BABI NA BIYU
Ya Yi “Tafiya Tare da Allah”
1, 2. Wane aiki ne Nuhu da iyalinsa suka yi, kuma waɗanne ƙalubale ne suka fuskanta?
NUHU ya tashi tsaye don ya miƙe jikinsa. A ce kana ganin sa yana kallon babban jirgin da suke ginawa yayin da yake zaune a kan wani babban katako don ya ɗan huta. Warin kwalta ya cika ko’ina kuma ana jin ƙarar kayayyakin aiki. Daga inda Nuhu yake zaune, yana ganin yadda yaransa suke aiki tuƙuru don su harhaɗa manya-manyan katako. Shi da matarsa da kuma ’ya’yansa da matansu duka sun yi shekaru da yawa suna fama da wannan aikin. Sun riga sun gama gina wani sashe na jirgin, amma akwai aiki birjik da ya rage!
2 Mutanen da suke ganin su sun ɗauka cewa su wawaye ne. Yayin da Nuhu da iyalinsa suka ci gaba da gina jirgin, mutane sun ci gaba da musu dariya domin suna ganin rigyawa ba za ta taɓa mamaye duniya ba. Suna ganin abin da Nuhu yake musu gargaɗi a kai ba zai taɓa faruwa ba! Sun kasa sanin dalilin da ya sa wannan mutum da iyalinsa suke ɓata lokacinsu suna irin wannan aikin banza. Amma, ba haka ne Jehobah ya ɗauki aikin da Nuhu yake yi ba.
3. A wace hanya ce Nuhu ya yi tafiya tare da Allah?
3 Kalmar Allah ta ce: Nuhu ya yi “tafiya tare da Allah.” (Karanta Farawa 6:9.) Mene ne hakan yake nufi? Ba wai Allah ya sauko duniya ko kuma Nuhu ya je sama domin su yi tafiya tare ba. Amma, Nuhu ya yi biyayya ga Jehobah da zuciya ɗaya kuma ya ƙaunace shi sosai, har ya zama kamar shi da Jehobah suna takawa tare a matsayin aminai. Dubban shekaru bayan haka, Littafi Mai Tsarki ya yi wannan furucin game da Nuhu: “Ta bangaskiya[rsa] kuma ya tabbatar wa duniya laifinta.” (Ibran. 11:7, Littafi Mai Tsarki) Ta yaya ya yi hakan? Mene ne za mu koya daga bangaskiyarsa?
Mutum Marar Aibi a Duniya da ke Cike da Mugunta
4, 5. Me ya sa duniya ta lalace sosai a zamanin Nuhu?
4 Nuhu ya yi girma a lokacin da mugunta take daɗa gaba gaba a duniya. Haka ma duniya take a zamanin kakan-kakanninsa Anuhu. Anuhu wani mutum ne mai adalci da ya yi tafiya tare da Allah. Ya annabta cewa za a hukunta mutane masu mugunta a duniya. Amma a zamanin Nuhu, mugunta ta daɗa muni. Hakika a gaban Jehobah, duniya ta ɓace gaba ɗaya domin ta cika da mugunta. (Far. 5:22; 6:11; Yahu. 14, 15) Me ya sa yanayin ya yi muni haka?
5 Wani mummunan abu ya faru tsakanin mala’ikun Allah. Ɗaya cikinsu ya yi tawaye da Jehobah kuma ya zama Shaiɗan Iblis. Ta yaya ya yi hakan? Ta wajen tsegunta Allah da kuma ruɗin Adamu da Hawwa’u su yi zunubi. A zamanin Nuhu, wasu mala’iku sun bi irin wannan tafarki na yin tawaye da Jehobah. Sa’ad da mala’ikun suka ƙi yin aikin da Jehobah ya ba su a sama, sai suka sauko duniya da siffar ’yan Adam kuma suka auri kyawawan mata. Waɗannan mala’ikun masu fahariya da son kai da suka yi tawaye sun yaudari wasu ’yan Adam ma.—Far. 6:1, 2; Yahu. 6, 7.
