WAƘA TA 139
Rayuwa a Cikin Aljanna
(Ru’ya ta Yohanna 21:1-5)
1. Ka ga kanka, ka gan ni ma,
Ka gan mu duk a cikin aljanna.
Yin rayuwa a aljanna
Zai yi daɗi, kome zai yi kyau.
Za a kawar da mugaye,
Mulkin Jehobah zai dawwama.
A lokacin da muke a aljanna
Duk za mu yi murna
muna rera yabo:
(AMSHI)
“Mun gode Allah don ayyukanka.
Ɗanka Yesu ya gyara duniya.
Muna godiya sosai don albarkarka.
Muna rera waƙar yabo ga sunanka.”
2. Ka ga kanka, ka gan ni ma,
Ka gan mu muna jin daɗi sosai.
Babu kome a duniya
Da zai sa mu riƙa jin tsoro.
Alkawuran Maɗaukaki
Duk sun cika yadda ya faɗa.
Jehobah Uba, zai ta da matattu,
Duk za mu rera yabo
da murna sosai:
(AMSHI)
“Mun gode Allah don ayyukanka.
Ɗanka Yesu ya gyara duniya.
Muna godiya sosai don albarkarka.
Muna rera waƙar yabo ga sunanka.”
(Ka kuma duba Zab. 37:10, 11; Isha. 65:17; Yoh. 5:28; 2 Bit. 3:13.)