WAƘA TA 111
Dalilan da Suke Sa Mu Murna
(Matta 5:12)
1. Muna da dalilan yin murna
Da yawa babu iyaka.
Jama’a daga duk al’umma
Na bauta wa Maɗaukaki.
Gaskiyar da ke Kalmar Allah
Na sa mu yin murna sosai.
Shi ya sa muke nazarin ta
Domin mu kusaci Allah.
Muna da dalilan yin murna
Daga cikin zuciyarmu.
Ko da muna fama da ƙunci,
Jehobah zai taimake mu.
(AMSHI)
Jehobah Allah mun gode,
Duk ayyukanka na da kyau
Da hikimarka da ayyukanka,
Na sa mu yi murna sosai!
2. In mun lura da ayyukanka,
Duniya, sararin sama,
Da kuma sauran halittunka,
Muna miƙa maka yabo.
Mun ƙudurta mu sa a sani
Game da Mulkin Allahnmu.
Da albarkun da za mu samu,
Muna koya wa mutane.
Za mu yi murna har abada,
Za mu ji daɗin rayuwa,
Rayuwa a cikin aljanna
Zai kawo albarka sosai.
(AMSHI)
Jehobah Allah mun gode,
Duk ayyukanka na da kyau
Da hikimarka da ayyukanka,
Na sa mu yi murna sosai!
(Ka kuma duba K. Sha. 16:15; Isha. 12:6; Yoh. 15:11.)