Ƙarin Bayani
a Muna bukatar mu canja halayenmu idan muna so mu cancanci yin baftisma. Talifin nan zai taimake mu mu san abin da ake nufi da halinmu na dā, da dalilin da ya sa muke bukatar mu kawar da shi, da yadda za mu iya yin hakan. A talifi na gaba kuma, za mu tattauna yadda za mu ci gaba da saka sabon hali har bayan mun yi baftisma.