TALIFIN NAZARI NA 12
Ka Ga Abin da Zakariya Ya Gani Kuwa?
“ ‘Ta wurin Ruhuna ne,’ in ji Yahweh Mai Runduna.”—ZAK. 4:6.
WAƘA TA 73 Ka Ba Mu Ƙarfin Zuciya
ABIN DA ZA A TATTAUNAa
1. Wane abin farin ciki ne zai faru ma Yahudawa da aka kai su bauta?
YAHUDAWA sun yi farin ciki sosai domin Jehobah ya “motsa zuciyar Sarki Sariyus” ya saki Isra’ilawa da suka yi shekaru suna bauta a Babila. Sarkin ya ce Yahudawa su koma ƙasarsu don su “sake gina gidan Yahweh Allahn Isra’ila.” (Ezra 1:1, 3) Umurnin ya sa Yahudawan farin ciki sosai. Hakan yana nufin cewa za a sake maido da bautar Jehobah a ƙasar da ya ba mutanensa.
2. Da farko, mene ne Yahudawa da suka koma Urushalima suka iya yi?
2 A shekara ta 537 kafin haihuwar Yesu, rukunin Yahudawa na farko sun isa Urushalima, wanda shi ne babban birnin ƙasar Yahudiya. Yahudawan da suka dawo sun soma gina haikalin ba tare da ɓata lokaci ba, kuma kafin shekara ta 536, sun kammala tushen haikalin!
3. Su wane ne suka yi hamayya da Yahudawan kuma ta yaya suka yi hakan?
3 Jim kaɗan bayan Yahudawan suka soma gina haikalin, sai suka soma fuskantar hamayya sosai. Ƙasashe da ke kewaye da su sun yi “ƙoƙari su hana mutanen Yahuda, suka kuma ba su tsoro domin kada su yi ginin.” (Ezra 4:4) Hakan bai yi wa Yahudawan sauƙi ba sam, kuma yanayin ya ci gaba da muni. A shekara ta 522 kafin haihuwar Yesu, an yi wani sabon sarki a ƙasar Fasiya mai suna Artazekzes.b Maƙiyan Yahudawan sun yi amfani da wannan damar don su hana Yahudawan yin gini ta wajen ƙulla maƙirci a sunan doka. (Zab. 94:20) Sun tura wasiƙa ga Sarki Artazekzes kuma suka gaya masa cewa Yahudawan suna so su yi masa tawaye. (Ezra 4:11-16) Sarkin ya yarda da ƙaryar da suka yi kuma ya ce a dakatar da aikin. (Ezra 4:17-23) Hakan ya sa Yahudawan suka daina aikin.—Ezra 4:24.
4. Mene ne Jehobah ya yi bayan maƙiya sun sa an dakatar da ginin haikalin? (Ishaya 55:11)
4 Wasu mutanen da suke zama a ƙasar da ba sa bauta wa Jehobah da kuma wasu da ke cikin gwamnatin Fasiya sun ƙuduri niyyar dakatar da aikin ginin. Amma Jehobah yana son Yahudawan su gama gina haikalin kuma babu abin da yake hana Jehobah cim ma nufinsa. (Karanta Ishaya 55:11.) Ya yi amfani da wani annabi marar tsoro mai suna Zakariya kuma ya ba shi wahayoyi guda takwas masu ban ƙarfafa. Ya gaya masa ya yi amfani da wahayin ya ƙarfafa Yahudawan. Wahayoyin sun ƙarfafa Yahudawan su ci gaba da gina haikalin kuma sun tabbatar musu cewa ba sa bukatar su ji tsoron maƙiyansu. A wahayi na biyar, Zakariya ya ga sandan da ke riƙe fitilu da kuma itatuwan zaitun guda biyu.
