Ƙarin Bayani
a Yawan damuwa na dogon lokaci zai iya shafanmu sosai. Ta yaya Jehobah zai iya taimaka mana? Za mu tattauna yadda Jehobah ya taimaka wa Iliya ya jimre sa’ad da yake baƙin ciki. Misalan wasu a cikin Littafi Mai Tsarki zai nuna mana abin da muke bukatar mu yi don mu sami taimakon Jehobah sa’ad da muke cikin damuwa.