YADDA AKE AMFANI DA GUDUMMAWARKA
Masu Wa’azi a Kasashen Waje “Har Zuwa Iyakar Duniya”
1 GA YUNI, 2021
Yesu ya gaya wa almajiransa cewa: “Za ku zama shaiduna . . . har zuwa iyakar duniya.” (Ayyukan Manzanni 1:8) A yau, Shaidun Jehobah suna yin wannan aikin da kwazo. Amma a wasu wurare a duniya, har da wuraren da mutane sun cika makil, ba a yi wa’azi sosai ba tukun. Wasu kasashe kuma ba su da masu shela da yawa. (Matiyu 9:37, 38) Me muke yi don mu yi wa karin mutane wa’azi?
Domin mu samu mu bi umurnin da Yesu ya ba mu, Kwamitin Hidima na Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah yana aika da masu wa’azi a kasashen waje zuwa wuraren da ake bukatar masu shela. A yanzu haka, akwai masu wa’azi a kasashen waje guda 3,090 a fadin duniya da suke ikilisiyoyin da ake bukatar masu shela sosai.a Yawancin su sun sami horarwa a makarantun da ake koyar da Littafi Mai Tsarki, alal misali, Makarantar Masu Yaɗa Bisharar Mulki. Masu wa’azi a kasashen waje suna shirye su bar gidajensu su kaura zuwa wata kasa. Wadannan masu wa’azin Kiristoci ne da suka manyanta, suna da kwarewa kuma an horar da su sosai. Saboda haka, suna iya wa’azi sosai kuma misalinsu yana karfafa ’yan’uwa da yawa a cikin ikilisiya.
Yadda Ake Taimaka wa Masu Wa’azi a Kasashen Waje
Kowane reshen ofishinmu yana da Sashen Kula da Masu Hidima da yake aiki a karkashin ja-gorancin Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu a kasar don su kula da bukatun masu wa’azi a kasashen waje kamar tanadar musu da gidaje, da kula da lafiyar jikinsu, da kuma ba su dan karamin alawus don a taimaka musu. A shekarar hidima ta 2020, Shaidun Jehobah sun kashe kudin da ya kai kusan dala miliyan 27 wajen kula da masu wa’azi a kasashen waje. Saboda wannan tanadin ne masu wa’azi a kasashen waje suna iya mai da hankali sosai ga yin wa’azi da kuma karfafa ikilisiyoyin da suke.
Ta yaya masu wa’azi a kasashen waje sun sa aikin wa’azi ya sami ci gaba? Wani memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu a Malawi mai suna Frank Madsen ya ce: “Saboda yadda masu wa’azi a kasashen waje suke da karfin zuciya da kuma kwarewa, sun iya taimaka wa ikilisiyoyi su yi wa’azi a wurare masu wuyan wa’azi, kamar yankunan da ke da gidaje da ba a cika barin mutane su shiga, da kuma yankunan da ake wani yare dabam. Kari ga haka, yadda suke saka kwazo a koyan yaren da ake yi a inda suke zama ya sa wasu masu shela su yi koyi da su, kuma suna karfafa matasa su soma hidimar majagaba na kullum. Muna godiya ga Jehobah don masu wa’azi a kasashen waje.”
Wani memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu a wata kasa kuma ya ce: “Masu wa’azi a kasashen waje suna ba da tabbaci cewa bayin Jehobah suna da hadin kai a ko’ina a duniya. Wadanda ba Shaidun Jehobah ba ma suna lura cewa ba ma barin al’adun kasa su raba kanmu. A maimakon haka, muna barin koyarwar Littafi Mai Tsarki ta sa mu zama tsintsiya madaurinki daya.”
A wace hanya ce masu wa’azi a kasashen waje suke taimaka wa masu shela? Wani dan’uwa daga Timor-Leste mai suna Paulo ya ce yana godiya don wasu ma’aurata masu wa’azi a kasashen waje da aka tura zuwa ikilisiyarsu. Ya ce: “Yankinmu yana da zafi sosai, amma duk da cewa ma’auratan sun fito daga kasa da ake sanyi sosai, ba sa taba fasa yin wa’azi saboda zafin rana. Suna zuwa taron fita wa’azi a kullum. Nakan ga suna komawa su ziyarci dalibansu da tsakar rana, a lokacin da ake zafi sosai, da kuma da yamma. Sun taimaka wa mutane da yawa su soma bauta wa Jehobah, har da ni a ciki. Da kwazo da kuma himma, suna amfani da rayuwarsu gaba daya su bauta wa Jehobah kuma hakan yana sa ’yan’uwa a ikilisiya su ma su kara kwazo.”
Wata majagaba a Malawi mai suna Ketti ta ba da labarin yadda wasu ma’aurata masu wa’azi a kasashen waje sun taimaka wa iyalinta. Ta ce: “A lokacin da aka tura ma’auratan zuwa ikilisiyarmu, ni ce kadai nake bauta wa Jehobah a iyalinmu. Amma ma’auratan sun taimaka min sosai kuma sun kusace mu a iyalinmu. Rayuwarsu ta taimaka wa yarana su ga cewa bauta wa Jehobah yana sa farin ciki sosai kuma yana kawo gamsarwa. Hakan ya sa yarana sun yi baftisma har sun soma hidimar majagaba na kullum kuma maigidana ma ya soma halartan taro yanzu.”
Daga ina ne ake samun kudin da ake amfani da shi wajen kula da masu wa’azi a kasashen waje da suke ikilisiyoyin da ake bukatar masu shela sosai? Gudummawar da ake yi don aikinmu a fadin duniya ne ake amfani da ita, kuma da yawa daga cikin gudummawar ta on donate.jw.org ne ake bayarwa. Mun gode muku sosai don yadda kuke bayarwa hannu sake.
a Ana tura masu wa’azi a kasashen waje zuwa ikilisiyoyin da ake bukatar masu wa’azi sosai. Wasu karin masu wa’azi a kasashen waje 1,001 kuma suna hidimar masu kula da da’ira.