5. Me za mu tattauna a talifin nan?
5 Dukanmu mukan yi sanyin gwiwa a wasu lokuta. Don haka, mu ma za mu iya amfana daga tattauna yadda Jehobah ya ƙarfafa Isra’ilawa ta wahayi na biyar da Zakariya ya gani. Idan muka fahimci wahayin, hakan zai taimake mu mu ci gaba da bauta ma Jehobah da aminci sa’ad da muke fuskantar hamayya, da sa’ad da yanayinmu ya canja da kuma sa’ad da aka ba mu umurnin da ba mu fahimta ba. Abubuwan da za mu tattauna a wannan talifin ke nan.
SA’AD DA MUKE FUSKANTAR HAMAYYA
6. Ta yaya wahayin da ke Zakariya 4:1-3 ya ƙarfafa Yahudawa? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)
6 Karanta Zakariya 4:1-3. Wahayi game da sandan da ke riƙe fitilu da itatuwan zaitun guda biyu sun ƙarfafa Yahudawan su ci gaba da aikinsu duk da hamayya. Ta yaya? Shin ka lura cewa mān fitilar ba ya ƙarewa? Māi yana fitowa daga itatuwan zaitun guda biyun zuwa cikin wani kwano, sai mān ya shiga cikin fitilu guda bakwai daga kwanon. Hakan yana sa fitilun su ci gaba da haskakawa. Zakariya ya yi tambaya ya ce: “Mene ne ma’anar waɗannan?” Jehobah ya amsa ta wurin mala’ikansa ya ce: “ ‘Ba ta wurin ƙarfi ba, ba ta wurin iko ba, amma ta wurin Ruhuna ne,’ in ji Yahweh Mai Runduna.” (Zak. 4:4, 6) Mān da ke fitowa daga itatuwan yana wakiltar ruhun Jehobah wanda ba zai taɓa ƙarewa ba. Ruhun Allah yana da iko fiye da sojojin Fasiya. Tun da Jehobah yana tare da su, Yahudawan za su iya ci gaba da gina haikalin har su gama shi duk da hamayyar da ake musu. Hakika, saƙon ya ƙarfafa Yahudawan. Abin da suke bukatar su yi shi ne su dogara ga Jehobah kuma su koma aiki. Kuma abin da suka yi ke nan duk da cewa ba a cire takunkumi da aka saka a aikin ba.
7. Me ya faru da ya taimaki Yahudawan da suke gina haikali?
7 An sami canji da ya kawo sauƙi ga Yahudawan da suke gina haikalin. Wane canji ke nan? Wani sabon sarki mai suna Dariyus na 1 ya zama sarkin Fasiya. Bayan ya yi shekara biyu da sarauta, wato a shekara ta 520 kafin haihuwar Yesu, ya gano cewa hana Yahudawa gina haikalin ba bisa doka ba ce. Sai Dariyus ya gaya wa Yahudawa cewa su ci gaba da gina haikalin. (Ezra 6:1-3) Matakin da sarkin ya ɗauka ya ba kowa mamaki. Amma sarkin ya yi wani abu fiye da hakan. Sarkin ya umurci ƙasashen da ke kewaye da Yahudawan su daina hamayya da ginin haikalin kuma su ba Yahudawan kuɗi da duk wani abin da suke bukata don su kammala ginin. (Ezra 6:7-12) Don haka, Yahudawan sun kammala aikin ginin cikin shekaru huɗu da ’yan kai, wato a shekara ta 515 kafin haihuwar Yesu.—Ezra 6:15.
