DARASI NA 52
Kayanmu da Adonmu Suna da Muhimmanci Ne?
Kowannenmu yana da irin riga da kuma adon da ya fi so. Akwai wasu ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da idan muka bi su, za mu iya saka kayan da muke so kuma mu faranta ran Jehobah. Bari mu tattauna wasu cikin waɗannan ƙa’idodin.
1. Waɗanne ƙa’idodi ne za su taimaka mana mu zaɓi irin rigar da za mu saka da adon da za mu yi?
Ya kamata mu riƙa saka “rigunan da suka dace” kuma mu kasance da tsabta, don hakan zai nuna cewa mu “masu bautar Allah” ne. (1 Timoti 2:9, 10) Ka yi la’akari da waɗannan abubuwa huɗu: (1) Ya kamata mu saka kayan “da suka dace.” Kamar yadda ka lura a taron ikilisiya, mutanen Jehobah suna son abubuwa dabam-dabam, amma rigunansu da irin aski ko kitson da suke yi suna nuna cewa suna daraja Allahn da suke bauta wa. (2) Ya kamata mu riƙa sa kayan da suka cancanta. Hakan yana nufin cewa mu guji saka kayan da zai sa mutane su yi tunanin da bai dace ba ko wanda zai sa mutane su riƙa kallon mu. (3) Ba dukan riga ko adon da ake yayin su ba ne ya kamata mu yi ba. Hakan zai nuna cewa mu masu hankali ne. (4) A kowane lokaci, ya kamata adonmu ya nuna cewa mu “masu bautar Allah” na gaskiya ne.—1 Korintiyawa 10:31.
2. Ta yaya adonmu zai iya shafan ’yan’uwanmu?
Ko da yake muna da ’yancin zaɓan irin kayan da za mu saka, zai dace mu yi tunani ko irin kayan da muke sakawa zai iya jefa wasu cikin matsala. Ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu don kada mu ɓata wa wani rai, amma mu ‘faranta wa maƙwabcinmu rai don kyautata zamansa da kuma ƙarfafa shi.’—Karanta Romawa 15:1, 2.
3. Ta yaya adonmu zai iya sa mutane su soma bauta wa Jehobah?
Ko da yake muna iya ƙoƙarinmu don mu yi adon da ya dace a kowane lokaci, ya kamata mu mai da hankali musamman ga adonmu sa’ad da muke halartan taron ikilisiya da kuma wa’azi. Mu yi ƙoƙari kada adonmu ya janye hankalin mutane daga wa’azin da muke yi. Maimakon haka, zai dace adonmu ya sa mutane su so jin wa’azi kuma su ‘daraja koyarwar nan da take game da Allah Mai Cetonmu.’—Titus 2:10.
KA YI BINCIKE SOSAI
Za mu ga yadda za mu tabbata cewa rigunanmu da adonmu sun dace da Kiristoci.
4. Ado mai kyau yana nuna cewa muna daraja Jehobah
Wane dalili mafi muhimmanci ne zai sa mu yi adon da ya dace? Ku karanta Zabura 47:2, sai ku tattauna tambayoyin nan:
Waɗanne irin kaya ne za mu saka idan muka tuna cewa za su iya sa mutane su bauta wa Jehobah ko kuma su ƙi yin hakan?
Kana ganin zai dace mu lura da adonmu kafin mu halarci taron ikilisiya ko mu je wa’azi? Me ya sa?
5. Yadda za mu yi zaɓi mai kyau game da rigunanmu da adonmu
Ko da rigunanmu masu tsada ne ko masu araha, ya kamata su kasance da tsabta kuma su dace da wurin da za mu je ko abin da muke yi. Ku karanta 1 Korintiyawa 10:24 da 1 Timoti 2:9, 10. Sai ku tattauna dalilin da zai sa mu guji saka kayan . . .
da ba su da tsabta ko ba su dace ba.
da suka matse mu ko suke sa a ga siffar jikinmu ko kuma su sa mutane su yi tunanin da bai dace ba.
Ko da yake Kiristoci ba sa bin Dokar da aka ba da ta hannun Musa, za su iya koyan ra’ayin Jehobah daga dokar. Ku karanta Maimaitawar Shari’a 22:5, sai ku tattauna tambayar nan:
Me ya sa za mu guji saka riguna ko yin adon da suke sa maza su zama kamar mata ko kuma mata su zama kamar maza?
Ku karanta 1 Korintiyawa 10:32, 33 da 1 Yohanna 2:15, 16, sai ku tattauna tambayoyin nan:
Me ya sa ya kamata mu lura ko adonmu yana ɓata wa wasu rai a unguwarmu ko kuma a ikilisiya?
Wane irin ado ko kaya ne ake sakawa a yankinku?
Kana ganin akwai wani cikinsu da bai dace da Kirista ba? Me ya sa?
WASU SUN CE: “Ina da ’yancin saka duk abin da na ga dama.”
Ka yarda da hakan? Me ya sa?
TAƘAITAWA
Idan muka yi adon da ya dace, muna nuna cewa muna daraja Jehobah da kuma mutane.
Bita
Me ya sa kayanmu da adonmu suke da muhimmanci ga Jehobah?
Waɗanne ƙa’idodi ne za su taimaka mana mu yanke shawara mai kyau game da kayanmu da kuma adonmu?
Ta yaya adonmu zai iya sa mutane su zo su bauta wa Jehobah ko kuma su ƙi yin hakan?
KA BINCIKA
Ku karanta talifin nan don ku ga irin ra’ayin da mutane za su iya kasancewa da shi game da kai sa’ad da suka ga irin kayan da ka saka.
Ku karanta talifin nan don ku ga abin da ya sa ya kamata mutum ya yi tunani kafin ya yi zane a jikinsa.
“Mene Ne Littafi Mai Tsarki Ya Faɗa Game da Zanen Jiki?” (Talifin jw.org)
Ku karanta talifin nan don ku ga wasu ƙa’idodin da za su taimaka mana.
“Tufafinka Suna Ɗaukaka Allah Kuwa?” (Hasumiyar Tsaro, Satumba 2016)
Ku karanta talifin nan don ku ga yadda wata mata ta kasance da ra’ayin da ya dace game da adon da wasu suke yi.
“Yadda Mutane Suke Sa Kaya da Yin Ado Yana Sa Ni Tuntuɓe” (Awake!, 22 ga Disamba, 2003, English)