Bisharar Mulki lamba na 36
Sabon Alif—Wane Abu Ne Zai Kawo Maka a nan Gaba?
Sabon Alif—Wayewar Sabuwar Tsara Ce?
A TSAKAR daran 31 ga Disamba, 1999, ƙarni na 20 ya ƙare.a Ƙarni ne da ya ga hayaniya ƙwarai. Amma kuma ya ga bunƙasar sabuwar fasaha, ci gaba na mamaki a aikin asibiti, yaɗuwar hanyar sadarwa, da kuma hanzarin ƙaruwar tattalin arziki na duniya. Saboda haka, wasu suka marabci sabon alif cewa alama ne na bege da canji. Shin zai ga ƙarshen yaƙi, talauci, gurɓata mahalli, da kuma cuta?
Mutane da yawa sun sa rai haka. Amma yaya ka ke jin sabon alif zai kawo canjin da zai amfane ka—canji da zai kawo maka kwanciyar rai da kuma iyalinka? Ka yi la’akari da tulin damuwa kaɗan kawai da muke fuskanta.
Gurɓata
Ƙasashe masu kamfanoni suna “ɓarnata mahalli a dukan duniya kuma suna gurɓata mahalli da kuma ɓata tsarin halitta.” Idan abin da yake faruwa yanzu ya ci gaba, “mahalli zai ci gaba da matsewa.”—“Global Environment Outlook—2000,” Tsarin Ayyukan Mahalli na Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ciwo
“A ƙarshen shekara ta 2020, cututtuka da ba sa yaɗuwa ana tsammanin za su kashe mutane bakwai a cikin goma a yankuna masu tasowa, in an gwada da wanda bai kai ma rabi ba a yau.”—“The Global Burden of Disease,” Harvard University Press, 1996.
Wasu gwanaye sun yi da’awar cewa “a shekara ta 2010, raguwar mutane miliyan 66 kawai [za su rayu] a ƙasashe 23 da suke da annoba mafi tsanani na [ƙanjamau].”—“Confronting AIDS: Evidence From the Developing World,” rahoton European Commission da Kuma Bankin Duniya.
Talauci
“Kusan mutane biliyan 1.3 suna rayuwa ta yin amfani da kasa da dala guda a rana, kuma kusan biliyan 1 ba sa samun abinci da suke bukata.”—“Human Development Report 1999,” Tsarin Bunƙasa na Majalisar Ɗinkin Duniya.
Yaƙi
“Kashe-kashe cikin [ƙasashe dabam dabam] zai zama babu iyaka. Wanda [bambancin] zuriya, ƙabila, da kuma addini ya ke jawowa, . . . irin waɗannan kashe-kashe zai zama . . . yaƙi da ya cika ko’ina a cikin rubu’in ƙarni na gaba . . . , yana kashe mutane dubbai kowace shekara.”—“New World Coming: American Security in the 21st Century,” U.S. Commission on National Security/21st Century.
Murna na ɗan lokaci domin sabon alif yana rufe gaskiyar cewa gurbata mahalli, ciwo, talauci, da kuma yaƙi suna kwance gaba fiye da dā. A ƙarƙashin waɗannan damuwa da akwai kwaɗayi, rashin amincewa da wane, da son kai—halaye da ba za a iya kawar da su ta nazarin kimiyya, fasaha, ko kuma siyasa ba.
Alif Da Zai Albarkaci Mutane
WANI marubuci na dā ya lura: “Hanyar mutum ba cikin nasa hannu ta ke ba; mutum kuwa ba shi da iko shi shirya tafiyarsa.” (Irmiya 10:23) Mutum, ba kawai ba shi da iyawa na sarautar duniya ba amma ba shi da damar yin hakan. Mahaliccinmu, Jehovah Allah ne kawai yake da dama kuma ya san yadda zai magance damuwar ’yan Adam.—Romawa 11:33-36; Ru’ya ta Yohanna 4:11.
Amma yaushe? Ta yaya? Alamun cewa muna kusa da ƙarshen “kwanaki na ƙarshe” suna da yawa. Don Allah, ka buɗe Littafi Mai-Tsarki naka, ka karanta 2 Timothawus 3:1-5. Ya kwatanta sarai halaye da mutane za su nuna a lokacin “miyagun zamanu.” Matta 24:3-14 da kuma Luka 21:10, 11 su ma sun kwatanta “kwanaki na ƙarshe.” A nan an mai da hankali ne ga abin da suka auku a zahiri tun daga shekara ta 1914, kamar su yaƙe-yaƙe a dukan duniya, annoba, bazuwar karancin abinci.