6. Ta yaya ƙatta suka sa mugunta ta yaɗu a duniya, kuma me Jehobah ya ce zai yi?
6 Irin wannan aure tsakanin mala’iku da mata ya saɓa wa nufin Allah, kuma matan sun haifi ’ya’ya ƙatta masu ƙarfin gaske. Littafi Mai Tsarki ya kira su Nephilim, kuma wannan kalmar tana nufin masu sa wasu tuntuɓe. Da yake Nephilim ɗin masu cin zali ne, sun sa zalunci ya daɗa yaɗuwa a duniya. Saboda haka, a gaban Mahaliccinmu, ‘muguntar mutum ta yi yawa cikin duniya, kuma kowace shawara ta tunanin zuciyarsa mugunta ce kaɗai kullayaumi.’ Sai Jehobah ya ƙudura cewa zai halaka miyagu nan da shekara 120.—Karanta Farawa 6:3-5.
7. Wane ƙalubale ne Nuhu da matarsa suka fuskanta yayin da suke ƙoƙarin kāre yaransu daga ɓatancin zamaninsu?
7 Ka yi tunanin yadda yake da wuya mutum ya yi renon yara a cikin irin wannan yanayin! Duk da haka, Nuhu ya yi renon yaransa da kyau. Ya auri mace mai hankali. Bayan Nuhu ya cika shekara 500, matarsa ta haifa masa ’ya’ya maza uku, wato Shem da Ham da kuma Japheth.a Nuhu da matarsa sun yi ƙoƙarin kāre ’ya’yansu daga miyagun mutane da ke kewaye da su. Yara maza sukan yi sha’awar kallon ‘ƙarfafa’ da kuma “shahararrun mutane.” Saboda haka, yana iya yiwuwa cewa yara sun yi sha’awar waɗannan Nephilim sosai. Nuhu da matarsa ba za su iya kāre ’ya’yansu daga jin labaran dukan miyagun abubuwa da ƙattan suke yi ba, amma za su iya koya musu gaskiya game da Jehobah Allah, wanda ya ƙi jinin masu mugunta. Sun bukaci su taimaki yaransu su gane cewa mugunta da tawaye da mutane suke yi a duniya suna ɓata wa Jehobah rai.—Far. 6:6.
8. Ta yaya iyaye masu hikima a yau za su iya yin koyi da misalin Nuhu da matarsa?
8 Iyaye ma a yau suna fuskantar irin yanayin Nuhu da matarsa. Duniya da muke ciki ma tana cike da mugunta da kuma tawaye. Kuma muna ganin hakan a wasanni da shirye-shiryen telibijin da aka tsara don yara. Iyaye masu ƙaunar Jehobah za su yi ƙoƙari sosai su koya wa yaransu tafarkin Jehobah, Allah na salama wanda zai kawar da dukan mugunta wata rana. (Zab. 11:5; 37:10, 11) Ko a wannan duniya da ke cike da mugunta, zai yiwu a koya wa yara nagarta! Nuhu da matarsa sun yi nasara. Yaransu sun yi girma har sun zama mazajen kirki, kuma suka auri matan da suka so yin nufin Jehobah, Allah na gaskiya.
“Ka Yi Jirgi”
9, 10. (a) Wane umurnin da Jehobah ya ba Nuhu ne ya canja salon rayuwarsa? (b) Mene ne Jehobah ya ce wa Nuhu game da fasalin jirgin da kuma dalilin gina shi?
9 Wata rana, wani abu ya faru da ya canja salon rayuwar Nuhu baki ɗaya. Jehobah ya gaya wa wannan bawansa cewa zai halaka miyagun mutane na zamanin. Sai Allah ya umurci Nuhu cewa: “Ka yi jirgi na itacen jufra.”—Far. 6:14.
