WAƘA TA 93
Ka Albarkaci Taronmu
Hoto
(Ibraniyawa 10:24, 25)
1. Ka albarkaci taronmu,
Muna roƙo, Ya Allah.
Mun gode domin taronmu
Da ruhunka mai tsarki.
2. Ya Allah ka taimake mu
Domin mu san Kalmarka.
Muna so mu riƙa himma
A yin wa’azin Mulki.
3. Ya Uba, muna roƙon ka
Ka sa mu yi haɗin kai.
Ayyukanmu, furucinmu,
Su ɗaukaka ikonka.
(Ka kuma duba Zab. 22:22; 34:3; Isha. 50:4.)