Ba da jimawa ba “kwanaki na ƙarshe” za su ƙare. Daniel 2:44 ya ce: “Allah mai-sama za ya kafa wani mulki, wanda ba za a rushe shi ba daɗai, . . . amma za ya farfashe dukan waɗannan mulkoki [na duniya] ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.” Saboda haka, an annabta cewa Allah zai kafa Mulki, ko kuma gwamnati, ta mallaki duniya. Ru’ya ta Yohanna 20:4 ta ce, wannan gwamnatin za ta yi sarauta ta shekara dubu—alif! Ka yi la’akari da wasu hanyoyi na yadda yanayin rayuwan dukan mutane zai gyaru lokacin wannan alif mai daraja:
Tattalin Arziki. “Za su gina gidaje, kuma za su zauna a ciki; su yi gonakin anab kuma, su ci amfaninsu. Ba za su yi gini, wani ya zauna ba: ba za su dasa, wani ya ci ba.”—Ishaya 65:21, 22.
Lafiyar Jiki. “Sa’annan za a buɗe idanun makafi, kunnuwan kurame kuma za a buɗe. Sa’annan gurgu za ya yi ta tsalle kamar barewa, harshen bebe kuma za ya rera waƙa.” “Wanda ya ke zaune a ciki ba za ya ce, Ina ciwo ba.”—Ishaya 33:24; Ishaya 35:5, 6.
Mahalli. Allah zai “halaka waɗanda ke halaka duniya.”—Ru’ya ta Yohanna 11:18.
Dangantakar Mutane. “Ba za su yi ciwutarwa ba; ba kuwa za su yi ɓarna ko’ina cikin dutsena mai-tsarki ba: gama duniya za ta cika da sanin Ubangiji, kamar yadda ruwaye su ke rufe teku.”—Ishaya 11:9.
Miliyoyin mutane suna da bangaskiya cikin waɗannan alkawuran Littafi Mai-Tsarki kuma saboda haka, suna da gaba gaɗi game da abin da yake zuwa a nan gaba. Saboda haka, suna iya bi da matsi da matsalolin rayuwa. Ta yaya Littafi Mai-Tsarki zai zama yana ja-gorar rayuwarka?
Sani da Yake Kai Zuwa Rai!
Kimiyya da fasaha wani lokaci sukan burge! Duk da haka, ilimin mutane bai mai da farin ciki da kwanciyar rai ba ga mutane da yawa. Sani da zai iya yin haka an kwatanta shi cikin Littafi Mai-Tsarki a Yohanna 17:3, wanda ya ce: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.”
Wannan sanin ana samunsa a shafofin Littafi Mai-Tsarki. Ko da yake mutane da yawa suna da kakkwarar ra’ayi game da wannan tsarkakken littafi, kaɗan ne kawai suka bincika shi da kansu. Kai fa? Hakika, karatun Littafi Mai-Tsarki yana bukatar ƙoƙari. Kuma kwalliya za ta biya kuɗin sabulu. Littafi Mai-Tsarki ne kawai littafin da ke “hurarre daga wurin Allah mai-amfani ne ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa, ga horo kuma da ke cikin adilci.”—2 Timothawus 3:16.
To, ta yaya za ka fara sanin Littafi Mai-Tsarki? Me ya sa ba za ka karɓi taimakon Shaidun Jehovah ba? Suna koya wa miliyoyin mutane a gidajensu, kyauta. Don su taimake ka game da wannan, suna amfani da littattafai dabam dabam daga Littafi Mai-Tsarki, kamar su mujallar nan Minene Allah ke Bukata Daga Garemu? Ta ba da taƙaitattun amsoshi ga tambayoyi da wataƙila ka ke da su game da Littafi Mai-Tsarki, kamar su: Wanene Allah? Menene Allah ya nufa wa duniya? Menene Mulkin Allah? Ta yaya Littafi Mai-Tsarki zai gyara rayuwar iyalinka?
Idan za ka so wani cikin Shaidun Jehovah ya zo gidanka, sai ka cika fom da yake ƙasa. Za su yi farin cikin ba ka ƙarin bayani game da Sarauta da take da ɗaukaka na Alif na Mulkin Allah!
□ Zan so na sami mujallar nan Minene Allah ke Bukata Daga Garemu? Ka nuna yaren da ka ke so
□ Don Allah ku zo wuri na game da nazarin Littafi Mai-Tsarki na gida kyauta
[Hasiya]
a A nan mun nuna ra’ayin yawanci ne a Yammacin duniya game da sabon alif. Ta hanyar kimiyya, sabon alif zai fara ne a 1 ga Janairu, 2001.