10 Wannan jirgin ba shi da fasalin jirgin ruwan da gama gari ne a yau, kamar yadda wasu suke tsammani. Amma, yana da fasalin babban akwati. Jehobah ya gaya wa Nuhu ainihin girman jirgin da fasalinsa, kuma ya ce a shafa masa kwalta ciki da waje. Allah ya kuma gaya wa Nuhu dalilin hakan, ya ce: “Ina kawo ruwan tufana a bisa duniya, . . . Dukan abin da ke cikin duniya za shi mutu.” Amma, Jehobah ya yi wa Nuhu alkawari cewa: “Za ka shiga cikin jirgi kuma, da kai, da ’ya’yanka, da matarka, da matayen ’ya’yanka tare da kai.” An kuma gaya wa Nuhu ya shigar da dabbobi iri-iri cikin jirgin. Abubuwan da ke cikin jirgin ne kaɗai za su tsira wa Rigyawar!—Far. 6:17-20.
11, 12. Wane gaggarumin aiki ne Allah ya ba Nuhu, kuma ta yaya ya bi da ƙalubalen?
11 Allah ya ba Nuhu gaggarumin aiki. Wannan jirgin zai yi girma sosai domin tsawonsa ƙafa 437 ne, faɗinsa ƙafa 73 ne kuma tsayinsa ƙafa 44 ne. Ya fi girman filin kwallon ƙafa. Shin Nuhu ya yi ƙoƙarin kauce wa wannan aikin ne, ko ya soma gunaguni game da ƙalubale da zai fuskanta ko kuma ya canja tsarin da aka ba shi domin aikin ya yi masa sauƙi? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Hakanan kuwa Nuhu ya yi; bisa ga abin da Allah ya umurce shi duka, haka ya yi.”—Far. 6:22.
12 Sun daɗe sosai suna wannan aikin, mai yiwuwa shekara 40 ko 50. Za su sare itatuwa, su kai su inda za su yi amfani da su, su yanyanke su, sa’an nan su gyara da kuma harhaɗa su. Jirgin zai zama mai hawa uku, za a yi ƙananan ɗakuna a ciki da kuma ƙofa a gefensa. Hakika, akwai tagogi ta saman jirgin da kuma rufin da aka ɗan karkata domin kada ruwan sama ya taru a kan jirgin.—Far. 6:14-16.
13. Wane sashen aikin da Allah ya ba Nuhu ne wataƙila ya fi wuya, kuma mene ne mutanen zamanin suka yi?
13 Babu shakka, Nuhu ya yi farin ciki sosai domin iyalinsa sun goyi bayansa, kuma sun kusan kammala aikin da Allah ya ba su. Amma, akwai wani sashen aikin da aka ba shi da ya fi gina jirgin wuya. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Nuhu “mai-shelan adalci” ne. (Karanta 2 Bitrus 2:5.) Nuhu ya ja-goranci iyalinsa da gaba gaɗi don su yi wa miyagun mutanen gargaɗi game da halakar da ke tafe. Mutanen sun saurare shi kuwa? Shekaru da yawa bayan wannan lokacin, Yesu ya ce mutanen zamanin Nuhu ba su mai da hankali ba. Amma, sun shagala da harkokinsu na yau da kullum, kamar ci da sha da aure, kuma hakan ya sa ba su saurari Nuhu ba. (Mat. 24:37-39) Hakika, mutane da yawa sun yi wa Nuhu da iyalinsa ba’a, mai yiwuwa wasu sun yi musu barazana da hamayya. Wataƙila ma sun yi ƙoƙari su hana su gina jirgin.
14. Mene ne iyalai Kiristoci za su iya koya daga Nuhu da kuma iyalinsa?
14 Duk da haka, Nuhu da iyalinsa ba su ja da baya ba, amma sun ci gaba da gina jirgin ko da yake mutanen da ke kewaye da su suna ganin yin hakan aikin banza ne. Iyalai Kiristoci a yau za su iya koyan darussa sosai daga bangaskiyar Nuhu da iyalinsa. Me ya sa? Domin kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce, muna rayuwa ne a “kwanaki na ƙarshe.” (2 Tim. 3:1) Yesu ya annabta cewa zamaninmu zai kasance ɗaya da na Nuhu. Saboda haka, idan mutane suka yi mana hamayya ko ba’a ko kuma sun tsananta mana saboda wa’azin da muke yi, ya kamata mu tuna da Nuhu. Ba mu ba ne muka fara fuskantar irin wannan yanayin ba.