8. Me zai iya ba ka ƙarfin zuciya sa’ad da kake fuskantar hamayya?
8 A yau ma, bayin Jehobah da dama suna fuskantar hamayya. Alal misali, wasu suna zama a ƙasar da ba a barin su su yi wa’azi a sake. A ƙasashen nan, ana kama ’yan’uwanmu kuma a kai su “gaban shugabanni da sarakuna” don shaida a gare su. (Mat. 10:17, 18) A wasu lokuta, canjin gwamnati yana iya taimaka musu ko kuma wani alƙali mai kirki zai iya yanke hukunci da zai ba su izinin yin wa’azi ba tare da takura ba. Wasu Shaidun Jehobah kuma suna fuskantar hamayya ta wata hanya dabam. Suna da izinin yin wa’azi da bauta wa Jehobah a ƙasarsu. Amma suna fuskantar hamayya daga membobin iyalinsu waɗanda suke so su hana su bauta wa Jehobah. (Mat. 10:32-36) A yawancin lokuta, idan membobin iyalin suka ga cewa sun ƙasa hana ɗan’uwansu bauta wa Jehobah duk da hamayyar da suke yi masa, sai su daina yin hakan. Kuma wasu da suka yi hamayya da Shaidun Jehobah sosai sun soma bauta wa Jehobah da ƙwazo daga baya. Idan ana hamayya da kai, kada ka daina bauta wa Jehobah. Ka yi ƙarfin zuciya, Jehobah da kuma ruhunsa mai tsarki za su taimaka maka. Don haka, kada ka ji tsoro.
SA’AD DA YANAYINKA YA CANJA
9. Me ya sa wasu Yahudawa ba su yi farin ciki ba da aka kafa tushen sabon haikalin?
9 Da aka gama gina tushen haikalin, wasu daga cikin dattawan Yahudawan sun yi kuka. (Ezra 3:12) Sun ga haikali mai ɗaukaka da Sulemanu ya gina kuma a ganinsu sabon haikalin “ba a bakin kome yake ba” idan aka kwatanta shi da haikali na dā. (Hag. 2:2, 3) Sun yi baƙin ciki sosai don sun gwada sabon haikalin da na dā. Wahayin da Zakariya ya gani zai taimaka musu su sake yin farin ciki. Ta yaya?
10. Ta yaya abin da mala’ika ya faɗa a Zakariya 4:8-10 ya taimaka ma Yahudawan su daina baƙin ciki?
10 Karanta Zakariya 4:8-10. Mene ne mala’ikan yake nufi sa’ad da ya ce Yahudawan za su yi ‘farin ciki sa’ad da suka ga igiyar awon kammalawar ginin’ a hannun gwamnan Yahudawa wato Zerubbabel? Igiyar awon, igiya ce da ake amfani da shi don a ga ko abu ya miƙe da kyau. Don haka, mala’ikan yana tabbatar wa Yahudawa cewa ko da yake haikalin ba zai kai na dā ba, za a kammala ginin kuma zai kasance daidai yadda Jehobah yake so. Jehobah zai yi farin ciki da haikalin, to me ya sa Yahudawan ba za su yi farin ciki ba? Abin da ya fi muhimmanci ga Jehobah shi ne bauta da za a yi a haikalin ta yi daidai da tsarin da ya kafa. Idan Yahudawan sun mai da hankali ga yadda za su bauta wa Jehobah a hanyar da yake so don su sami amincewarsa, za su sake yin farin ciki.
11. Waɗanne ƙalubale ne bayin Jehobah suke fuskanta a yau?
11 Ba ya yi wa yawancin mu sauƙi idan yanayinmu ya canja. An canja ma wasu ’yan’uwa hidima bayan sun jima suna yin hidima ta cikakken lokaci. Wasu kuma sun daina hidimar da suke jin daɗin sa saboda tsufa. Idan yanayinmu ya canja kamar haka, za mu iya yin baƙin ciki. Mai yiwuwa da farko ba za mu fahimci dalilin da ya sa hakan ya faru ba ko kuma mu ƙi yarda da hakan. Za mu iya soma ji kamar yadda abubuwa suke a baya sun fi kyau, kuma za mu iya soma sanyin gwiwa domin muna ganin ba mu da amfani a ƙungiyar Jehobah kamar dā. (Karin Magana 24:10, New World Translation) Ta yaya wahayin da Zakariya ya gani zai taimaka mana mu ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu a ƙungiyar Jehobah?
