobah. Wannan talifin zai tattauna abubuwa guda uku da Iblis yake amfani da su, da kuma abubuwan da za mu iya yi don mu riƙe amincinmu ga Jehobah da kuma ƙungiyarsa.
b An canja wasu sunayen.