‘Ka Shiga Cikin Jirgin’
15. Wane rasuwa ne aka yi wa Nuhu sa’ad da ya kusan shekara 600?
15 Shekaru da dama sun shige kuma a hankali, aka gama gina jirgin. Sa’ad da Nuhu ya kusan shekara 600, an yi masa rasuwa. Mahaifinsa Lamech ya rasu.b Shekaru biyar bayan hakan, Methuselah kakan Nuhu da kuma mahaifin Lamech ma ya rasu yana ɗan shekara 969. Shi ne ɗan Adam da ya fi kowa shekaru a duniya. (Far. 5:27) An haifi Methuselah da Lamech a lokacin da Adamu yake da rai.
16, 17. (a) Mene ne Allah ya gaya wa Nuhu sa’ad da yake ɗan shekara 600? (b) Ka bayyana abin da Nuhu da iyalinsa suka gani da ba za su taɓa mantawa ba.
16 Sa’ad da Nuhu ya kai shekara 600, sai Jehobah ya ce masa: ‘Ka shiga kai da dukan gidanka cikin jirgi.’ Allah ya sake gaya wa Nuhu ya shigar da dabbobi dabam-dabam cikin jirgin, wato masu tsabta da za a iya yin hadaya da su bakwai-bakwai, sauran kuma bibbiyu.—Far. 7:1-3.
17 Wannan abu ne da ba za a taɓa mantawa ba. Ɗarurruwan dabbobi sun yi ta shiga jirgin, wasu suna tashi su shiga, wasu suna rarrafe, wasu kuma suna tafiya da sauri. Waɗannan dabbobin kala-kala ne, akwai manya da ƙanana masu halaye dabam-dabam. Nuhu bai lallaɓi dabbobin jejin kafin su shiga inda za a rufe su cikin jirgin ba. Labarin ya ce ‘suka shiga cikin jirgi wurin Nuhu.’—Far. 7:9.
18, 19. (a) Mene ne masu sūka suka faɗa game da labarin Nuhu, kuma me za mu iya ce musu? (b) Ta yaya yadda Jehobah ya ceci dabbobi ya nuna cewa yana da hikima sosai?
18 Wasu masu sūkar Littafi Mai Tsarki sun ce: ‘Ta yaya irin wannan abin zai iya faruwa? Ta yaya waɗannan dabbobin za su zauna tare a wurin da aka ajiye su?’ Ka yi la’akari da wannan: Shin zai gagare Mahaliccin sararin sama ya horar da dabbobin da ya halitta? Ka tuna cewa Jehobah ne Allahn da ya taɓa raba Jan Teku kuma ya sa rana ta tsaya cak. Ashe ba zai iya yin dukan abubuwan da aka ambata cewa sun faru a cikin labarin Nuhu ba? Hakika zai iya, kuma ya yi hakan!
19 Da a ce Allah ya so, da ya ceci dabbobin a wata hanya. Amma, ya zaɓi hanya da za ta tuna mana cewa tun asali, ya umurci ’yan Adam su kula da dukan abubuwa masu rai a wannan duniyar. (Far. 1:28) Iyaye da yawa a yau suna amfani da labarin Nuhu, don su koya wa yaransu cewa Jehobah yana daraja mutane da kuma dabbobin da ya halitta.
