WAƘA TA 67
Mu Yi “Wa’azin Kalmar Allah”
(2 Timotawus 4:2)
1. Allah ya ba mu umurni,
Umurnin da ya kamata mu bi.
Mu riƙa yin shiri a kullum
Domin mu yi wa’azin bishara.
(AMSHI)
Mu yi shela
Mu gaya wa mutane
Da ƙwazo!
Domin ƙarshe na zuwa,
Yi shela
Don su juyo ga Allah,
Yi shela
A ko’ina!
2. Tsanantawa har da ƙunci,
Suna iya hana mu wa’azi.
Ba za mu rufe bakinmu ba,
Ko da mutane sun ƙi saurara.
(AMSHI)
Mu yi shela
Mu gaya wa mutane
Da ƙwazo!
Domin ƙarshe na zuwa,
Yi shela
Don su juyo ga Allah,
Yi shela
A ko’ina!
3. Wasu za su saurare mu,
Za mu koya musu Kalmar Allah.
Bishara na sa su yin bege,
Da kuma tsarkake sunan Allah.
(AMSHI)
Mu yi shela
Mu gaya wa mutane
Da ƙwazo!
Domin ƙarshe na zuwa,
Yi shela
Don su juyo ga Allah,
Yi shela
A ko’ina!
(Ka kuma duba Mat. 10:7; 24:14; A. M. 10:42; 1 Bit. 3:15.)