12. Ta yaya wahayin da Zakariya ya gani zai taimaka mana mu ci gaba da farin ciki ko da yanayinmu ya canja?
12 Zai yi mana sauƙi mu saba da sabon yanayinmu idan muna ɗaukan yanayinmu yadda Jehobah yake ɗaukan sa. Yana yin abubuwa masu muhimmanci a yau kuma muna da gatan yin aiki tare da shi. (1 Kor. 3:9) Ko da a yanzu ba ma iya yin ayyukan da muke yi a dā, Jehobah zai ci gaba da ƙaunar mu. Don haka, idan canji da ƙungiyarmu ta yi ya shafe ka, kada ka ɓata lokaci kana tunani a kan dalilin da ya sa aka yi canjin. A maimakon ka ce “kwanakin dā sun fi na yanzu” ka yi addu’a kuma ka mai da hankali ga abubuwa masu kyau da kake mora a yanzu. (M. Wa. 7:10) Ka mai da hankali a kan abubuwan da za ka iya yi, maimakon abubuwan da ba za ka iya yi yanzu ba. Wahayin da Zakariya ya gani ya koya mana muhimmancin kasancewa da ra’ayin da ya dace. Don haka, za mu ci gaba da kasancewa da amincinmu kuma mu yi farin ciki ko da yanayinmu ya canja.
SA’AD DA YAKE MANA WUYA MU BI UMURNI
13. Me ya sa wasu Yahudawa za su iya ɗauka cewa umurnin da aka ba su su ci gaba da gina haikalin bai dace ba?
13 An dakatar da aikin gina haikalin amma Babban Firist Yeshuwa (Joshua) da kuma Gwamna Zerubbabel waɗanda aka naɗa su su ja-goranci Yahudawan sun “ci gaba da aikin gina gidan Allah.” (Ezra 5:1, 2) Mai yiwuwa wasu Yahudawa sun ɗauka cewa matakin bai dace ba. Yahudawan ba za su iya yin aikin a ɓoye ba kuma sun san cewa maƙiyansu za su yi iya ƙoƙarinsu don su hana su ginin. Joshua da Zerubbabel sun bukaci tabbaci cewa Jehobah yana goyan bayan su. Sun sami tabbacin. Ta yaya?
14. Bisa ga Zakariya 4:12, 14, wane tabbaci ne Babban Firist Joshua da Gwamna Zerubbabel suka samu?
14 Karanta Zakariya 4:12, 14. A wannan wahayin, mala’ikan ya gaya wa annabin cewa itatuwan zaitun guda biyun suna wakiltar “mutane biyu wanda aka keɓe,” wato Joshua da Zerubbabel. Mala’ikan ya ce kamar dai mutane biyun nan suna yi wa “Ubangijin dukan duniya hidima” ne. Wannan babban gata ne. Jehobah ya yarda da su. Don haka, Isra’ilawan za su iya gaskata da duk wani umurni da mutane biyun nan suka ba su domin Jehobah ne yake amfani da su.
15. Ta yaya za mu nuna cewa muna bin umurnin Jehobah da ke Kalmarsa?
15 Hanya ɗaya da Jehobah yake ci gaba da ba mutanensa umurni ita ce ta Kalmarsa. A ciki, ya gaya mana yadda yake so mu bauta masa. Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja umurnin da muke karantawa daga Kalmar Allah? Ta wajen karanta ta da kuma yin iya ƙoƙarinmu mu fahimci abin da ke ciki. Ka tambayi kanka: ‘Idan na karanta Littafi Mai Tsarki, ina ɗan dakatawa in yi tunani a kan abin da na karanta? Ina yin bincike don in fahimci wasu batutuwa a cikin Littafi Mai Tsarki da suke da “wuyar ganewa”? Ko kuma ina karanta batun cikin hanzari ne kawai?’ (2 Bit. 3:16) Idan muna yin tunani mai zurfi a kan abubuwan da Jehobah yake koya mana, za mu iya bin umurninsa kuma za mu iya yin wa’azi da kyau.—1 Tim. 4:15, 16.
