WAƘA TA 126
Mu Yi Tsaro, Mu Riƙe Aminci, Mu Yi Ƙarfi
Hoto
(1 Korintiyawa 16:13)
1. Mu yi tsaro mu yi ƙarfi,
Kar mu daina jimrewa.
Mu zama da ƙarfin hali,
Domin mu yi nasara.
Umurnin Yesu ne muke bi,
Za mu bi shi babu fasawa.
(AMSHI)
Yi tsaro, ƙarfi da aminci!
Kar mu daina jimrewa!
2. Mu kasance a faɗake,
Mu riƙa yin biyayya.
Mu bi ja-gorancin Kristi
Da bawa mai aminci.
Mu yi wa dattawa biyayya,
Don suna kula da mu sosai.
(AMSHI)
Yi tsaro, ƙarfi da aminci!
Kar mu daina jimrewa!
3. Mu yi tsaro da haɗin kai,
Mu riƙa yin wa’azi.
Ko da mutane sun ƙi ji,
Za mu riƙa wa’azi.
Mu kai bishara a ko’ina,
Ranar Jehobah ta yi kusa!
(AMSHI)
Yi tsaro, ƙarfi da aminci!
Kar mu daina jimrewa!
(Ka kuma duba Mat. 24:13; Ibran. 13:7, 17; 1 Bit. 5:8.)