WAƘA TA 3
Ƙarfinmu, Begenmu da Makiyayinmu
Hoto
(Misalai 14:26)
1. Ya Jehobah, ka ba mu bege,
bege mai tamani.
Mun gode don wannan begen,
muna yin shelar sa.
Amma matsalolin rayuwa
na iya sa mu gaji,
Kuma mu daina yin ƙwazo
a yin hidimarka.
(AMSHI)
Ƙarfinmu, begenmu,
makiyayinmu,
Kana biyan bukatunmu.
Muna yin wa’azi
da gaba gaɗi
don muna dogara da kai.
2. Ya Jehobah ka taimake mu,
mu riƙa tunawa
da dukan alkawuranka
lokacin wahala.
Kuma dukan alkawuranka
za su sa mu yi ƙwazo,
Domin za su ƙarfafa mu
mu yi shela sosai.
(AMSHI)
Ƙarfinmu, begenmu,
makiyayinmu,
Kana biyan bukatunmu.
Muna yin wa’azi
da gaba gaɗi
don muna dogara da kai.
(Ka kuma duba Zab. 72:13, 14; Mis. 3:5, 6, 26; Irm. 17:7.)