16. Idan ba mu fahimci dalilin da ya sa “bawan nan mai aminci” ya ba mu wani umurni ba, me zai taimake mu mu bi umurnin?
16 Wata hanya kuma da Jehobah yake ba mu umurni ita ce ta wurin “bawan nan mai aminci, mai hikima.” (Mat. 24:45) A wasu lokuta, bawan nan zai iya ba mu umurni da ba mu fahimci dalilin ba. Alal misali, za a iya ba mu umurni a kan yadda za mu kāre kanmu daga wani bala’in da muke ganin ba zai taɓa faruwa a yankinmu ba. Ko kuma, za mu iya ɗauka cewa matakan da bawan yake ɗaukawa a lokacin annoba sun wuce gona da iri. Me ya kamata mu yi idan muna ji kamar umurnin da aka ba mu bai dace ba? Za mu iya yin tunani a kan yadda Isra’ilawa suka amfana domin sun yi biyayya da umurnin da Joshua da Zerubbabel suka ba su. Za mu kuma iya yin tunani a kan wasu labarai da muka karanta a Littafi Mai Tsarki. A wasu lokuta, akan ba bayin Allah umurni da a gun ’yan Adam bai dace ba, amma daga baya yakan ceci rayuka.—Alƙa. 7:7; 8:10.
KA GA ABIN DA ZAKARIYA YA GANI
17. Ta yaya wahayin sandan da ke riƙe fitilu da itatuwan zaitun guda biyu ya shafi Yahudawan?
17 Wahayi na biyar da Zakariya ya gani gajere ne amma ya taimaki Yahudawan su yi ƙwazo kuma su ci gaba da aikin gina haikalin. Kuma da suka yi biyayya ga abin da Zakariya ya faɗa, sun ga yadda Jehobah ya taimake su kuma ya ja-gorance su cikin ƙauna. Ta wurin ruhunsa mai tsarki, Jehobah ya taimaka musu su ci gaba da aikinsu kuma su sake farin ciki.—Ezra 6:16.
18. Ta yaya wahayin da Zakariya ya gani zai iya shafan ka?
18 Wahayin sandan da ke riƙe fitilu da itatuwan zaitun guda biyu zai iya shafan rayuwarka sosai. Kamar yadda muka tattauna, zai iya ƙarfafa ka ka jimre sa’ad da ake hamayya da kai, zai taimaka maka ka yi farin ciki sa’ad da yanayinka ya canja, kuma zai taimaka maka ka dogara ga Jehobah kuma ka yi biyayya idan aka ba ka umurnin da ba ka fahimci dalilin ba. Me ya kamata ka yi idan kana fuskantar matsaloli a rayuwarka? Da farko, ka ga abin da Zakariya ya gani, wato tabbacin cewa Jehobah yana kula da mutanensa. Sai ka bar abin da ka gani ya sa ka dogara ga Jehobah kuma ka ci gaba da bauta masa da dukan zuciyarka. (Mat. 22:37) Idan ka yi hakan, Jehobah zai taimaka maka ka bauta masa da farin ciki har abada.—Kol. 1:10, 11.
WAƘA TA 7 Jehobah Ne Ƙarfinmu
a Jehobah ya ba annabi Zakariya jerin wahayoyi masu ban ƙarfafa. Wahayin da Zakariya ya gani ya ƙarfafa shi da sauran bayin Jehobah su iya shawo kan hamayya yayin da suke ƙoƙarin sake maido da bauta ta gaskiya. Wahayoyin za su taimaka mana mu ci gaba da bauta ma Jehobah duk da matsaloli. A talifin nan, za mu tattauna ɗaya daga cikin wahayoyin, wanda ya ƙunshi sandan da ke riƙe da fitilu da kuma itatuwan zaitun.
b Shekaru da yawa bayan wannan lokacin, a zamanin Gwamna Nehemiya, an yi wani sarki kuma mai suna Artazekzes wanda ya yi alheri ga Yahudawa.
c BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗan’uwa ya ga cewa ya dace ya saba da sabon yanayin da ya shiga saboda tsufa da kuma rashin lafiya.
d BAYANI A KAN HOTUNA: Wata ’yar’uwa tana tunani a kan yadda Jehobah yake goyon bayan “bawan nan mai aminci, mai hikima” kamar yadda ya goyi bayan Joshua da kuma Zerubbabel.