20. Ta yaya Nuhu da iyalinsa suka shagala da aikin a mako na ƙarshe kafin Rigyawar?
20 Jehobah ya gaya wa Nuhu cewa za a yi Rigyawar bayan mako ɗaya. Babu shakka, iyalin Nuhu sun shaƙu sosai da hidimomi a wannan lokacin. Ka yi tunanin irin aikin da ke gaban su. Za su shigar da kayayyakinsu da dabbobin da abincinsu kuma su shirya waɗannan abubuwan da kyau. Wataƙila matar Nuhu da matan Shem da Ham da Japheth sun damu da yadda za su mai da jirgin wurin zama mai kyau.
21, 22. (a) Me ya sa bai kamata mu yi mamaki ba cewa an yi wa Nuhu hamayya? (b) A wane lokaci ne mutanen suka daina yi wa Nuhu da iyalinsa ba’a?
21 Mene ne mutane da ke kewaye da su suka yi? Duk da tabbacin da suke gani cewa Jehobah yana wa Nuhu da ayyukansa albarka, ba su mai da hankali ba. Sun lura cewa dabbobin suna shiga cikin jirgin, amma duk da haka sun ƙi saƙon. Mutane a yau ma ba sa mai da hankali ga tabbacin da suke gani cewa muna rayuwa a kwanaki na ƙarshe. Kuma kamar yadda manzo Bitrus ya annabta, masu ba’a za su yi wa waɗanda suke bin gargaɗin Allah dariya. (Karanta 2 Bitrus 3:3-6.) Hakazalika, mutane sun yi wa Nuhu da iyalinsa ba’a.
22 Yaushe ne suka daina ba’ar? Labarin ya nuna mana cewa muddin Nuhu da iyalinsa da dabbobin suka shiga cikin jirgin, sai “Ubangiji kuma ya rufe shi a ciki.” Idan akwai masu ba’ar kusa da jirgin, yadda Jehobah ya kulle ƙofar jirgin ko kuma ruwan saman da aka yi kamar da bakin ƙwarya ya rufe baƙinsu. Kuma an ci gaba da yin ruwan har ya mamaye duniya baki ɗaya, kamar yadda Jehobah ya ce.—Far. 7:16-21.
23. (a) Ta yaya muka san cewa Jehobah bai ji daɗi yadda miyagu suka halaka a zamanin Nuhu ba? (b) Me ya sa ya dace mu kasance da bangaskiya kamar Nuhu?
23 Shin Jehobah ya yi farin ciki sa’ad da miyagun nan suka halaka? A’a! (Ezek. 33:11) Kafin lokacin, ya ba su dama su canja halinsu kuma su yi abin da ya dace. Da za su iya canjawa kuwa? Rayuwar Nuhu ta ba da amsar wannan tambayar. Nuhu ya nuna cewa hakan zai yiwu, ta wajen yin tafiya da Jehobah da kuma yi masa biyayya a kome. Ta hakan, bangaskiyarsa ta bayyana laifin mutanen zamaninsa, kuma ta nuna cewa zai yiwu mutum ya faranta wa Allah rai. Bangaskiyarsa ta sa shi da iyalinsa sun sami ceto. Idan ka yi koyi da bangaskiyar Nuhu, za ka iya ceci kanka da kuma waɗanda kake ƙauna. Kamar Nuhu, za ka iya yin tafiya tare da Jehobah a matsayin amininsa. Kuma wannan abokantakar za ta iya dawwama har abada!
a Mutane a wancan zamanin suna shekaru da yawa fiye da mu kafin su mutu. Me ya sa? Domin wataƙila bai daɗe ba da Adamu da Hawwa’u suka yi zunubi.
b Lamech ya sa wa ɗansa suna Nuhu, wataƙila sunan yana nufin “Hutu” ko kuma “Ta’aziyya.” Lamech ya annabta cewa Nuhu zai cika sunansa, ta wajen kawo wa mutane hutu daga wahalar da suke sha don an la’anta ƙasa. (Far. 5:28, 29) Lamech ya mutu kafin annabcin nan ya cika. Wataƙila Rigyawar ta halaka mahaifiyar Nuhu da ’yan’uwansa.