TAIMAKO DON IYALI | AURE
Idan Abokin Aurenka Yana da Halin da ba Ka So Fa?
Ba ka damu da yin shiri kafin ka yi abubuwa ba, amma kila matarka tana son shirya kome da kome.
Matarka shiru-shiru ce kuma ba ta cika son jamaꞌa, amma kai mai surutu ne da ke son jamaꞌa sosai.
Matarka tana da wani halin da ke bata maka rai ne? Idan kana yawan mai da hankali a kan halin, hakan zai iya bata aurenku. Littafi Mai Tsarki ya ce “mai rike laifi yakan raba abokai na kurkusa.”—Karin Magana 17:9.
A maimakon ka bar halin nan ya kawo rashin jituwa a tsakaninka da matarka, za ka iya kasancewa da raꞌayin da ya dace game da halin.
A talifin nan za a tattauna
Yadda za ka kasance da raꞌayin da ya dace game da halayen da ba ka so
Wani halin da ke bata maka rai zai iya zama daya daga cikin halayen da suka sa ka so matarka. Ka yi laꞌakari da misalai ukun nan:
Wata mai suna Chelsea ta ce: “Maigidana yana yin abubuwa a hankali kuma ba ya shiri da sauri idan muna so mu je wani wuri. Amma halin nan yana sa ya rika hakuri, kuma yana hakuri da ni. A wasu lokuta, jinkirinsa yakan bata min rai, amma yana cikin dalilan da suka sa nake kaunarsa.”
Wani mai suna Christopher ya ce: “Matata takan shirya kome dalla-dalla; takan so ta tabbatar cewa kome yana tafiya sumul, kuma hakan na bata min rai. Amma yadda take mai da hankali ga abubuwa yana sa ta kasance a shirye a kowane lokaci.”
Wata mai suna Danielle ta ce: “Maigidana yana da halin ko-in-kula a kan abubuwa, kuma hakan na ba ni haushi. Amma yadda yake yin abubuwa cikin lumana ne ya sa na kusace shi da farko. Yadda yake natsuwa a yanayoyi masu wuya yana burge ni.”
Kamar yadda Chelsea, da Christopher, da kuma Danielle suka fada, halayen miji ko matan mutum da ke bata masa rai suna da inda suke da amfani. Don haka, zai dace mu so halayen abokan aurenmu masu kyau da ma halayensu da ke bata mana rai.
Hakika, wasu halaye ba su da inda suke da amfani. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce wasu mutane suna “saurin fushi.” (Karin Magana 29:22) A wannan yanayin, ya kamata mutum ya yi iya kokarinsa ya “rabu da kowane irin dacin rai, da haushi, da fushi, da fada, da bata suna.”a—Afisawa 4:31.
Amma idan halin yana ba ka haushi ne kawai, ka bi shawarar Littafi Mai Tsarki da ya ce: “Ku yi ta hakuri da juna . . . ko da wani a cikinku ya yi muku laifi.”—Kolosiyawa 3:13, New World Translation.
Kari ga haka, ka yi kokari ka ga yadda halin nan da ke bata maka rai yake da amfani a wani bangare. Watakila halin ne ya sa ka soma son abokin aurenka. Wani magidanci mai suna Joseph ya ce, “Mai da hankali ga halin da ke bata maka rai yana kamar lura da yadda ake kera luꞌuluꞌu ne, maimakon lura da yadda yake da kyau.”
Abubuwan da ya kamata ku tattauna
Da farko, kowannenku zai iya yin laꞌakari da wadannan tambayoyin. Saꞌan nan ku tattauna amsoshin tare.
Shin matarka tana da wani halin da yake jawo matsala a aurenku? Idan haka ne, wane hali ke nan?
Halin ba shi da kyau ne, ko dai yana ba ka haushi ne kawai?
Shin akwai abu mai kyau game da halin? Idan akwai, wane abu ke nan, kuma me ya sa kake son wannan abu game da halin?
a Ka duba talifofin nan “Yadda Za Ka Kame Kanka Idan Ka Yi Fushi,” da “How to Avoid Hurtful Speech,” da kuma “How to Stop Arguing.”