Alhamis, 3 ga Satumba
Mai shariꞌar dukan duniya, ba za ka yi shariꞌa daidai ba?—Far. 18:25.
Shin, za iya buga ƙirji mu ce idan har Jehobah ne ya shariꞌanta mutum, shariꞌar daidai ne? Ƙwarai kuwa! Ibrahim ya ga tabbaci cewa Jehobah, “mai shariꞌar dukan duniya” ba ya kuskure, hikimarsa babu iyaka, kuma shi mai jinƙai ne. Ya riga ya koyar da Ɗansa kuma ya ba shi hakkin yi wa kowa shariꞌa. (Yoh. 5:22) Kamar Jehobah, Yesu ma zai iya sanin abin da mutum yake tunani a zuciyarsa. (Mat. 9:4) Don haka idan suka zo shariꞌanta kowane mutum, za su “yi shariꞌa daidai”! Bari mu ƙudiri niyya cewa za mu yarda da duk wata shawara da Jehobah ya yanke. Mun san ba mu cancanci mu yi shariꞌa ba, amma Jehobah ya cancanci yin hakan! (Isha. 55:8, 9) Don haka, mun bar dukan shariꞌa a hannun Jehobah da Ɗansa, kuma mun tabbata za su yi shariꞌar gaskiya. Tabbas, Sarkinmu Yesu zai yi koyi da adalci da kuma jinƙan Ubansa.—Isha. 11:3, 4. w24.05 7 sakin layi na 18-19
Jumma’a, 4 ga Satumba
Yahweh yana ƙyamar mai halin ruɗu, amma yana amincewa da mai gaskiya a zuci.—K. Mag. 3:32.
Abin da ya faru saꞌad da Filibus ya kawo abokinsa Nataniyel wurin Yesu, ya nuna cewa yana da muhimmanci sosai mutum ya zama mai faɗin gaskiya daga zuciyarsa. Ko da yake Yesu bai taɓa haɗuwa da Nataniyel ba, da ganin sa Yesu ya ce: “Ku ga mutumin Israꞌila na gaske, wanda ba shi da ƙarya a cikinsa.” (Yoh. 1:47) ya lura cewa Nataniyel yana faɗin gaskiya ba kaɗan ba. Ko da yake Nataniyel ajizi ne kamar mu, ba ya munafunci, yana yin gaskiya a kome da yake yi. Halinsa ya burge Yesu kuma Yesu ya yaba masa. Yawancin umurnan da ke Zabura ta 15 game da yadda ya kamata mu yi shaꞌani da mutane ne. Zabura 15:3 ta ce baƙo da ya shigo tentin Jehobah “ba ya ɓata sunan wani, . . . ba ya yi wa abokansa mugunta, ko ya baza jita-jita game da maƙwabtansa.” Irin waɗannan maganganun za su iya cutar da mutane sosai.—Yak. 1:26. w24.06 10 sakin layi na 7, 9; 11 sakin layi na 10
Asabar, 5 ga Satumba
Ubangiji, har aljanu ma suna jinmu idan mun umarce su cikin sunanka!—Luk. 10:17.
Idan ka yi shiri kafin ka fita waꞌazi ba za ka ji tsoro sosai saꞌad da kake yi wa mutane magana ba. Yesu ya shirya almajiransa kafin ya aike su su yi waꞌazi. (Luk. 10:1-11) Almajiran Yesu sun bi abin da ya koya musu, shi ya sa suka yi abubuwa masu kyau da yawa, kuma hakan ya sa su farin ciki. Ta yaya za mu yi shiri kafin mu fita waꞌazi? Ya kamata mu yi tunani sosai a kan abin da muke so mu faɗa. Hakan zai taimaka mana mu yi magana daga zuciyarmu. Zai dace kuma mu yi tunani a kan abubuwa biyu ko uku da mutanen za su iya gaya mana, saꞌan nan mu yi tunani a kan amsar da za mu ba su. Saꞌad da muke magana da mutane, mu yi ƙoƙari mu sake jiki kuma mu yi murmushi. w24.04 16 sakin layi na 6-7